Tagwayen da Tiktok ya sake haɗawa bayan sace su tun suna jarirai

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
    • Marubuci, By Fay Nurse and Woody Morris
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Amy da Ano tagwaye ne masu kama da juna, to sai dai jim kaɗan bayan haihuwarsu sai aka sace su daga wajen mahaifiyarsu aka kuma sayar da su ga iyalai daban-daban.

Tagwayen sun sun gano juna sakamakon ashirin wani gidan talbijin da ke nuna kyawawan bidiyoyin TikTok.

Yayin da suka shiga cikin abubuwan da suka faru a baya, sun fahimci cewa suna cikin dubban jarirai a Jojiya da aka sace daga asibitoci aka sayar, wasu a baya-bayan nan kamar a shekarar 2005. Yanzu suna sonin wasu amsoshi.

Amy na aiki ne a wani otal a birnin Leipzig. "Na tsorata kwarai da gaske''kamar yadda ta bayyana a firgice. ta ƙara da cewa ba ta yi barci ba tsawon mako guda

''Wannan ce damata ta ƙarshe ta samun wasu amsoshi game da abin da ya faru da mu."

'Yar'uwarta, Ano, na zaune a kan kujera, tana kallon bidiyon TikTok a cikin wayarta. "Na tabbata wannan ce matar da ta sayar da mu'', ta bayyana yayin da take zare idanu.

Ano ta yarda cewa tana cikin tashin hankali, amma ba ta san yadda za ta yi ba ko yadda za ta iya ɓoye ɓacin ranta.

An yi tafiya daga Jojiya a Amurka zuwa Jamus, da nufin gano tagwayen da suka ɓacewa juna, aɗanda a ƙarshe suka sake haɗuwa da mahaifyarsu.

Shekaru biyu da suka gabata sun yi ƙoƙarin adana abin da ya faru. Yayin da suke bayyana gaskiya, sun gano cewa suna cikin dubban jariran da aka ɗauke su daga asibitoci aka kuma sayar da su shekaru masu yawa da suka gabata.

Duk da yunkurin da hukumomi suka yi na gudanar da bincike kan abin da ya faru, har yanzu babu wanda aka tuhume shi da laifi.

Labarin yadda Amy da Ano suka gano juna ya fara tun suna da shekara 12.

Wata rana Amy Khvitia na zaune a gidan uwar ɗakinta a kusa da tekun Maliya, tana kallon wani shirin talabijin da ta fi so. Kwatsam sai ga wata yarinya tana rawa mai kama da ita. Ba ma kama kawai bar ta ba, a zahiri ta ga tamkar ita ce.

Amy Khvitia here aged four

Asalin hoton, Amy Khvitia

Bayanan hoto, Amy Khvitia, lokacin tana shekara huɗu, ta ce a koyaushe tana jin cewa akwai wani abu maras daɗi a rayuwarta.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Sai kowa ya riƙa kiran mahaifiyata yana tambaya: 'Ya muka ga Amy tana rawa da wani suna na daban?'" in ji ta.

Amy ta gaya wa 'yan uwanta abin da ta gani, amma ba su kula ta ba. "Kowa yana ce mai kama da ita ne," in ji mahaifiyarta.

Shekara bakwai bayan haka, a cikin Nuwamba 2021, Amy ta wallafa wani bidiyonta da shuɗin gashi da gashin gira a shafinta na TikTok.

Can kuma a Tbilisi mai nisana kilomita 320 daga inda Amy take rayuwa, wani mutum ne ya aika wa Ano Sartania, tunaninsa ita ce saboda yadda suka yi kama da juna.

Ano ya yi kokarin gano yarinyar da ke cikin bidiyon a shafukan intanet, amma ba ta yi nasara ba, don haka ta tura bidiyon zuwa wani zauren whatsapp na ƙawayenta na jami'a ko za ta samu mai mai taimakamata. Daga nan ne wani da ya sa san Amy ya ga saƙon inda kuma ya haɗa su ta shafin Facebook.

Nan take Amy ta fahimcvi cewa Ano ce yarinyar da take gani a duka tsawon waɗannan shekarun da suka gabata a shirin talbijin ɗin.

