Ɗan takarar Turkiyya mai taushin murya da ke ƙalubalantar Erdogan mai ƙarfin iko

Mutumin ya kuma kasance mai natsuwar da a wasu lokuta yakan shiga ran abokan aikinsa, a cewar wani na hannun damarsa.

Kuma duk da haka Kemal Kilicdaroglu mai shekara 74 – na da dama mai tarin yawa ta karbe ragamar mulki daga hannun mutum mafi karfin iko a Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, tun bayan da ya karbi mulki shekaru 20 da suka gabata.

Tsohon ma’aikacin gwamnati mai magana da taushin murya, ya bambanta kwarai da shugaban Turkiyya mai nuna isa da karfin iko.

Ya sha faduwa zabe tun bayan da ya karbi shugabancin jam’iyyar Republican People's Party (CHP) a shekarar 2010, lokacin da aka tilasta wa wanda ya gabace shi sauka saboda aikata laifin neman matan waje.

Baya da haka kuma, Kemal Kilicdaroglu gogaggen dan siyasa ne.

An zabe shi a shekarar 2002, shekarar da jam’iyyar AK mai mulki ta Mr Erdogan ta karbi mulki.

Ya tsira daga jerin munanan hare-hare, da suka sa shi zama mai tagomashin kasancewa dan siyasar Turkiyya da aka fi kai wa hari.

A shekaru 13 da ya shafe a matsayin shugaba ya kara fadada harkokin jam’iyarsa tare da tafiya da dukkanin bangarorin kasar, " kamar yadda yake bayyanawa.

An jima ana danganta jam’iyar CHP da kasancewa mai kusanci da rundunar sojin kasar, wacce ta hambarar da gwamnati sau hudu a shekarar 1960.

Kuma a ko da yaushe ana yi mata kallon jam’iya mai tsauri a kan batutuwan da ke raba coci da kasar.

Bayan juyin mulki a shekarar 1980, alal misali, ya goyi bayan haramta saka dankwali ko hijabi a makarantu da wuraren aikin gwamnati.

An haifi Kemal Kilicdaroglu a watan Disambar shekarar 1948, kuma shi ne na hudu a cikin ‘ya'ya bakwai da wata mata ma’aikaciyar gwamnati a birnin Tunceli da ke gabashi ta haifa.

Ya fito ne daga iyalan Alevi – wata kungiyar addinin Islama, kana Musulmai ‘yan tsiraru masu akidar Sunni na kasar Turkiyya.

Ya kasance tauraron dalibi a makarantu da dama da ya halarta, kuma ya yi karatu ne a fannin tattalin arziki a Jami’ar Ankara.

Ya shafe shekaru a matsayinsa maa’aikacin gwamnati a ma’ikatun kudi na Turkiyya kuma ya samu lambar yabo kan magance matsalar cin hanci da rashawa a matsayinsa na daraktan hukumar kula da harkokin inganta rayuwar al’umma.

Cikin shekara guda da samun wadannan nasarori, shugaban jam’iyar ta CHP ya yi murabus bayan da wani hoton bidiyo na sirri kan neman wata mace ya bayyana.

Kuma Mr Kilicdaroglu ba zato ba tsammani ya samu kansa a matsayin firaminista na wannan aiki.

Recep Tayyip Erdogan yanzu na kan kololuwarsa ta mulki, inda ya zama firaministan Turkiyya mafi samun nasarori a wannan zamanin, ta hanyar samun rabin kuri’u a zaben Jam’iyar AK a zaben shekarar 2011.

Jam’iyar CHP ce ta zo ta biyu, amma ta kara yawan kuri’unta da kashi biyar bisa dari.

Amma a shekaru 13 da ya yi yana jagoranci, ya yi ta kokarin samar da wanzuwar zaman lafiya da masu tsattsauran ra’ayin addinin Isalama ta hanyar nuna dattaku wajen halartar liyafar buda-baki lokacin azumin watan Ramadan.

Wani abokin tafiyarsa a jam’iyar ya shaida wa BBC cewa bai taba daga muryarsa ba.

"A wasu lokutan abubuwa kan matukar bata mana rai, kuma ba yadda muka iya dole mu daga murya. Amma duk da haka Kilicdaroglu yakan ci gaba da kasancewa a cikin natsuwa,’’ in ji shi.

Da zarar wani ya shiga cikin dakin , yakan tsaya a tsaye ya yi hannu da shi, ba ya taba yin magana da mutane yayin da yake zaune a kan teburinsa, kuma ba ya taba katse hanzarin kowa, a cewar abokan huldarsa.

Wannan halayya ta kasancewa mai sanyin zuciya da kuma yanayi da shugaban kasar India ya sa aka lakaba masa suna Gandhi Kemal.

Ya tsira daga yunkurin lakada masa duka a shekarar 2019 a wurin jana’izar wani soja.

Lokacin da aka kai masa hari, an garzaya da shi zuwa wani gida mafi kusa inda wata mata ta yi kira ga taron jama’ar da su banka wa gidan wuta.

Lokacin da ‘yan sanda suka kai shi tudun-mun-tsira, ya bayyana daga baya cewa: "Wadannan yunkuri ba za su iya taka mana birki ba.’’

Amma sai bayan juyin mulkin 2016 da bai samu nasara ba ne mutuncin Kemal Kilicdaroglu ya karu a fiye da kasar Turkiyya.

A yayin da Shugaba Erdogan ke cafke masu aikata laifukan cin amanar kasa, da korar dubban Turkawan da ake yi wa kallon masu alaka da wadanda suka yi yunkurin juyin mulki, jagoran adawa ya kaddamar da tattakin neman yin adalci da aka yi wa lakabi da "March for Justice", tattakin kilomita 450 daga birnin Ankara zuwa Istanbul.

Duk da samun nasarar tattakin nasa, ya zabu kasa ya kalubalanci shugaban kasa shekara guda bayan nan, yana mai jiran wasu shekaru biyar na samun wata damarsa.

Ya dauki tsawon watanni kafin ya ja hankalin jam’iyun adawa na su goyi bayan yunkurinsa.

Jam’iyar CHP ta fi fitattun masu fitowa su yi magana, da kuma fitattun mutanen da suka samu galaba a zaben zama magadan garin biranen Istanbul da kuma Ankara.

Ya kuma samu galaba wajen hada kawunan jam’iyun adawa shida – wadanda in ba haka ba abu kalilan ne suke da shi iri daya - bayan shi.

"Ban taba jin wata kalma ta kiyayya na fitowa daga bakinsa ba. Wani zai iya bata masa rai amma yakan natsu kana ya yafe wa mutum nan da nan,’’ a cewar Okan Konuralp.

"Da haka yakan yi aiki tare da ‘yan siyasar da ke tsananin hamayya da shi a baya.’’