Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin zai yiwu mutum ya sauya ko shi wane ne?
- Marubuci, Shannon Sauer-Zavala
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, The Conversation*
- Lokacin karatu: Minti 3
A cewar masana ilimin halayyar dan'adam, yadda mutum ke tunani ko jin abu ko kuma yadda yake yin abubuwa, shi ke nuna ko wanene shi.
Shin kai mutum ne da ke yi wa abubuwan da ke faruwa a rayuwa mummunan kallo ko kuwa wanda ke da kyakkyawan fata ga rayuwa?
Shin kana jin haushi idan wani ya zo ya sha gabanka a lokacin da kake tuƙa mota, ko kuwa kai mai bayar da uzuri ne — kila ko yana sauri ne za shi asibiti?
Kana jira sai dab da lokaci ya kusan cika kafin ka yi abin da ke gabanka, ko kuwa kana shiryawa tun da wurwuri.
Ana iya bayyana ɗabi'ar mutum a matsayin halayyar da ke nuna yadda mutum ke amsa wasu tambayoyi kamar waɗannan. Akan gane mai ƙwarin gwiwa ne, ko mai tausayi, ko mai amana da amsoshin da ya bayar game da tambayoyin.
Masana na cewa ana iya dunƙule waɗanna siffofin zuwa rukuni biyar na halayyar mutum - abin da masana halayya ke kira da "Big Five" a Turance.
A shekarun 1930, masana halayya sun lalube ƙamusu domin nemo kalmomin da ke siffanta halin mutum tare da karkasa su zuwa maudu'ai.
Misali, sun haɗa kalmomi kamar "kirki" da "mai fahimta", da "mai yawan abota" a rukuni ɗaya.
Saɓanin haka: A lokuta da dama mutane kan ɗauki halayensu da muhimmanci bisa tunanin cewa su ne abubuwan da suka bambanta su da saura.
Amma a cewar masana kimiyya, halayen mutum ba su ne bubuwan da yake so ko ƙi ba. Ba kuma barkwanci ba ne, ko kuma wani abu da yake jin yana da muhimmanci a rayuwarsa.
A wani gefen, sauya muhimman abubuwa biyar (Big Five) ba zai iya sauya ko shi wane ne. Kawai na nufin sauya tunani game da abubuwan da ke faruwa da shi ta hanyar tunani, da ji a jiki, da kuma ɗabi'a.
Ko za ku iya sauya ku su wane ne?
Kada ku manta halayen mutum ne abubuwan da ke bayyana a matsayin ɗabi'u da hanyoyin tunaninsa.
Yayin da ake ganin sauya hali abu ne mai wuya, mutane kan iya sauya yadda suke tunani, da ji a jiki.
Mu ɗauki misali da mutumin da ba shi ɗukar abubuwa da muhimmanci. Idan ya fara tunanin zuwa wurare a kan lokaci zai sa mutane su fara jin cewa yana girmama alƙawari, ko ya fara jin alfahar a gban abokansa, ko ya sauya wasu ɗabi'u da za su ƙara masa kima, nan take zai koma mutum mai kima.
Idan mutumin ya ci gaba da aikata hakan, kuma ya saka a ransa, da tunaninsa to lallai mutane za su koma girmama shi da kuma ɗaukar sa da muhimmanci.
Bincike ya tabbatar da haka. Mutum kan sauya a tsawon rayuwarsa. Yayin da mutum ke ƙara shekaru, yakan ji ƙwarin gwiwa kan abubuwa sama da sanyin gwiwa, ya dinga mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci, da kuma rage yanke wa mutane hukunci.
Amma akan samu bambanci tsakanin mutane. Wasu kan sauya da yawa, yayin da wasu ke bi sannu a hankali.
Wani bincike da na yi da kaina ya nuna cewa yunƙurin da wasu kan yi da gangan domin sauya halinsu na hanzarta sauyin a cikin tunaninsu da ɗabi'unsu.
Irin wannan yunƙuri kan taimaka wajen samun sauyi mai yawa cikin mako 20 - maimakon shekara 20.
Tsara ɗabi'un da suka fi dacewa
Labari mai daɗi shi ne abubuwan da suka danganci tunanin mutum na da sauƙin sauyawa, kuma ba sai an ga likita ba a mafi yawan lokaci.
Abu na farko shi ne sauya salon da mutum ke bi wajen yin tunani - shi ne abin da ya fi shafar ƙwaƙwalwa.
Ya kamata mutum ya dinga tuntuntuni kan yadda yake yin tunani domin ganin suna hana shi yin abin da ya dace ta hanyar bin wani takamaiman salo ɗaya. Misali, idan mutum ya fiya tunanin cewa sauran mutane kansu kawai suka sani, to kuwa ɗabi'unsa za su koma na kare kan sa kawai.
Shi kuma ɓangaren ɗabi'u na nufin kasancewa a ankare game da ɗabi'un mutum yayin da yake mayar da martani ga me da abubuwan da ke faruwa.