Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fafaroma uku ƴan asalin Afirka a tarihi
- Marubuci, Catherine Heathwood
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
Mutuwar Fafaroma Francis ta haifar da hasashen cewa sabon jagoran Cocin Katolika na iya fitowa daga nahiyar Afirka.
Amma dai Cocin ta taɓa samun 'yan Afirka a matsayin shugabanni a baya.
Masana tarihi sun yi imani cewa an taɓa samun Fafaroma uku da ke da alaƙa da nahiyar.
Ana kyautata zaton cewa dukkansu 'yan asalin Arewacin Afirka ne. Daular Roma ta shafi yankunan da a yau su ne Tunisiya da arewa maso gabashin Aljeriya, da kuma Gaɓar yamma ta Libiya.
Kafin shigowar Musulunci a ƙarni na bakwai, Kiristanci yana da gagarumar kafa a wannan yanki.
Farfesa Christopher Bellitto daga Jami'ar Kean a Amurka ya shaida wa BBC cewa: "Arewacin Afirka ita ce cibiyar addinin Kiristanci a zamanin dā."
Ko da yake ba a san abubuwa da yawa game da rayuwar Fafaroman Afirka ukun ba, masana tarihi sun amince cewa kowannensu ya taka muhimmiyar rawa a tarihin farko na Cocin Katolika.
Victor na ɗaya (189–199).
Fafaroma Victor I, wanda ake ganin asalinsa daga ƙabilan Berber ne, ya jagoranci Cocin Katolika daga shekarar 189 zuwa 199 a wani lokaci da Kiristoci ke fuskantar tsanantawa.
Ya fi shahara da warware rikicin ranar bikin Easter, inda ya nace cewa a rika gudanar da bikin a ranar Lahadi, kamar yadda Kiristoci na yammacin duniya suka amince.
Ya kira taron koli na farko na Roma domin tilasta wannan matsaya, inda ya yi barazanar korar bishof-bishof da suka ki bin umarninsa daga Coci, in ji farfesa Bellitto
Victor I ne kuma ya maye gurbin yaren Girkawa na da a matsayin harshen Coci. Duk da cewa Kiristanci ba doka ba ce a Daular Roma a lokacin, ya kasance shugaba mai karfin hali.
Miltiades (311-314)
An fi kyautata zaton cewa Fafaroma Miltiades ya fito ne daga nahiyar Afirka. A lokacin shugabancinsa, Kiristanci ya fara samun karɓuwa a wurin sarakunan Roma, har ta kai ga zama addini a hukumance na Daular Roma.
Kafin wannan lokaci, ana yawan tsananta wa Kiristoci a sassa daban-daban na Daular.
Sai dai Farfesa Bellitto ya bayyana cewa Miltiades ba shi ne ya kawo wannan sauyi ba, yana cewa Fafaroman ya amfana ne da alherin da Daular Roma ta nuna, ba wai saboda ya ƙware a tattaunawa ba.
Sarkin Roma Constantine ya bai Miltiades matsayin fada, wanda ya sa shi ya zama Fafaroma na farko da ya samu matsuguni hukumance.
Constantine ya kuma ba shi izinin gina cocin Basilica, wanda yanzu shi ne cocin jama'a wanda ya fi tsufa a birnin Roma.
Duk da cewa Fafaroma na zamani na zama ne a birnin Vatican, ana ɗaukar cocin ta Laterano a matsayin "uwa ga dukkan majami'u" a cikin addinin Katolika.
Gelasius na ɗaya (492-496)
Fafaroma Gelasius I shi ne daya tilo daga cikin Fafaroma ukun Afirka da masana tarihin addini ke ganin ba a Afrika aka haife shi ba, akwai wasu bayanai da ke nuna cewa an haife shi a Roma, ko da yake yana da asalin Afirka.
Shi ne mafi muhimmanci cikin shugabannin cocin Katolika na Afirka guda uku
Gelasius I ya kasance Fafaroma na farko da aka fara kiran sa da lakabin "Vicar of Christ," wanda ke nuna matsayin Fafaroma a matsayin wakilin Yesu a doron ƙasa.
Ya kuma tsara "Ka'idar Takubba Biyu", wadda ta raba ikon mulki da na addini, amma kuma duka suna da ƙarfi ɗaya, sai dai cocin ce ke da ikon da ya fi, domin ita ce ta fara samun iko kafin wani bangare ga gwamnati.
Fafaroma Gelasius I ya taka muhimmiyar rawa a rikicin addini da ake kira Acacian Schism (484-519), wanda ya raba cocin Gabas da ta Yamma.
Haka kuma, Gelasius I ne ya kafa bikin St Valentine na ranar masoya a ranar 14 ga Fabrairu a shekarar 496, domin tuna wa da shahadar St Valentine wanda ya ci gaba da aurar da ma'aurata a ɓoye bayan da Sarki Claudius II ya haramta auren.
Mene ne kamannin Fafaroman Afirka?
Farfesa Bellitto ya ce babu wata hanya da za a iya tabbatar da kamannin fafaroman ukun
"Dole ne mu tuna cewa Daular Roma, da kuma zamanin jahiliya ba su ɗauki batun kabila kamar yadda muke ɗaukar sa a yau ba. Bai da wata alaƙa da launin fata," in ji shi lokacin da yake magana da BBC.
Farfesa Philomena Mwaura, Malamar Kimiyyar Addini a Jami'ar Kenyatta da ke Nairobi, ta bayyana cewa yankin Afirka ta Roma ya kasance mai ɗimbin al'adu daban-daban da suka haɗa da Berber da Punic da bayi da aka 'yanta, da kuma mutanen da suka fito daga Roma.
"Al'ummar Arewacin Afirka sun kasance jama'a daga sassa daban-daban, kuma yankin wata hanya ce ta kasuwanci ga mutane da dama tun a tsohon zamani," in ji ta a wata hira da BBC.
Me ya sa har yanzu babu wani sabon Fafaroma daga Afrika?
Bayan Gelasius I, babu wani Fafaroma da ake ganin ya fito daga lardin Afirka na Daular Roma.
"Cocin da ke Arewacin Afirka ta raunana saboda dalilai da dama, ciki har da faduwar Daular Roma da kuma zuwan Musulmi yankin a ƙarni na bakwai," in ji Farfesa Mwaura.
Sai dai wasu masana na ganin cewa yawaitar Musulunci a yankin ba ya bayyana dalilin rashin samun Fafaroma daga Afirka tsawon shekaru dubu biyu da suka gabata.
Farfesa Bellitto ya ce tsarin zaɓen sabon Fafaroma na Italiya kawai ake amfani da shi tsawon shekaru.
Amma ya ce akwai yiwuwar samun Fafaroma daga Asiya ko Afirka a cikin shekaru masu zuwa, domin yanzu Kiristoci da ke Kudancin duniya sun fi yawan na Arewa.
Sabbin alkaluma sun nuna cewa a shekara ta 2023, akwai Katolika miliyan 281 a Afirka — wanda ya kai kashi 20 cikin ɗari na dukan mabiya Katolika a duniya.
Amma Farfesa Mwaura ta ce "ko da yake Kiristanci yana da ƙarfi a Afirka, ikon Cocin yana nan a Arewacin duniya, inda dukiya da albarkatu suka fi yawa."