'An ce in kashe ɗana saboda na haife shi babu hannu'

...

Shindara yaro ne mai kazar-kazar gashi cike da farin ciki, sai dai mahaifiyarsa ta haife shi ne babu hannaye.

Hakan bai sanyaya wa Funmilayo gwiwa ba, inda ta fara koya masa yadda zai tafiyar da rayuwarsa ya kuma girma ya samu ilimi.

A cewar Funmilayo, mutane sun ba ta shawarar cewa ta sayi wata allura wadda za ta yi amfani da ita wajen kashe ɗanta, sai dai ta ƙi jin wannan shawarar.

Tana koya wa ɗanta yadda zai ci gaba da zama mai ƙarfin zuciya ba tare da ya saduda ba.

“Ina ɓoye shi a da, wani ya taɓa gaya mini cewa akwai wani asibiti, inda zan iya sayen allurar da zan iya ba shi ya mutu, in ji babar yaron.

“Lokacin da na haife shi, mutane sun sha yi mini surutun cewa shekaruna ba su kai ba, gashi na je na haifi yaron da ba shi da hannu".

...

Shindara na son karatu, don haka babarsa ta fara koya masa wasu muhimman abubuwan da ya kamata ya sani, sannan ta saya masa fensur da littafi don yin rubutu.

Tun da ba shi da hannu, Shindara na amfani da ƙafarsa wajen yin rubutu kuma burinsa shi ne ya zama lauya.

“Yana son karatu sosai, a koda yaushe yana maganar cewa zai zama lauya idan ya girma. Na saya masa fensur da littafi ne domin lauya ba malalaci ba ne. Na shaida masa cewa sai ya wuce masu hannaye ma."

....

Mahaifiyar Shindara na da kyakkyawan fatan cewa ɗanta zai samu hannayen roba waɗanda za su taimaka masa wajen yin abubuwa sosai idan ya girma, da kuma inganta yanayinsa.

“Idan ɗana zai samu hannuwan roba wanda ake haɗawa da kwaƙwalwa, hakan zai taimaka masa. Ina yi wa rayuwarsa ta nan gaba kyakkyawan fata, kuma na yi amannar cewa zai iya," in ji ta.