Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lokuta takwas da shugaba Tinubu ya ciyo bashi a shekaru biyu na mulkinsa
Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da buƙatar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu ta neman majalisar dokokin ƙasar su sahhale masa ciyo bashin dala biliyan 21.5 daga ƙasashen waje da kuma lamunin naira biliyan 758 daga cikin gida.
A wasiƙar da aka karanta a zauren majalisa dattawa, shugaba Tinubu ya ce za a yi amfani da bashin ne domin samar da manyan ayyuka da suka jiɓanci lafiya da ilimi da samar da ruwan sha da kuma biyan basukan da ƴan fansho ke bi.
Tuni dai aka miƙa buƙatar ga kwamitin majalisar dattawa da ke lura da harkokin basukan gida da na waje domin tantancewa kuma ana sa ran kwamitin zai kammala aikinsa cikin makonni biyu.
BBC ta yi nazarcin shafukan Bankin Duniya da jaridu tare da sauraron tattaunawar da Sanata Ali Ndume ya yi da gidan talbijin na Arise TV domin zaƙulo lokutan da shugaba Tinubu ya ciyo bashi a shekarun mulkinsa biyu, kamar haka:
1) Yuni 2023
A watan Yunin shekarar 2023 wato wata ɗaya bayan kama aikinsa, shugaba Bola Tinubu ya karɓi bashin dala miliyan 500 da manufar inganta shirin mata da aka yi wa take da MPWPS.
2) Yuni 23, 2023
A ranar 23 ga watan na Yuni na shekarar ta 2023 dai, shugaban ya kuma ciyo bashi dala miliyan 800 da manufar rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.
3) Satumba, 2023
A ranar 23 ga watan Satumban shekarar 2023, watanni huɗu bayan kama aiki, gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta sake cin bashi dala miliyan 700 da manufar tafiyar da shirin inganta rayuwar ƴaƴa mata da matasa a harkokin ilimi.
4) Disamba. 2023
Bayan wata ɗaya da bashin watan Satumba a shekarar ta 2023, gwamnatin ta ƙara ciyo bashin dala miliyan 750 a ranar 23 ga watan Disamba domin haɓaka shirin samar da makamashi marar gurɓata muhalli.
5) Yuni, 2024
Bashi na farko da gwamnatin Tinubu ta ciyo a shekarar 2024 shi ne na dala miliyan biliyan ɗaya da rabi wanda gwamnatin ta ce ta ciyo da manufar tallafa wa shirin gwamnati na yin kwaskwarima da daidata tsare-tsaren tattalin arziƙin ƙasar da sauye-sauye.
6) Yuni 24, 2024
A ranar 24 ga watan Yunin dai an kuma ranto dala miliyan 750 da manufar inganta tsarin tattalin arziƙi musamman ta fuskantar tallafa wa ƴan ƙasa matalauta da waɗanda ke fuskantar barazanar talaucewa.
7) Satumba 26, 2024
A ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2024 ne Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya jerin basuka guda uku daban-daban da suka kai tsabar kuɗi har dala biliyan 1.57.
- Dala miliyan 570 domin inganta harkokin lafiya da inganta madatsun ruwa da noman rani a faɗin ƙasar.
- Dala miliyan 500 domin haɓaka harkokin inganta damarmaki ga ma'aikata da daidaito a aikin gwamnati.
- Dala miliyan 500 domin inganta harkar noma da tallata abin da aka noma a cikin ƙasa.
Da zarar kwamitin majalisar dattawan na Najeriya ya kammala aikinsa nan da makonni biyu wajen tantance bashi kuma majalisar ta sahhale wa shugaban ya ciyo bashin na dala biliyan 21.5 da lamunin naira biliyan 758 daga cikin gida to yawan kuɗin da ake bin Najeriya zai zama tasamma tiriliyan 200.
Sai dai kuma gwamnati ta ce bashin da take shirin karɓa ba wai a lokaci guda ne za a karɓe shi ba.
"Bashin na ɗaya daga cikin wani yanki na tsarin karɓar bashi daga ƙasashen waje na Najeriya na 2024-2026, wanda ke nufin a tsawon shekaru biyu za a ci bashi domin gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya da na sauran gwamnatoci."