Yadda Facebook ya daƙile labaran da ke fitowa daga yankin Falasɗinawa

    • Marubuci, Ahmed Nour, Joe Tidy and Yara Farag
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic, BBC World Service & BBC Monitoring
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ɓangaren da ke bin kwakkwafi na BBC ya gano cewa Facebook ya yi ta hana kafafen yaɗa labaran Falasɗinawa wallafa labaran da za su isa ga masu bibiyar su lokacin da ake yaƙin Isra'ila da Gaza.

Cikin wani sharhi da aka yi kan bayanan Facebook, mun gano cewa ɗakunan labaran yankin Falasdinawa da ke Gaza da gabar Yamma da kogin Jordan - sun fuskanci ƙaranci rashin mabiya tun watan Oktoba 2023.

BBC ta fitar da bayanai da ke nuna Instagram wanda shi ma kamfanin Meta ne ke da shi ya ƙara matsawa kan rufe ra'ayoyin da masu amfani da manhajar daga yankin Falasɗinawa bayyanawa tun bayan harin Oktoban 2023.

Meta ya ce - duk wani zargin cewa sun yi ƙoƙarin daƙile ra'ayoyin wasu da gangan "wannan ƙarya ce tsagwaronta".

Tun lokacin da aka fara yaƙin Isra'ila da Gaza - masu aika rahotanni kaɗan aka bari su shiga yankin Falasɗinawa da ke Gaza, kuma ana barin su yin hakan ne kawai tare da rakiyar dakarun Isra'ila.

Kafafen sada zumunta ne suka cike giɓin da aka samu na waɗanda ke son jin abin da ke faruwa a Gaza da ba sa cikin garin.

Shafukan Facebook irin su Palestine TV, Kamfanin dillancin labarai na Wafa da kuma Palestinian Al-Watan - waɗanda ke aiki a nesa da yankin gaɓar yamma da kogin Jordan - sai da suka zama madogara wajen samun labarai a faɗin duniya.

Sashen BBC na larabci ya tattara bayanai kan yadda shafuka 20 da suka yi fice a Facebook wajen yaɗa labarai suka zama zakarun gwajin dafi a bara tun bayan kai harin 7 ga watan Oktoba da kuma wannan shekarar.

Yadda mutane ke bayyana ra'ayoyinsu na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake gane tasirin shafi ke da shi da kuma gane mutane nawa ne ke ganin abin da ya wallafa. Bayyana ra'ayin da nuna damuwa ko kuma sake turawa duniya labarin na cikin manyan abubuwan da ake lura da su.

Yadda ake bibiyar kafafen yaɗa labaran yankin Falasdinawa a Facebook

Masu bibiyar shafukan yaɗa labaran Isra'ila a Facebook

A lokacin yaƙi, ana tsammanin masu bibiyar shafuka sun ƙaru. Amma sai dai alƙalumma sun nuna an samu raguwar su ne da kashi 77 bayan harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai a 2023.

Shafin Palestine TV na da mabiya miliyan 5.8 a Facebook. 'Yan jaridar yankin sun nuna an samu raguwar kashi 60 na mabiyan da ke kallon shafukansu.

"An hana bayyana ra'ayi ko damuwa da abin da aka wallafa, abin da muka wallafa ba ya kai wa ga masu bibiyar mu," in ji Tariq Zaid wani ɗan jarida da ke aiki da cahnnel.

Bayan shekara guda, 'Yan jaridar Falasdinawa sun nuna fargabar yadda kamfanin Meta ke daƙile abubuwan da suke wallafawa - ko kuma taƙaita yawan mutane da za su gani.

Domin tabbatar da hakan, mun yi amfani da irin alƙaluman baya na bibiyar manyan shafukan yaɗa labarai na Isra'ila 20 kamar su Yediot Ahronot, Isra'ila Hayom da kuma Channel 13.

Wadannan shafuka sun wallafa labaran da ke da alaƙa da yaƙin, sai dai yadda mabiya ke bin su ya ƙaru da kashi 37.

A baya ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da Falasɗinawa sun zargi kamfanin Meta na gaza sanya idanu kan abubuwan da ke faruwa a shafukansa ba tare da nuna san kai ba.

Wani rahoto da kamfanin ya fitar a 2021 ya ce ba da saninsa hakan ke faruwa ba - kuma hakan ya biyo bayan ƙarancin masu jin yaran larabci ne cikin masu sanya ido.

Ana yawan fassara kalaman da aka wallafa a matsayin na tashin hankali, kuma ba hakan suke nufi ba.

Misali, "Alhamdulillah", tana nufin "godiya ga Allah" amma a abin da ke musu fassara sai ya nuna kalmar neman ƴanci da ƴan ta'adda ke amfani da ita.

Yadda ake bibiyar kafafen yaɗa labaran Larabci (Da ba na Falasɗinawa ba) a Facebook

Da yake mayar da martani ga bincikenmu, kamfanin ya nuna babu wani abu da ya boye na matakan da yake ɗauka a manufofinsa tun daga Oktoba 2023.

Ya ce yana fuskantar kalubale wajen tantance 'yancin tofa albarkacin baki, da kuma batun cewa Amurka ta ƙaƙaba wa Hamas takunkumi da ayyana su a matsayin ƙungiya mai haɗari ƙarƙashin ƙa'idojin kamfanin Meta.

Kamfanin ya ce shafukan da suke wallafa abubuwan yaƙin kawai za su iya ganin ci gaba mai yawa.

Bayanan sirrin Instagram da aka kwarmata

BBC ta yi magana da wasu mutane biyar da suka yi aiki da Meta da kuma wasu da suke aiki da kamfanin yanzu haka kan cewa kamfanin na da ka'idojoji kan ɗaiɗaikun Falasɗinawa da ke amfanin da shafuknsa.

Wani da ya nuna a sakaya sunansa, ya bayyana wasu bayanan sirri kan sauyin da aka yi a wajen tattara bayannan Instagram, wanda shi ke jan ragamar tsaftace ra'ayoyin falasinawa da ake wallafawa.

"Cikin satin da Hamas ta kai hari aka sauya tsarin aka mayar da shi mai tsaurarawa kan kalaman Falasɗinawa," in ji shi.

Wasu saƙonnin cikin gida sun nuna yadda wani injiniya ya nuna damuwa a kan sauyin, cewa an kawo wani sabon tsarin son zuciya a tsarin da zai riƙa aiki kan Falasɗinawa masu amfani da Instagram".

Meta ya ce ya gudanar da wasu sauye-sauye da suka zama dole waɗanda ya kira "kalaman nuna ƙiyayya" da suke fitowa daga yankin Falasdinawa.

Ya ce sabon tsarin da aka kawo bayan fara yaƙin Isra'ila da Gaza yanzu an janye shi, sai dai bai bayyana yaushe hakan ya faru ba.

Akalla Falasɗinawa 137 ne aka kashe tun fara yaƙin Gaza - amma kaɗan ne ke ci gaba da aikin saboda haɗarin da ke cikinsa.