Shugaban kanfanin TikTok ya gargadi Amurka kan haramta shafin

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kamfanin shafin sada zumunta da muhawara na TikTok ya ce, kamfanin zai yi duk abin da zai iya domin kare kansa, bayan da majalisar wakilan Amurka ta amince da wani kudurin doka, da zai iya kaiwa ga haramta amfani da shafin a Amurka.
Fadar Gwamnatin Amurka, White House, ta yi kira ga 'yan majalisar dattawa da su gaggauta amincewa da kudurin, wanda 'yan majalisa suka ce zai kare Amurkawa daga barazanar alakar TikTok din da gwamnatin China.
A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafin na TikTok, shugaban kamfanin Shou Zi Chew ya yi gargadin cewa muddin aka zartar da wannan doka, to dokar za ta kai ga hana amfani da shafin gaba daya a Amurka.
A don haka ya ce, kamfanin zai yi amfani da dama da ‘yancin da yake da shi na doka ya kare shafin da kuma Amurkawa miliyan 170 da suke amfani da shi.
Mista Chew ya ce manufar matakin kawai haramta amfani da manhajar ne.
Ya ce : ''Wannan dokar, idan aka amince da ita za ta kai ga hana amfani da TikTok ne a Amurka. Hatta ma wadanda suka kawo kudurin sun yadda cewa burinsu kenan. Wannan kudurin doka ya bayar da karin iko ga wasu kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara ‘yan kadan. Haka kuma zai raba masu kirkira da masu kananan harkokin kasuwanci biliyoyin dola. Zai kuma jefa aikin Amurkawa sama da dubu 300 cikin hadari, kuma zai dauke TikTok dinku.''
Fadar gwamnatin Amurka, White House ta ce tana goyon bayan kudurin dokar, da zai bai wa masu shafin ‘yan China damar kusan wata shida ta ko dai su sayar da shafin ko kuma su fuskanci haramcin amfani da shi a wayoyi.
‘Yan majalisar na daukar shafin a matsayin wata barzana ga tsaron Amurka.
Kamfanin na TikTok ya musanta alaka da gwamnatin China, ya kuma bukaci masu amfani da shafin a Amurka, da su yi ta kiran wayoyin ‘yan majalisar, su bukace su da su yi watsi da wannan doka.













