Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Rasha Vlaimir Putin ya zargi shugabannin kungiyar sojan haya ta Wagner da suka shirya boren da sojojin kungiyar suka yi a karshen mako da son ganin "Rasha ta tsunduma cikin wani rikici mai cike da zubar da jini".
A cikin wani gajeren jawabi mai cike da fushi, Mista Putin ya sha alwashin gurfanar da wadanda suka shirya boren a gaban kuliya.
Ya kuma bayyana tsohon amininsa a matsayin wanda ya ci amanar Rasha.
Ya yi amfani da jawabinsa a matsayin wani yunkuri na karfafa ikonsa tare da kawar da tunanin da ake yi a kan cewa akwai rauni a matakan da ya dauka kan kungiyar ta Wagner.
Sai dai ya bayyana dakarun Wagner da ba su sa kansu a cikin wannan rikicin ba a matsayin "masu kishin kasa" wadanda za a ba su damar shiga aikin soja, ko zuwa kasar Belarus ko komawa gida.
Sai dai bai bayyana sunan shugaban kungiyar Wagner, Yevgeny Prigozhin kai-tsaye ba, wanda tun farko ya musanta cewa tattakin da suka yi ba wani yunkuri ba ne na kifar da gwamnatin Putin.
Wagner dai runduna ce mai zaman kanta ta sojojin haya wadda ke fafatawa tare da sojojin Rasha a yakin da suke yi da Ukraine.
Boren na gajeren zango wanda ya sa mayakan Wagner suka ƙwace wani babban birni kafin daga bisani suka doshi birnin Moscow a cikin jerin motocin sojoji, martani ne ga shirin gwamnati na karɓe iko da kungiyar kai-tsaye, kamar yadda Prigozhin ya yi ikirari a muryarsa da aka naɗa na tsawon mintuna 11, aka kuma wallafa a shafin Telegram a ranar Litinin.
A watan Yuni ne Rasha ta ce za a nemi wasu rundunonin sa -kai da su rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakaninsu da ma'aikatar tsaro wanda wani mataki ne da ake kallo a matsayin barazana a kan yadda Prigozhin ke tafiyar da kungiyar ta Wagner.
Jagoran sojin hayar ya ce ya shirya borenm ne domin nuna rashin amincewa da kura -kuran da jami'an tsaro suka aiktata a yaƙin Ukraine.
Amma ya dage da cewa a ko yaushe Wagner na aiki ne domin kare muradun Rasha.
Wannan shi ne kalaman farko da Prigozhin ya yi a bainar jama'a tun bayan da ya amince da dakatar da boren.
An ba shi damar tafiya Belarus tare da jingine duk wasu tuhume-tuhumen da ake yi masa, ko da yake kafofin yada labaran Rasha sun ambato jami'ai na cewa kawo yanzu suna gudanar da bincike a kansa.