"Na dade ina nemanki!" Na yi ta turo miki saƙo. "Ni ma haka" Ano ta amsa.

A cikin 'yan kwanaki masu zuwa, sun gano cewa suna da abubuwa masu yawa da suka yi kamanceceniya da juna, amma ba komai ba.

An haife su ne a asibitin haihuwa na Kirtskhi - wanda a yanzu aka rufe shi - a yammacin Jojiya, amma takardun haihuwarsu, sun nuna cewa an haife su tsakanin makonni.

Suna son kiɗan iri ɗaya, dukansu suna son rawa, kuma suna da salon gashi iri ɗaya. Sun gano cewa suna da cututtukan kwayoyin halitta iri ɗaya, cutar ƙashi da ake kira 'dysplasia'.

Labarinsu ya yi kamar tare suke tona wani asiri. "Duk lokacin da na koyi wani sabon abu daga Ano, nakan ji su kamar baƙi," in ji Amy.

Ano (L) and Amy (R) standing in front of graffiti wall

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, Ano (Hagu) da Amy (Dama) sun gana a karon farko a Rustaveli, kuma suna sha'awar yin salon gashi iri guda.

Sun shirya haɗuwa bayan mako guda, inda tagwayen suka gana da juna tashar jirgin karon faro.

Amy ta ce "Kamar madubi na kalla , fuska ɗaya, murya ɗaya. Ni ce ita, kuma ita ce ni," in ji Amy. Ta tabbata cewa lallai su tagwaye ne.

"A ɗabi'ata ba na son runguma, amma na rungume ta," in ji Ano.

Sun yanke shawarar su fuskanci iyalinsu kuma sun gano gaskiya. Inda suka taso a hannun iyaye daban-daban, makonnin farko cikin shekarar 2002.

Amy ba ta ji daɗi ba kasancewar ta gano cewa duka rayuwar da ta yi a baya ƙarya ce. Sanye da baƙaƙen tufafi, ta ce ba ta ji daɗin yadda abubuwa suka kasance ba, yayin da take goye hawaye a fuskarta, "Labari ne mars daɗi," in ji ta. "Amma gaskiya ne."

Ano ta yi "fushi tare da jin haushin iyalina, amma na fi so mu ƙare wannan hirar maras daɗi, mu kuma tunkari raytuwarmu ta gaba''.

Da aka zurfafa bincike, tagwayen sun gano cikakkun bayanai kan takardun haihuwarsu na hukuma, ciki har da ranakun haihuwarsu duka ba daidai ba ne.

Sakamakon rashin haihuwa, uwar da ta riƙe Amy ta ce wata kawarta ce ta gaya mata cewa akwai wata jaririya da ba a buƙata a asibitin yankin idan tana so. Amma za ta buƙaci biyan likitocin kafin ta ɗauketa ta kuma reneta a gidanta.

Haka nan kuma aka gaya wa uwar da ta riƙe Ano kafin ta ɗauketa.

Duka iyalan da suka ɗauki jariran ba su son cewa tagwaye ba ne, duk kuwa da maƙudan kuɗaɗen da suka biya kafin samun yaran, sun ce ba su taɓa tunanin cewa abin da suka yi ya saɓa doka ba.

Duka iyalan ba su bayyana adadin kuɗin da suka biya kafin a ba su jariran ba.

Tagwayen sun shiga ruɗani game da mamakin yadda mahaifansu za su sayar da su saboda kuɗi.

Tamuna Museridze in red jacket standing in the site of a hospital

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, Tamuna Museridze ta kafa wani shafi a Facebook domin neman 'yan uwan juna da suka rabu.

Amy na son su nemo mahaifiyarsu domin gano haƙiƙanin abin da ya faru, to amma Ano ba ta so.

''Me ya sa za mu nemi mutumin da ya ci amanarmu''? in ji ta

Amy ta gano wani shafin Facebook da ke aikin sake haɗa iyalai da yaransu da aka yi zargin cewa an ɗauke su ta hanyar da ba ta dace ba suka kuma taso a hannun wasu iyayen. Inda ta wallafa labarinsu a shafin.

