Ƙungiyoyin da ke yi wa Hamas taron dangi don ƙwace iko da Gaza

غزة

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Ethar Shalabi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sakamakon yanayin tsaro da ake ciki a Zirin Gaza, yanbindigar da ke yankin yanzu ba wasu shahararru ba ne, ƙananan ƙungiyoyi ne na dangi-dangi da ke adawa da Hamas.

Waɗannan ƙananan ƙungiyoyi sun ɓulla ne saboda rarrabuwar kai da aka samu sakamakon yaƙin Isra'ila da Hamas, wanda ya sa ta rasa iko da zirin.

Ƙungiyoyin kan yi iko da abubuwa da yankuna daban-daban, inda suke biyayya ga dangi da 'yan'uwansu.

Amma me muka sani game da waɗannan ƙungiyoyi?

Dangin Daghmash

Ƙungiyar dangin Daghmash na ɗaya daga cikin mafiya girma tsakanin zuri'ar Falasɗinawa a Zirin Gaza, inda aka yi ƙiyasin suna da mayaƙa 3,000 a Gaza, da kuma 1,500 a wajensa.

Ta fi ƙarfi a unguwannin Sabra da Tel al-Hawa da ke Birnin Gaza. A cewar jagoran zuri'ar mai suna Salah Daghmash lokacin da yake hira da 'yanjarida a 2007, mambobinta na bin jam'iyyar siyasa daban-daban, kamar Hamas da Fatah, da Popular Front for the Liberation of Palestine.

Mambobin ƙungiyar sun sha gwabzawa da Hamas, musamman bayan Hamas ta kama iko da Gaza a 2007.

Gwabzawar ta fi faruwa a unguwannin Sabra da Tel al-Hawa bayan mambobinta sun ƙi amincewa su miƙa makamansu.

Tsohon wakilin BBC Alan Johnston ya ce wata ƙungiya da ta ƙunshi mambobin dangin Daghmash ce ta yi garkuwa da shi a 2007. A cewarsa, a lokacin Daghmush na jagorantar wata ƙungiya mai suna Sojojin Musulunci, wadda ita ce ke riƙe da shi.

A watan Oktoban 2025 ne aka yi gwabzawa ta baya-bayan nan yayin da Hamas ke zargin ƙungiyar da yin aiki tare da Isra'ila, zargin da suka musanta.

Bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, Hamas ta ƙaddamar da abin da ta kira "hukunci" kan wasu mambobin Daghmash bisa laifin cin amanar ƙasa.

Abu Shabab

Yasser Abu Shabab ne shugaban ƙungiyar Popular Forces da ta ɓulla a 2024

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Yasser Abu Shabab ne shugaban ƙungiyar Popular Forces da ta ɓulla a 2024
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ƙungiyar ta ɓulla ne a 2024 wadda Yasser Abu Shabaab ke jagoranta. Dangi ne daga tsatson Larabawan ƙauye na Bedouin Tarabi da ke unguwar Rafah a kudancin Gaza.

A watannin baya, Adel al-Tarabin ɗaya daga cikin shugabannin ƙabilar Tarabin, ya sanar cewa ƙungiyar ta raba gari da Yasser bayan Hamas ta zarge shi da satar kayayyakin agaji ta hanyar haɗa kai da Isra'ila.

Yasser ya musanta zarge-zargen kafin daga baya ya amince cewa sun yi aiki tare da dakarun Isra'ilar, yana cewa: "Taimako ne kawai daga sojojin Isra'ila ba wani abu ba. Idan za mu fita aiki za mu sanar da su - babu wani abu bayan haka."

Jaridar Times of Israel ta ruwaito cewa Isra'ila na taimaka wa 'yanbindigar da ke adawa da Hamas a Gaza, waɗanda 'yan ƙabilar Bedouin ne, abin da ke alamta ƙungiyar Abu Shabab ne.

A cewar jaridar, ɗansiyasar adawa a Isra'ila Avigdor Lieberman ya faɗa wa wata kafar yaɗa labaran ƙasar cewa Firaminista Benjamin Netanyahu ne ya bayar da umarnin aika wa ƙungiyar Abu Shabab makamai.

