Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle da Bayern da Chelsea na son Olise, Virgil na son komawa Saudiyya
Kungiyoyin Newcastle, Bayern Munich da Chelsea na son dan wasan tsakiya na Cystal Palace Michael Olise, tun da fari dai Newcastle da Bayern Munich ne suka fara tuntubar Palace kan dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 22 da ta ke niyyar saidawa. (Athletic - subscription required)
Daga nan ne a ranar Alhamis Chelsea ta tuntubi Palace kan Olise. (Mirror)
Dan wasan Chelsea, na Ingila ajin 'yan kasa da shekara 21 Noni Madueke, mai shekara 22, na cikin wadanda Newcastle ke so da zarar an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa. (i Sport),
Kungiyar Alnassr ta Pro League din Saudiyya na son dan wasan Liverpool kuma na bayan Netherlands, Virgil van Dijk akan farashi mafi tsoka kan wani dan wasa a duniya (Marca)
Manchester United ana son dan wasan Bayern Munich da Netherlands Matthijs de Ligt mai shekara . (Sky Sports Germany)
Manchester United na son dan wasan Faransa Frenchman Jean-Clair Todibo of Nice, ita ma kungiyar Ineos own na son dan wasan mai shekara 22, a kokarin karfafa 'yan wasanta na baya. (Mail)
Manchester United na son dan wasan Bologna mai kai hari a Netherlands Joshua Zirkzee, 23, a kakar wasan nan, sai dai za su fafata da Juventus da AC Milan da su ma ke son dan wasan. (Telegraph - subscription required)
Liverpool da Manchester United na son matashin dan wasan baya na Faransa Leny Yoro, mai shekara 18, to amma ita ma kungiyar Real Madrid na son dan wasan. (Athletic - subscription required)
Kungiyoyin Tottenham, Aston Villa da West Ham na son dan wasan Ingila mai taka leda a Roma, Tammy Abraham, 26. (Telegraph - subscription required)
Aston Villa na son saida mai kai hari Jhon Duran akan farashin fam miliyan 40, tuni Chelsea ta fara tattaunawa kan sayan shi. Sau uku kacal dan wasan dan Colombia ya taba halartar gasar Premier League tun watan Junairun 2023. (Times - subscription required)
Sabon shugaban Fenerbahce boss Jose Mourinho na son dauko dan wasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 28, wanda ke taka leda a Tottenham. (Takvim - in Turkish, subscription required)