‘Sai da izinin miji’: Tsauraran matakan da ke hana matan Iran samun aiki

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Faranak Amidi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai rahoto kan harkokin mata, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
"Lokacin da na je neman aiki aka ce min dole ne sai na kai izinin mijina a rubuce domin a samu tabbacin cewa shi ne ya amince kafin na yi aiki", in ji Neda, wadda ta yi digiri biyu a harkar man fetur da gas a ƙasar Iran.
Ta ce ta ji tamkar an ci fuskarta ne.
"Na ce musu ni fa mai hankali ce, zan iya yanke wa kaina hukunci kan abin da nake so."
Wannan abu ne da mata suke yawan fuskanta a Iran. Matan aure a Iran na buƙatar izinin mazansu kafin su samu aiki - wannan ɗaya ne daga cikin manyan ƙalubalen da suke fuskanta a lokocin da suke son su fara aikin gwamnati ko na kamfani.
Wani rahoton Bankin Duniya na shekara ta 2024 ya lissafa Iran a matsayin ƙasa mafi tsanani idan ana batun matsalolin wariyar jinsi a harkar ƙwadago (Yemen da Gaza ne kawai lamarin ya fi na Iran muni).
Kuma wasu nazarce-nazarce sun ambato hakan. Wani rahoto kan giɓin da ake samu sanadiyyar bambancin jinsi na Ƙungiyar lura da tattalin arziƙi ta duniya a 2024, ya nuna cewa Iran ce ta fi mafi ƙanƙantarr yawan matan da ke shiga harkar ƙwadago a cikin ƙasashe 146 da aka yi nazari a kai.
Alƙaluma a shekarar 2023 sun nuna cewa, duk da cewa mata ne ke da kashi 50 cikin ɗari na ɗaliban da ke kammala karatun jami'a, amma matan na da kashi 12 cikin ɗari ne kacal na yawan ma'aikata a ƙasar.
Dokokin da suka shafi jinsi da kuma cin zarafin lalata da kuma tsangwamar da ake yi wa mata saboda jinsinsu sun sanya mata ba su jin daɗin shiga harkar ayyukan gwamnati.
Yawancin matan da BBC ta tattauna da su domin rubuta wannan labari sun ce suna ganin ba a ɗaukan su da muhimmanci a harkar aiki.
"Wasu abubuwa da suka jiɓanci dokoki da na al'ada na korar mata daga harkar ƙwadago a Iran", in ji Nadereh Chamlou, wata tsohuwar babbar mai bayar da shawara a Bankin Duniya.
Chamlou ta ce abubuwa kamar rashin dokokin da suka kamata da wasu tanade-tanden dokoki da suka shata iyaka, da rashin daidaiton albashi da kuma rashin samun damar riƙe manyan muƙamai na taimakawa wajen hana mata shiga ayyuka da dama a Iran.
A doka ne… da kuma al'ada
Maza na sane da cewa doka ta ba su damar hana matansu yin aiki, kuma wasu daga cikinsu na amfani da damar.
Wani da ya mallaki kamfani a Iran, Saeed ya shaida wa BBC cewa ya taɓa "samun wani miji da ya shiga ofishinsa a fusace, ɗauke da wani mulmulelen ƙarfe yana cewa 'wa ya ba ka izinin ɗaukar matata aiki?' da ƙarfi".
Ya ce a yanzu sai ya tabbatar ya samu rubutaccen izini daga miji kafin ya bai wa duk wata matar aure aiki.
Razieh, wani ma'aikaci a wani kamfani mai zaman kansa, ya ce zai iya tuna wani abu makamancin haka da ya faru a kamfaninsu, lokacin da wani miji ya shiga a fusace yana tuhumar shugaban kamfanin cewa "ba na son matata tana aiki a nan'.
Razieh ya ce dole sai dai shugaban kamfanin ya shaida wa matar, wadda babbar akanta ce cewa "ta je gida ta lallashi mijinta ya amince, in ba haka nan ba sai dai ta ajiye aiki, kuma a ƙarshe sai dai ta ajiye aikin."

Asalin hoton, Getty Images
Nadereh Chamlou ta ce wannan doka na sanyawa wasu kamfanoni ba su son ɗaukar ƴanmata aiki, domin ba su son "su kashe kudi wajen bai wa ƴanmatan horo amma daga ƙarshe idan suka yi aure mazansu su hana su yin aiki."
Haka nan ma koda sun samu nasarar shawo kan mazajensu da iyalansu wajen barin su su shiga aikin, matan kan fuskanci tsangwama a ma'aikatu, waɗanda kuma doka ba ta hana ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin irin waɗannan dokoki ita ce doka ta 1105 ta aikin gwamnatin ƙasar, wadda ta bayyana miji a matsayin shugaban iyali kuma 'mai ciyarwa'.
Wannan ya sanya aka fi bai wa maza fifiko wajen ɗaukar aiki fiye da mata, waɗanda ba a biyan su albashin da ya kai na maza, koda an ɗauke su aikin.
Raz, wadda ta zarta shekara 20 da kaɗan, kuma ta sauya ayyuka da dama. Ta ce a duk wuraren da ta yi aiki, ayyukan da mata ke riƙe da su ne aka fi ɗauka a matsayin marasa muhimmanci.
Wata matar da ba ta son a bayyana sunata, ta ce ta bar aikinta ne bayan kwashe shekara 10 tana aikin, "saboda na san ba za a ƙara mata girma ba".
"Matuƙar akwai maza a ofis ɗin, to kuwa ba za a ƙara min girma ba koda na fi su cancanta. Zan ɓata lokacina ne kawai," in ji ta.
Kasancewar doka ba ta bayyana mata a matsayin waɗanda ke ciyarwa ba, ya sanya ba su da tabbas wajen samun alawus-alawus na aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Tattalin arziƙin Iran ya shiga mummunan hali sanadiyyar takunkumai da kuma badaƙala.
Wani rahoton Hukumar Lamuni ta Duniya ya nuna cewa haɓakar tattalin arziƙi na da dangantaka da gudumawar mata a harkar ƙwadago, inda rahoton ya yi hasashen cewa idan har Iran za ta ƙara yawan matan da ke shiga harkar ƙadago daidai da yawan maza, tattalin arziƙinta na cikin gida zai samu bunƙasa da kimanin kashi 40 cikin ɗari.
Duk da dai Nadereh Chamlou na ganin cewa "babu ƙwaƙƙwarar aniyar" ganin an kawo wannan sauyi a halin yanzu.
Sai dai ta ce ta yi amannar cewa matan Iran za su iya ɗaukar mataki da kansu ta hanyar kafa ƙananan sana'o'i nasu na kansu, wanda hakan zai ƙara faɗaɗa rawar da suke takawa a ɓangaren ƙadago.











