Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'yan daudu a Najeriya suka fada cikin fargaba kan ƙudirin dokar da zai sa a fara ɗaure su
'Yan daudu da mutanen da ke iƙirarin ba su da jinsi sun fada cikin fargaba game da wani ƙudirin doka da ke Majalisar Wakilan Najeriya da ke son hana yin shigar kwaikwayo.
Ƙudirin na son yi wa Dokar Auren Jinsi kwaskwarima (SSMPA), wadda ta bayyana shigar 'yan daudu da cewa "saka tufafin da akasari ɗaya jinsin ne yake saka su".
Duk wanda aka kama da laifi zai iya fuskantar ɗaurin zaman gida yari na wata shida ko kuma tarar dala naira 500,000 - kwatankwacin dala 1,200.
Ƙudirin na nuna irin matsin da 'yan daudu ke fuskanta a Najeriya tsawon shekaru.
An saka wa dokar hannu ne a 2014, lokacin mulkin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.
Ta haramta duk wani nau'i na auren jinsi ko kuma duk wani aiki da zai nuna alamun soyayya tsakanin mutanen da ke da jinsi iri ɗaya".
Lokacin da ake muhawara kan dokar ta SSMPA shekara 10 da suka wuce, 'yan majalisar sun ce suna ƙoƙarin jaddada al'adun Najeriya ne.
Sai dai wani ɗan daudu kuma mai zana tufafi, Fola Francis, mai shekara 28, ya ce "gaskiya ƙudirin na firgita ni".
"Ƙudirin hana daudu na da matuƙar haɗari kuma zai shafi mutanen da ke iƙirarin ba su da jinsi.
Ko a yanzu ma da babu dokar tukunna, ya ce a tsorace yake inda ba ya iya zama a gidansa na tsawon watanni " saboda ina yawan samun barazanar kisa daga maƙwabtana bayan sun gano ɗan daudu ne ni a shafukan zumunta".
Bobrisky - wanda ke cikin 'yan daudu mafiya shahara a Najeriya kuma mai mabiya miliya 4.5 a Instagram - ya yi shaguɓe game da yunƙurin sauya dokar ta hanyar cewa hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaro da ɗaukewar lantarki a ƙasar, da kuma rage hauhawar farashi.
Shi ma wani tauraron daudu, James Brown, ya bayyana ra'ayinsa cewa ya kamata a tantance masu nishaɗantarwa.
"Ku yi bincike kafin ku zo kaina. Aikina shi ne nishadantawar...kar ku ɗauki ikona da wasa. Ku tambayi magoya bayana," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Ɗan majalisar Muda Lawal Ulnar ne ya gabatar da ƙuidirin. Sai dai bai faɗi babban dalilin da ya sa ya ɗauki matakin ba, yayin da ƙudirin zai shiga matakin karatu na biyu.
Sai dai ɗaya daga cikin masu goyon bayan ƙudirin, wani lauya mai suna Manfred Ekpe, ya bayyana hikimar a shafinsa.
Ya ce ya kamata a ƙyale majalisa ta saka dokokin da za su "daidaita ɗabi'un al'umma".
Da yake kawo ayoyi daga Bable da Al-Ƙur'ani, Mista Ekpe ya ce daudu kan lalata ɗabi'u da tarbiyyar matasa.
Wannan lamari bai zo wa Lolu Vangei - wadda aka fi sani da Jordyn - da mamaki ba, wata mai shekara 23 da ke ɗaukar kanta a matsayin namiji.
An yi ta tsangwamarta a bainar jama'a. "Tun kafin a gabatar da ƙudirin na yi ta samun saƙonnin tsangwama," kamar yadda ta faɗa wa BBC.
"Na taba zuwa kasuwa da rigar danne nono a jikina, amma sai wani namiji ya zo ya taɓa ƙirjina don ya ji su.
"Da na tambaye shi dalilin yin hakan sai kawai ya falla min mari kuma ya kira abokansa maza su zo su ga macen da ke shiga irin ta maza."
Sai dai shirun da suka yi na nuna yadda suke fargabar za a iya zaƙulo su.
Emerie Udiahgebi na da damuwa kan tasirin da ƙudirin zai yi idan ya zama doka, amma yana ganin ba zai sauya komai ba.
"Na san za a tilasta wa mutane da yawa, za a kama mutane da dama. Ban san sauran mutane ba, amma ba za taɓa iya manta wahalar da na sha ba kafi mutane su karɓe ni a yadda nake," in ji shi.