Abin da muka sani kan daftarin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Dakarun Sojin Ukraine su na harba bindiga a cikin wani yanayi na hazo a ƙarƙashin ragar kariya a kusa da Pokrovsk

Asalin hoton, Marharyta Fal/Frontliner/Getty Images

    • Marubuci, Paul Kirby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Europe digital editor
  • Lokacin karatu: Minti 5

An kammala tattaunawa a Geneva da aka tattauna daftarin shirin zaman lafiya da Amurka ta gabatar don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine bayan kwana guda.

An bayar da rahoton cewa wakilan Amurka da na Ukraine sun yi nazari kan shawarwari 28 da jami'an Amurka da na Rasha suka tsara a watan da ya gabata.

Rasha ta ce ba ta ga wani sabon daftarin da aka tsara ba, bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Amurka da Ukraine.

Asalin daftarin da aka tsara ya bayar da shawarar miƙa waɗansu yankunan masana'antun Ukraine na gabashin yankin Donbas da har yanzu ke ƙarƙashin ikon Ukraine ga hannun shugaban Rasha Vladimir Putin - wani zaɓin da ba zai yin wa Ukraine daɗi ba.

Shirin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta rage adadin sojojinta zuwa dakaru 600,000.

Mene ne daftarin ya ƙunsa?

Da dama daga cikin muhimman batutuwa 28 na daftarin na iya samun karɓuwa daga Ukraine.

Amma akwai wasu da ba yi cikakken bayani a kansu ba.

Za a "tabbatar da ƴancin Ukraine" kuma za a sami "cikakkiyar yarjejeniya ta rashin cin zali tsakanin Rasha da Ukraine da Turai", tare da ingantaccen tabbacin tsaro da kuma buƙatar a gudanar da zaɓe cikin kwanaki 100.

Idan har Rasha ta yi yunƙurin mamaye Ukraine an bayar da shawarar "mayar da madaidaicin martanin soja na hadin gwiwa" tare da maido da takunkumai da soke yarjejeniyar.

Kodayake ba za a iya yin zaɓe a Ukraine ba saboda akwai dokar ta-ɓaci, amma za a iya gudanar da zaɓen idan an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Miƙa wasu yankunan Ukraine

Daga cikin sharuɗɗan da suka fi janyo cece-kuce har dabatun da ke buƙatar:

Ƙasar Ukraine ta miƙa wasu yankunan kasarta da ba a mamaye ba da kuma rage girman rundunar sojinta.

"Dakarun Ukraine za su janye daga wani ɓangaren yankin Donetsk Oblast da suke iko da su a halin yanzu, kuma wannan yanki zai kasance a matsayin wani yanki mai zaman kansa wanda aka amince da shi a matsayin yanki na Tarayyar Rasha.

Miƙa yankin inda aƙalla ƴan Ukraine 250,000 ke rayuwa.

Yankin Donetsk - da ya ƙunshi biranen Slovyansk da Kramatorsk da Druzhkivka - ba zai zama abu mai karɓuwa ga akasarin ƴan ƙasar ba.

Rasha ta kwashe sama da shekara guda tana ƙoƙarin mamaye garin Pokrovsk.

to amma da wuya Ukraine ta miƙa irin waɗannan muhimman cibiyoyi masu muhimmanci ba tare da wata jayayya ba.

Rage dakarun Ukraine

"Za a rage girman rundunar sojin zuwa dakaru 600,000."

A watan Janairun da ya gabata an ƙiyasta rundunar sojin Ukraine na da dakaru 880,000, inda aka samu ƙari daga 250,000 da ake da su a farkon mamayar da aka yi ma ta a watan Fabrairun 2022.

Yayin da dakaru 600,000 ke iya zama adadi mai gamsarwa a lokacin zaman lafiya, irin wannan iyakancewar zai keta ƴancin ƙasar Ukraine.

Hakanan yana iya zama adadin da Rasha za ta iya ƙin amincewa da shi.

Daftarin kuma ya ba da shawarar cewa ƙasashen duniya da suka haɗa da Amurka za su amince da "Crimea da Luhansk da Donetsk za a matsayin yankunan Rasha.''

Makomar Ukraine kan EU da NATO

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daftarin yana ba da shawarwari masu mahimmanci game da halin da Ukraine za ta shiga nan gaba:

"Ukraine ta amince ta sanya a cikin kundin tsarin mulkinta cewa ba za ta shiga ƙungiyar NATO ba, kuma NATO ta amince da sanya wa cikin dokokinta wani tanadi da ba za a amince da Ukraine nan gaba ba."

"Ukraine ta cancanci zama memba na ƙungiyar EU kuma za ta sami damar shiga kasuwannin Turai na gajeren yayin da ake nazari kan wannan batu."

Ba lallai ne Ukraine ta samu damar shiga ƙungiyar tsaro ta NATO cikin kwana kusa ba kuma a ƴan watannin baya-bayan nan Rasha ta sassauta matsayinta kan batun Ukraine na neman zama mamba a ƙungiyar EU.

Daftarin na da alamun bai wa Kyiv damar shiga kasuwannin EU yayin da ake yin watsi da ra'ayoyin ƙasashen Turai 27.

