Mutum hudu sun mutu, wasu da dama sun bace a hadarin jirgin ruwan Indonesiya

Lokacin karatu: Minti 2

Akalla mutum hudu ne suka mutu, wasu da dama kuma sun bace bayan wani jirgin ruwa ya nutse a tsibirin Bali na kasar Indonesiya.

Jirgin na dauke da fasinjoji 53 da ma'aikata 12 a lokacin da ya nutse da misalin karfe 23:20 agogon kasar a ranar Larabar a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bali daga Banyuwangi da ke gabar tekun gabashin tsibirin Java, kamar yadda ofishin Hukumar Bincike da Ceto ta kasar Surabaya ya bayyana.

Aikin ceto ya fuskanci cikas saboda tsagewar tekuna da duhu.

An gano fasinjoji hudu a karamin jirgin ruwan da ake karawa iska da sanyin safiyar Alhamis yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka tsira.

Hotunan da Kamfanin Dillancin Labarai na Antara ya wallafa sun nuna motocin daukar marasa lafiya a cikin shirin ko ta kwana da mazauna garin suna jiran samun bayanai a bakin hanya.

Hukumomi na binciken musabbabin nutsewar jirgin.

Kamfanin da ya mallaki jirgin ya shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa jirgin ya ba da rahoton matsalar inji jim kadan kafin ya nutse.

Sau da yawa mazauna yankin suna amfani da hanyar jirgin da ke tsakanin tsibiran Java da Bali.

Mutanen hudu da suka tsira dukkansu mazauna Banyuwangi ne, in ji tawagar binciken Surabaya.

Hatsarin ruwa na yawan afkuwa a Indonesiya, wadda kasa ce mai tsibirai kusan 17,000, inda an dade ana nuna damuwa kan rashin aiwatar da ka'idojin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji

Wata mata 'yar Australia ta mutu a watan Maris a lokacinda wani kwale-kwale ya kife a Bali dauke da mutane 16.