Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Ɗage zaɓen gwamnoni, cire sunan Doguwa da kashe masunta 30
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da 'yan majalisun jihohi
A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris.
INEC ta tabbatar wa da BBC ɗage zaɓen, bayan wani taron gaggawa da manyan jami'an hukumar suka yi a Abuja.
A wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun jami'in yaɗa labaru da wayar da kai na hukumar, Festus Okoye, ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun damar sanya sabbin bayanai a cikin na'urorin BVAS da za a yi amfani da su a zaɓen mai zuwa.
Bako Haram sun kashe masunta 30 a jihar Borno
Haka kuma a ranar Larabar da ta gabata ne mayaƙan Boko Haram masu kiran kansu ƴan ƙungiyar IS a yankin Afirka ta yamma wato ISWAP suka hallaka wasu fararen hula akalla 30.
Lamarin dai ya faru ne a yankin ƙaramar hukumar Gamborun Ngala lokacin mutanen da galibi manoma ne da masunta suka fita neman abin da za su ci.
An kai harin ne kusa da garin Mukdolo wanda ke kusa da wata matattarar ƴan Boko Haram inda mutanen suka shiga don kamun kifi da kuma neman itacen wuta.
Bayan mutanen kusan talatin da maharan suka kashe, akwai waɗanda suka tsira amma da raunukan bindiga da kuma wasu da rahotanni suka ce ba a san inda suke ba har yanzu.
INEC za ta ɗaukaka ƙara kan amfani da katin zaɓen wucin-gadi
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya ta ce tana shirye-shiryen ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu wanda ya bai wa waɗanda suka shigar da ƙara damar yin zaɓe da katin zaɓe na wucin-gadi.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na tuwita, INEC ta ce “an kai mata hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, wanda ya bai wa waɗanda suka shigar da ƙarar damar yin amfani da katin zaɓensu na wucin-gadi wajen kaɗa ƙuri’a.”
Bayanin ya ƙara da cewa “Hukumar na duba matakan da suka kamata ta wajen ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.”
A ranar Alhamis ne mai shari’a Obiora Egwuatu ya bai wa masu shigar da ƙarar gaskiya, inda ya ce suna da ƴancin amfani da katunansu na wucin-gadi domin kaɗa ƙuri’a.
Akwai shirin tayar da hankali a zaɓen gwamnoni - DSS
Hukumar 'yan sandan ciki ta DSS ta ce akwai shirin da wasu mutane ke yi na tayar da hankali a wasu sassan ƙasar a zaɓen gwamnoni da ke tafe.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Peter Afunanya ya fitar a ranar cikin makon da muke bankwana da shi, ta gargaɗi mutane ko ƙungiyoyi da su guji yin duk abin da zai tayar da hankali domin kauce wa fushin hukuma.
A don haka DSS ɗin ta ja kunnen 'yan siyasa da su zama masu bin doka da oda a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke shirin fita rumfunan zaɓe domin zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Maris.
INEC ta cire sunan Doguwa daga jerin zaɓaɓɓun 'yan majalisun tarayya
Haka kuma a makon da ya gabatan ne hukumar zaɓen Najeriya ta bayar da shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun 'yan majalisar wakilai da suka yi nasara a zaɓen ranar 25 ga watan jiya.
To sai dai hukumar zaɓen ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan ƙasar Alhassan Ado Doguwa daga cikin jerin sunayen zaɓaɓɓeun 'yan majalisar.
Hukumar zaɓen ƙasar ce dai tun da farko ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
To amma a jerin sunayen zaɓaɓɓun 'yan majalisun da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na Twitter, babu sunan Alhassan Ado Doguwa a cikin jerin 'yan majalisun.
INEC ɗin ta ce an tilasta wa jami'in tattara sakamakon zaɓen wajen bayyana sakamakon da ya bai wa Doguwa nasara a zaɓen da aka gudanar.