Shiga ƙungiyoyin EU da NATO wani ɓangare ne na kundin tsarin mulkin Ukraine kuma wani jan layi na Khrystyna Hayovyshyn a Majalisar Dinkin Duniya shi ne: "Ba za mu amince da duk wani cin zarafi a kan ƴancinmu ba, ciki har da ƙancin mu na zaɓar ƙawancen da mu ke son shiga."

Dawo da Rasha cikin jerin ƙasashen duniya

Abubuwa da dama cikin daftarin suna nuni da dawo da Rasha daga ''kaɗaici'' tare da ''sake shigar da Rasha cikin fagen tattalin arzikin duniya" kuma a sake gayyatarta ta dawo cikin ƙungiyar ƙasashe ta G8.

Da alama hakan ba zai faru cikin kwana kusa ba, yayin da Putin ke fuskantar sammacin kama shi daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

An fitar da Rasha daga cikin ƙungiyar ƙasashen G7 bayan da ta ƙwace sannan kuma ta mamaye Crimea a shekarar 2014 kuma Trump ya yi ƙoƙarin dawo da Putin cikin rukunin bayan shekara shida.

Idan Birtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan sun yi jinkiri kafin cikakken mamayar Ukraine da Rasha ta yi, akwai ma ƙarancin damar faruwar hakan a yanzu.

Ya labarin kadarorin Rasha da aka ƙwace?

Daftarin ya ba da shawarar cewa kadarorin Rasha mau darajar $100bn (€ 87bn; £ 76bn) da aka ƙwace za a yi amfani da su wajen "ƙoƙarin da Amurka ke jagoranta na sake ginawa tare kuma da sanya hannun jari a Ukraine", yayin da Amurka za ta samu kashi 50 cikin ɗari na ribar sa'annan Turai ta ƙara dala biliyan 100 na jari don sake gina ƙasar.

Wannan yana kamanceceniya da yarjejeniyar ma'adinan da Amurka ta ƙulla da Ukraine a farkon wannan shekarar, inda ta za ta biya Amurka farashin shiga yaƙin, sannan kuma ta bar Tarayyar Turai da alhakin biyan kuɗaɗe masu yawa.

Mai yiwuwa adadin kuɗaɗen da aka ambata ba zai wadatar ba, a farkon wannan shekarar an sanya jimillar kuɗin sake gina ƙasar Ukraine a kan dala biliyan 524.

Wasu kadarorin Rasha da aka daskarar sun kai Yuro biliyan 200 ne akasari suna hannun Euroclear ne a Belgium, kuma a halin yanzu ƙungiyar Tarayyar Turai na shirin yin amfani da kuɗin wajen samar da kuɗaɗen da Kyiv za ta yi amfani da su ta fuskar kuɗi da kuma na soji.

Mene ne ba ya cikin daftarin?

Masu sharhi da dama sun yi nuni da cewa shirin ba ya buƙatar takaita yawar makaman sojojin Ukraine ko kuma masana'antunta na makamai, duk da cewa akwai tanadin da ke cewa:

Idan Ukraine ta harba makami mai linzami zuwa Moscow ko St.Petersburg, wannan zai wargaza duk wani tabbacin tsaro da aka ba ta.

Amma ba ta sanya takunkumi kan makamai masu cin dogon zango da Ukraine ke ƙerawa ba - kamar makamanta masu linzami nau'in Flamingo da Long Neptune.

Shin wannan tabbataccen shirin zaman lafiya ne?

A'a.

"Har yanzu da sauran aiki a gaba," in ji sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio a yammacin Lahadin da ta gabata, bayan tawagarsa ta tattauna da wakilan Ukraine da na Turai a birnin Geneva na ƙasar Switzerland.

Babban jami'in diflomasiyyar na Amurka ya ƙara da cewa "Amma mun samu ci gaba sosai a wannan lokaci fiye da yadda muka fara da safiyar yau da kuma haka ma idan muka kwatanta da matsayin mu mako guda da ya gabata."

Ya dai ƙi yin cikakken bayani kan sauran abubuwa masu sarƙaƙiya da suka rage.

Rubio ya kuma ce dole ne Rasha, waca samu amincewar Rasha kan duk wata yarjejeniya, amma dai ba ta fito fili ta yi tsokaci kan sabbin abubuwan da ke faruwa ba.

A halin da ake ciki, kafofin yaɗa labarai da dama sun ba da rahoto tare da wallafa abin da suka bayyana a matsayin wani shiri ne na daban daga ƙawayen Ukraine na Turai ƙarƙashin jagorancin Birtaniya da Faransa da Jamus.

Daftarin duk buƙatun Putin ne?

An san cewa wakilin Rasha na musamman, Kirill Dmitriev ya shafe tsawon kwanaki uku tare da wakilin Trump na musamman, Steve Witkoff suna tattaunawa kan wannan shiri, inda ya ba da shawarwarin ƙulla yarjejeniyar da ta dace da Moscow.

Wasu ƴan majalisar dattawan Amurka sun ce Rubio ya shaida musu cewa shirin ba shawara ce ta Amurka ba - cewa yana wakiltar matsayin Rasha ne kuma wakilin Moscow ne ya bayyana shi.

Wannan dai ya ci karo da matsayin fadar White House, wadda ta ce shugaba Donald Trump ya amince da shirin, bayan da jami'ansa suka tsara shi.

Daga baya Rubio ya ce "Amurka ce ta rubuta daftarin".