Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko sanya dokar ta-ɓaci a Rivers zai warware rikicin siyasar jihar?
Yanzu haka dai dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ta Najeriya ta tabbata, bayan da a ranar Alhamis majalisar dokokin tarayyar ƙasar ta amince da matakin shugaban ƙasar Bola Tinubu na ƙaƙaba dokar.
Hakan na zuwa ne duk kuwa da irin sukar da matakin ya sha daga ɓangarori da dama, kamar daga ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar, da ɓangaren adawa da kuma na ƴan ƙwadago.
Duk da cewa rikicin siyasa tsakanin tsoho da kuma gwamna mai ci a jihohi ba sabon abu ba ne a Najeriya, amma na jihar Rivers na cikin waɗanda suka fi ƙazancewa.
Lamari ya tsayar da jihar cik, bayan da aka gaza samun matsaya tsakanin gwamna Siminalayi Fubara da mafi yawan ƴanmajalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.
Duk matakan da aka bi na ganin an warware rikicin - kamar sanya bakin shugaban ƙasa, da tsoma bakin masu ruwa da tsaki da kuma hukuncin kotun ƙoli - abin ya ci tura.
Ko dokar ta-ɓaci za ta warware matsalar da shugaban ƙasa da kotu da kuma masu ruwa da tsaki suka gaza warwarewa?
BBC ta tuntuɓi Farfesa Abubakar Kari na Jami'ar Abuja da Farfesa Tukur Abdulƙadir na Jami'ar Jihar Kaduna - masana a harkar siyasa a Najeriya.
'Mace ce mai ciki'
Farfesa Kari ya bayyana cewa ba lallai ba ne dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana a jihar Rivers ta kawo masalaha game da rikicin siyasar jihar.
"Abin da ya sa ake shakku kan ko wannan mataki zai kawo maslaha shi ne ganin cewa duk da rawar da ministan Abuja (Nyesom Wike) ke takawa a rigimar, wannan dokar ba ta shafe shi ba," in ji Kari.
"In dai har ana son dokar ta yi tasiri to dole ne sai an taka masa birki.
"Ko dai shugaban ƙasa ya ja masa kunne kan ya tsame hannunsa daga rikicin siyasar ko kuma dai shugaban ya nemi hanyar da zai taka masa burki".
Nyesom Wike, wanda ya yi gwaman jihar Rivers, daga shekara 2015 zuwa 2023, ana yi masa kallon 'kanwa uwar gami' a rikicin siyasar, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Hasali ma, ƴanmajalisar dokokin jihar 24 ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule, waɗanda ba su ga-maciji da gwamna Siminalayi Fubara, suna mubaya'a ne ga tsohon gwamna Nyesom Wike, wanda a yanzu shi ne ministan Abuja, babban birnin Najeriya.
'Takobi ne mai kaifi biyu'
Farfesa Tukur Abdulkadir kuwa cewa ya yi "wannan abu na iya kawo hanyar sulhu ko kuma ya ƙara dagula lamarin".
Ya bayyana cewa za a samu sulhu ne "idan ɓangaren gwamnan jihar da majalisar dokokin jihar da kuma ɓangaren ministan Abuja, wanda ke mara musu baya" suka jefar da duk wani son rai domin amfanin jihar.
"In ba haka ba, idan ba su hankali ba za a yi abin da ake cewa a fasa kowa ya rasa," in ji Farfesa Abdulkadir.
Ya ƙara da cewa in dai har suka sanya siyasa kawai a gaba, "to zai yi wahala a kawo ƙarshen wannan lamarin."
Ko Tinubu zai iya taka wa Wike burki?
Dukkanin Farfesoshin biyu dai sun haɗu a kan cewa ministan Abuja, babban birnin Najeriya, Nyesom Wike na da hannu dumu-dumu a cikin rikicin, kuma shawo kansa ya sassauto daga matsayarsa za ta iya warware taƙaddamar siyasar ta jihar Rivers.
Sai dai Farfesa Kari ya ce alamu sun nuna cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fi karkata ne a ɓangaren Wike: "Idan aka yi la'akari da jawabin Tinubu lokacin da ya ayyana dokar ta-ɓaci a Rivers, cike yake da bai wa gwamna Fubara rashin gaskiya...saboda haka ya zuwa yanzu tamkar Tinubu ya fi karkata ne a ɓangaren Nyesom Wike.
"Zuwa yanzu Tinubu baya da niyyar ja wa Wike burki," in ji Farfesa Kari.
Me ya sa rikicin ke da sarƙaƙiya?
Farfesa Abubakar Kari na ganin cewa ɗaya daga cikin abubuwan da ya sanya rikicin siyasar jihar Rivers ke da sarƙaƙiya shi ne batun ƙabilanci, kasancewar gwamna Sinimalayi Fubara shi ne gwamna na farko da ya fito daga ƙabilar Ijaw.
Ya ce shugabannin ƴan ƙabilar Ijaw "na ganin cewa abin da faru tamkar an wulaƙanta su ne ko an yi musu cin fuska ko kuma ana so ne a ƙwace muƙamin gwamna daga hannun ɗan ƙabilar".
Ijaw al'umma ce da ta yaɗu a jihohi da dama na yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur a Najeriya, inda suke a jihohin Delta da Bayelsa da kuma Rivers, kuma mutane ne waɗanda ke da ƙarfin faɗa a ji a yankin.
Sannan wani abu da yake ganin ya sanya rikicin siyasar ta jihar Rivers ke da sarƙaƙiya shi ne yadda yake da haɗarin taɓa tattalin arziƙin Najeriya, ksancewar duk wani rikici a yankin na Neja-Delta zai yi cikas ga fitar da ɗanyen man fetur, wanda shi ne babban abin da ƙasar ke sayarwa zuwa ƙasashen ƙetare.
Abin da dokar za ta magance
Wani abu da yi fito zahiri tun bayan ƙazancewar rikicin siyasar jihar shi ne yadda aka fara ganin alamomin ƙaruwar tashin hankali a jihar.
A ranar 18 ga watan Maris, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun fasa babban bututun man fetur na Trans Niger Pipeline a yankin Kpor da Bodo na jihar, wanda ke ɗaukar ɗanyen man fetur daga filayen haƙar mai zuwa tashar fitar da ɗanyen man fetur ɗin ta Bonny.
Lamarin da ya haifar da tashin gagarumar gobara a yankin.
Lamarin ya faru ne kwana ɗaya bayan majalisar dokokin jihar ta ƙaddamar da matakin farko na tsige gwamnan jihar ta hanyar aika masa da takardar tuhuma wadda ta samu sa hannun mafiya rinjaye na ƴanmajalisar dokokin
Farfesa Tukur Abduklkadir na da ra'ayin cewa abu ɗaya kawai da dokar za ta iya magancewa shi ne wannan alamu na taɓarbarewar tsaro a jihar.
"Ƙila zai iya daƙile mummunan tashin hankali wanda ba llai ne ya tsaya a jihar kaɗai ba, zai iya shafar ko'ina."