Yadda man kaɗe ke fuskantar barazana a wasu yankunan Afirka

- Marubuci, Njoroge Muigai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Marubuci, Anne Okumu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
A yankin arewa maso yammacin Uganda, inda aka fi samun itatuwan kaɗe, Mustafa Gerima ya kasance yana ƙarfafa wa al'ummar yankin gwiwa da kuma wayar musu da kai kan kare itatuwan daga sarewa.
Mustafa ya kasance mai gwagwarmaya waje kare itatuwan kaɗe daga masu sare bishiyoyi, wani abu mai muhimmanci ga tattalin arziƙi.
Ga Mustafa - wanda malamin koyar da ilimin halittu, daga baya kuma ya koma mai fafutukar kare muhalli - na gwagwarmayar kare bishiyar kaɗe, saboda yadad ya ɗauki hakan da muhimmanci.
Shekaru da dama da suka gabata, Mustafa ya bar Uganda zuwa Tanzania domin aiki.
To sai bayan sake komawarsa Uganda ya tarar an sassare itatuwan kaɗe da ke dajin Mount Kie, inda ya ce yanayin da ya gani yayi matuƙar yi masa ciwo
Ya bayyana cewa al'umma, da ke fama da talauci, suna ganin itatuwan kaɗe a matsayin hanya mai sauƙi na samun kuɗi.
Wannan lalata gandun daji ne ya sa Mustafa ɗaukar nauyin ilimantar da al'umma game da muhimmancin itacen.
A cikin fafutikarsa, ya yi tafiyar kwanaki 19, kilomita 644, daga babban birnin ƙasar, Kampala, zuwa shalkwatar Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) a Nairobi, Kenya.
'Zinaren itace'
A Uganda, itacen kaɗe, wanda aka sani da "Zinarin mata" saboda rawar da yake takawa wajen samar da man kaɗe mai daraja, yana fuskantar ƙalubale saboda canjin yanayi.
Mata sun kasance suna tattara ganyen kaɗe domin yin man kaɗe a matsayin kasuwancinsu, wani aiki mai ɗorewa da ke tallafa wa al'ummomin yankin.
Sai dai, manoma yanzu na fusantar ƙalubale wajen shukawa da renon itacen kaɗen.
"Shekaru 30 da suka wuce, itacen kaɗe yana fure sosai a watan Disamba, sannan a watan Afrilu ana iya cire ƴaƴan. Amma yanzu, saboda canjin yanayi, lamarin ya sauya" in ji manomi Mustafa.
A sakamakon haka, yawancin manoma suka koma ƙona itatuwan suna yin gawayi da su suna siyarwa.

Farfesa John Bosco Okullo, ƙwararren masani a fannin kimiyyar gona daga Jami'ar Makerere, ya kasance yana nazarin itacen kaɗe tsawon sama da shekara 20.
Shiga aikinsa da wannan itace ya fara ne a shekarar 1999, lokacin da ya zama ɓangare na wani shirin Tarayyar Turai da ke nufin kiyaye amfani da itacen.
"A shekarun 1990, al'ummomi suna da mallakar itacen kaɗe kuma suna kula da su," in ji shi.
Amma a Lokacin da mutane suka dawo, sun koma ƙona itatuwan suna yin gawayi a matsayin sana'a
Farfesa Okullo ya ce canjin yanayi ya ƙara dagula lamarin.
Kiyaye muhalli
Uganda na rasa kimanin hekta 100,000 na gandun daji a kowace shekara, kuma wani babban ɓangare na wannan yana haɗawa da itacen kaɗe.
Da farko, itacen kaɗe yana rufe manyan yankuna daga yammacin zuwa gabashin Afirka, amma a wasu yankuna, yawan itacen kaɗe ya faɗi daga kashi 43 cikin 100 zuwa kashi 13.

Wannan asara ta yi tasiri kai tsaye ga mutane kamar Mariam Chandiru, wata mai samar da man kaɗe a Koboko.
"Mun kasance muna samun kuɗi mai yawa da muke tura 'ya'yanmu makaranta da kula da iyalanmu. Amma yanzu kasuwancina na rushewa, babban ƙalubale ne," in ji ta.
"Na kasance ina sayar da jarkoki biyar na man kaɗe a kowane mako, amma yanzu guda biyu kawai nake samu a mafi yawan lokaci."
"A yanzu, akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama suna ƙarfafa al'ummomi," in ji Farfesa Okullo. "Mutane na shuka sabbin itace da kuma kula da waɗanda ke farfaɗowa daga tushe."

Gwamnatin Uganda ta kuma gane cewa itacen kaɗe na cikin haɗari, kuma a shekarar 2023, ta haramta sare itatuwan kaɗen don yin gawayi.
Sai dai aiwatar da wannan doka na ci gaba da fusknatar ƙalubale.
"Akwai umarnin shugaban ƙasa da ya hana sare itatuwan kaɗe, amma aiwatar da shi ya kasance da wahala," in ji Farfesa Okullo.
A Koboko kuwa, Mustafa Gerima na ci gaba da wayar da kai. Yana magana da majalisun yankin da shirya shuka itatuwar kaɗe da dama.
"Wannan bai kamata ya zama abin mutum ɗaya ba. Ya kamata ya zama aiki tare da haɗin gwiwa da alhakin kowa," in ji shi.
Matakan da ya ke shirin ɗauka na gaba sun haɗa da ƙaddamar da wani shiri na sa ido kan itatuwa daga tushe, tare da haɗin gwiwa da makarantu don saka koyar da muhalli cikin kundin karatu na yankin.