Sai wata matashiya a Jamus ta yi mata tsokaci, da cewa mahaifiyarta ce ta taɓa haihuwar tagwaye mata a asibitin haihuwa na Kirtskhi a shekarar 2002, kuma duk da cewa an gaya mata cewa sun mutu, matar tana da shakku game da hakan.

Gwajin ƙwayoyin halitta da aka yi wa matashiyar da ta yi tsaokacin a Facebook, ya nuna cewa 'yar uwar tagwayen ce, kuma ita tana zauen da mahaifiyarta mai suna Aza a ƙasar Jamus.

Amy ta zaƙu ta gana da Aza, amma Ano tana taka-tsantsan ''Wanna fa ita ce matar da wataƙila ta sayar da mu, ba za ta gaya mana gaskiya ba ne,'' tana mai gargaɗin 'yar uwar tata. Duk kuwa da cewa ta amince ta bi Amy zuwa Jamus don gano gaskiya.

Shafin Facebook da tagwayen suka wallafa saƙon nasu, ya samu saƙonni daga mataye daban-daban da ke cewa sun taɓa haihuwar tagwaye a asibitin, inda ma'aikantan asibitin suka shaida musu cewa tagwayen nasu sun mutu, amma daga baya sun gano cewa ba a shigar da bayanan rasuwar 'yayan nasu cikin rajistar mutanen da suka mutu a asibitin ba.

Sauran saƙonnin da aka wallafa a shafin daya wasu tagwaye ne irin su Amy da Ano da ke neman iyayensu na ainihi.

Shafin ya samu fiye da mambobi 230,000.

Wata 'yar jarida ce mai suna Tamuna Museridze ta ƙirƙiro da shafin a shekarar 2021, bayan da ta gano cewa ta taso ne a hannun iyayen riƙo, ta gano cewa bayanan da ke cikin takardar haihuwarta ba na gaskiya ba ne, a lokacin da take share ɗakin uwar riƙon tata.

Ta fara wallafa shafin ne domin neman danginta, to amma daga ƙarshe an yi amfani da shafin wajen fallasa yadda ake safarar jarirai, lamarin da ya shafi dubban mutane cikin gomman shekaru.

A Georgian sign over a hallway in a derelict hospital

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, Asibitin haihuwa na Gurjaani na ɗaya daga cikin asibitoci aƙalla 20 da aka samu da sayar da jarirai.

Shafin da Ms Tamuna ta buɗe ya taimaka matuƙa wajen haɗa daruruwan iyalan da danginsu, to amma har yanzu ita ba ta dace ba.

Tamuna ta gano wani kasuwart bayan fage da ake harƙallar sayar da jarirai a Jojiya, wanda aka fara gudanarwa tun farkon shekarun 1950 zuwa 2005.

Ta ce wasu gungun ɓata gari ne ke gudanar da kasuwar, wadda ta ƙunshi rukunin mabambantan mutane kama daga direbobin tasi zuwa mutanen da kle riƙe da madafun iko a gwamnati.

"Girman ba ya misaltuwa, jariran da aka sace sun kai 100,000 . Lamarin tsararre ne," in ji ta.

Tamuna ta ce ta haɗa waɗannan alƙaluma ne ta hanyar mutanenda suka tuntuɓeta kan matsalar tare da tsawon lokacin da ka ɗauka ana gudanar da harƙallar a ƙasar.

Sakamakon rashin takardu, wasu sun rasa 'yan uwansu ba tare da wani bayani ba, don ahaka abu ne mai wuya a gano haƙiƙanin alƙaluman.

Tamuna ta ce iyaye masu yawa sun shaida mata cewa idan suka tambayi likitocin gawrwakin jariran nasu , sai su ce musu an riga an binne su a asibitin. Daga baya kuma ta gano cewa babu maƙabartu a asibitocin Jojiya.

Wasu matan kuma akan nuna musu gawarwakin wasu jariran da aka riga aka daskarar a ɗakunan ajiye gwarwaki, ace musu na jariran nasu ne.

Irina Otarashvili in her garden

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, Irina Otarashvili ta haifi tagwaye a 1978 - Inda aka ce mata sun rasu, amma tana shakkar cewa ƙarya aka yi mata.