Ƙungiyar Abu Shabab na kiran gungunsu Popular Forces a gabashin Rafah. Ƙungiyar kan ce tana kare kayan agaji da kuma ayyukan taimaka wa al'umma a birnin.

Kazalika, takan ce tana kare mutane daga abin da ta kira "zalincin Hamas".

Kafofin yaɗa labarai sun ce Hamas ta taɓa kulle Abu Shabab a gidan yari kafin fara yaƙi da Isra'ila.

Ƙungiyar Husam al-Astal

Husam al-Astal ya ce ƙungiyarsa na yaƙi da Hamas kuma za ta shiga shirin gina Gaza bayan yaƙi

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Husam al-Astal ya ce ƙungiyarsa na yaƙi da Hamas kuma za ta shiga shirin gina Gaza bayan yaƙi

Wannan ƙungiya ce da ke ƙarƙashin jagorancin Husam al-Astal, wani tsohon jami'i a rundunar tsaro ta Hukumar Falasɗinawa.

Hamas ta sha kama shi har ma ta yanke masa hukuncin kisa bayan tuhumar sa da kisan wani mamban ƙungiyar a Malaysia a 2018. Al-Astal ya samu tserewa wata biyu bayan ɓarkewar yaƙin Gaza.

Shi ma Hamas ta zarge shi da haɗa kai da Isra'ila. Ya amsa yin aiki tare da dakarun Isra'ila amma ba cikakken haɗin kai ba, inda ya nuna cewa Isra'ila ta kashe 'yarsa. Amma ya zargi Hamas kan hakan waɗanda ya ce suna ɓuya cikin fararen hula.

Cikin wata hira da Sky News a watan Oktoba, Al-Astal ya ce burinsa tare da ƙungiyoyin Abu Shabab, Rami Halas, da Ashraf Al-Mansi shi ne adawa da Hamas da kuma kafa sabuwar Gaza.

Ƙungiyar Mantattu

Ashraf al-Mansi na jagorantar ƙungiyar "Popular Army" a Gaza

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Ashraf al-Mansi na jagorantar ƙungiyar "Popular Army" a Gaza

Ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin da ke adawa da Hamas, wadda ke kiran kanta "Dakarun Al'umma".

Tana da mambobi aƙalla 20 kuma an yi imanin an kafa ta ne a wata Satumban da ya gabata ƙarƙashin jagorancin Ashraf al-Mansi.

Daga baya al-Mansi ya bayyana a wani bidiyo yana musanta cewa an kai wa ƙungiyarsa hari.

A bidiyon, Al-Mansi ya kuma gargaɗi mayaƙan Hamas da kada su shiga yankin da suke iko da shi a arewacin Gaza.

Haka nan, ya tabbatar wa mazauna Gaza cewa ƙungiyarsa za ta ba su kariya ta hanyar korar Hamas daga arewacin Gaza.

Ƙungiyar Helles

Rami Halas na jagorantar ƙungiyar Popular Defense Forces

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Rami Halas na jagorantar ƙungiyar Popular Defense Forces

Ƙungiyar Helles na ƙarƙashin jagorancin Rami Helles a yankin Shuja'iyya da ke gabashin Gaza kuma mai adawa da Hamas.

Helles tsohon jami'in soja ne a rundunar Hukumar Falasɗinawa, kuma yana cikin manyan zuri'o'i a Gaza.

Kafofin yaɗa labarai a Isra'ila sun ce Helles ɗan jam'iyyar Fatah ne kuma yana cikin masu aiki tare da dakarun ƙasar yayi yaƙin Gaza.

Sai dai Manjo Janar Anwar Rajab ya musanta duk wata alaƙa tsakanin ƙungiyar da Hukumar Falasɗinawa.

Rahotonni sun ce mambobin Helles sun sha fafatawa kai-tsaye tare da dakarun Hamas a Shuja'iyya a 'yan kwanakin nan, amma kuma babu tabbas game da makomar ƙungiyar a yanzu.