An sallami Kean daga Asibiti bayan da ya faɗi ana tsaka da wasa

Lokacin karatu: Minti 1

An sallami dan wasan Fiorentina, Moise Kean daga asibiti, wanda ya faɗi ana tsaka da wasan da Hellas Verona ta yi nasara 1-0 a gasar Serie A.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi, lokacin da gwiwar Pawel Dawidowic ta buge shi a fuska, nan take ya faɗi kasa a sume.

An duba lafiyar ɗan wasan mai shekara 24 a cikin fili daga baya aka amince ya ci gaba da fafatawar.

Nan take sai ya zame ya faɗi kasa, daga nan ƴan wasan ɓangaren biyu suka kira masu kula da lafiyar ƴan wasa da zarar an ci karo da cikas a cikin fili.

Ɗan wasan, wanda shi ne na biyu a cin ƙwallaye a Serie A mai 15 a raga a bana, an ɗauke shi a kan gadon marasa lafiya zuwa motar da ta kai shi asibiti.

Fiorentina ta tabbatar da cewar ''A tsakar daren Lahadi aka sallami Kean daga asibiti a Verona, yana kuma kara samun sauki.''

A watan Disamba an taɓa fuskantar irin wannan matsalar, inda ɗan wasan Fiorentina, Edoardo Bove ya faɗi a cikin fili ana tsaka da wasa da Inter Milan, har sai da ta kai an soke fafatawar.

Daga baya likitoci suka yi wa Bove tiyata, inda suka sa masa wata na'urar da take taimaka masa yin numfashi, domin zuciyarsa ta ci gaba da aiki yadda ya kamata.