Tamuna ta ce jarirai na da tsada, domin kuwa ana kashe kusan albashin shekara guda kafin tara kudin sayen jariri. Ta gano cewa ana sayra da wasu jariran zuwa ƙasashen ƙetare kamar su Amurka da Canada da Cyprus da Rasha da kuma Ukraine.

A shekarar 2005 Jojiya ta sauya dokokinta game da riƙo 'ya'ya, tare da ƙarffa dokokin safarar jarirai, lamarin da ya sa ɗaukar jarirai ba bisa ƙa'ida ta ƙara tsauri.

Wata mata da ke neman amsa game da tagwayen da ta haifa ita ce Irina Otarashvili, ta haifi tagwaye maza a asibitin haihuwa na Kvareli da ke kusa da tsanukan Caucasus a shekarar 1978.

Likitoci sun gaya mata cewa duka jariran nata suna cikin ƙoshin lafiya, to amma sakamakon wasu dalilai da ba su gaya mata ba, za a ajiye su wani wuri nesa da ita.

Kwana uku bayan haka, aka shaida mata cewa sun mutu. Inda likitocin suka ce sunj gamu da matsalar numfashi.

Irina's daughter Nino Elizbarashvili stands next to a suitcase and a shovel in the garden

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, 'Yar gidan Irina, Nino Elizbarashvili ya ce ta yi tunanin cewa binne 'yan uwanta aka yi a cikin lambun asibitin.

A cikin wani otal a birnin Leipzig na ƙasar Jamus Amy da Ano na shirin ganawa da mahaifiyarsu. Ano ta ce ta sauya tunaninta, a yanzu tana son haduwa da mahaifiyarta.

Mahaifiyar tasu mai suna Aza, tana jira a cikin wani ɗaiki cikin zaƙuwa domin sake arba da tagwayen da ta rasa tun suna jarirai

Amy ta buɗe kofar ɗakin Ano ta biyo ta a baya, har ma tana tura ta cikin ɗakin.

Aza ta yi murmushi tare da rungumarsu, a lokaci guda, sun kwashe mintuna masu yawa ba tare da yin magana ba.

Ano, Aza and Amy embrace

Asalin hoton, BBC/ Woody Morris

Bayanan hoto, Ano (Hagu), Aza (tsakiya) da kuma Amy (Dama) sun gana da juna karon farko a birnin Leipzig na ƙasar Jamsu, inda Aza ke zaune a yanzu.

Hawaye sun cika fuskar Amy, amma Ano ko gezau, fuskarta tamkar ma fushe take yi.

Daga nan suka zaune domin su yi magana a tsakaninsu.

Daga baya tagwayen sun ce mahaifiyar tasu ta ce ta gamu da jinya bayan haihuwarsu, a lokacin da likitoci suka shaida mata cewa tagwayen da ta haifa sun rasu.

Ta ce sake haɗuwa da tagwayen nata ya buɗe mata sabon babi a rayuwarta, ta ƙara da cewa ta ji daɗi yadda tagwayen nata suka riƙa magana da juna duk da cewa ba sa wuri guda.

A shekarar 2022, gwamnatin Jojiya ta ƙaddamar da wani bincike na tarihi kan matsalar safarar ƙananan yara.

Gwamnatin ta shaida wa BBC cewa ta yi magana da fiye da mutum 40 game da batun, amma da alamu duka batutuwansu tsoffin batutuwa ne.

BBc ta tuntuɓi ministan cikin gida na Jojiya kan ƙarin bayani game da batun, amma sai aka shaida mana cewa ba za a iya magana kan lamarin ba, saboda dokar kare bayanan mutane

A yanzu Tamuna ta haɗa hannu da lauyan kare haƙƙin bil-adama Lia Mukhashavria domin ƙwatowa mutanen da irin wannan lamari ya shafa a kotunan ƙasar.

Suna fatan cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalar.''A koyaushe nakan ji cewa akwai wani abu da na rasa a rayuwata'', in ji Ano.

''Na sha yin mafarki kan yarinyar da nake gani a talbijin tana rawa wadda nake ganinta tamkar ni ce'', in ji ta.

Amma ta ce wannan tunani nata ya gushe a lokacin da ta gano Amy.