Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta fi kowace ƙungiya ƙoƙari a Champions League - Arteta
- Marubuci, Alex Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport football news reporter in Paris
- Lokacin karatu: Minti 1
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ƙungiyar tasa ce ta fi kowacce ƙoƙari a gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana duk da kashin da suka sha a hannun Paris St-Germain.
Arsenal ɗin ta je filin wasa na Parc des Princes ne da zimmar rama ƙwallo ɗaya da aka zira mata a gidanta a wasan farko domin kaiwa wasan ƙarshe na gasar.
Sai dai duk da damarmakin da suka ƙirƙira, 'yanwasan Arsenal ɗin ba su iya yin nasara ba.
Ƙwallayen da Fabian Ruiz da Achraf Hakimi suka ci ne suka taimaka wa PSG din, inda har sai a minti na 76 Bukayo Saka ya farke wa Arsenal ɗaya, inda wasa ya tashi 3-1 gida da waje.
"Saura ƙiris, ƙiris ya rage mu sauya sakamakon wasan, amma kuma aka fitar da mu," a cewar Arteta.
"Ina matuƙar alfahari da 'yanwasana 100 bisa 100. Ba na jin akwai wata tawaga [da ta fi Arsenal] a gasar bisa abin da na gani, amma dai an cire mu.
"A wannan gasar, akwai da'irar yadi na 18, da masu tsaron raga, da masu cin ƙwallo, kuma nasu ne suka fi ƙoƙari a wasannin biyu."
Saboda gaza kaiwa wasan ƙarshe a Champions League karon farko tun 2006, kocin na Arsenal ya ce 'yanwasansa sun yi ta kuka bayan wasan.