Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Taliban ke mayar da mata gidajen miji 'ƙarfi da yaji'
- Marubuci, Mamoon Durrani
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC sashen Afghanistan
- Lokacin karatu: Minti 5
Shekara uku tun bayan da Taliban ta karɓi mulki a Afghanistan, sauye-sauyen da ƙungiyar ke kawowa a ɓangaren shari'a na ƙasar na shafar rayukan mutane da dama.
Taliban ta ce a yanzu haka alƙalanta ba kawai suna ƙoƙarin tabbatar da dokoki ba ne, har ma da zaƙulo wasu shari'o'in da aka yi a baya domin duba ingancinsu.
A wani gagarumin mataki da ta ɗauka, gwamnati na bai wa duk mai son ɗaukaka ƙara damar yin hakan a kyauta.
Wannan ya sanya bisa dogaro da tsarin tsauraran dokokin shari'a da ake amfani da su a yanzu, an soke dubun dubatar shari'o'i da aka yi a shekarun baya.
Kuma wannan lamari ya fi shafar mata.
Yanzu haka an fara soke wasu daga cikin sake-saken aure da kotu ta zartar a gwamnatin baya, lamarin da ke tursasa wa wasu mata komawa gidajen auren da suka guda a baya.
Haka nan kuma a yanzu an haramta wa alƙalai mata shiga harkar ta shari'a: 'Mata ba su cancanci yanke hukunci na shari'a ba domin kuwa a tsarinmu na shari'a, alƙalanci na buƙatar mutane masu kaifin ƙwaƙwalwa.
An sake kira na kotu
Kwana 10 bayan Taliban ta sake karɓe mulki, Bibi Nazdana, mai shekara 20 a duniya na taya mahaifiyarta aikin gida, sai ga mahaifinta ya dawo.
Lokacin da jikinta ya fara ba ta wani abu na faruwa, sai ta matsa kusa domin jiyo abin da mahaifinta ke faɗa wa mahaifiyarta.
Nazdana ta ce: "gabana ya faɗi ras, lokacin da na ji an ambaci sunana, sai hawaye suka fara kwarara daga idona."
Kotun Taliban da ke ƙauyensu a lardin Uruzgan za ta sake sauraron shari'arta. An buƙace ta ta sake bayyana a gaban kotu domin kare mutuwar aurenta da tsohon mijinta, wanda ba ta taɓa son shi a zuciyarta ba.
A lokacin da Nazdana ke da shekara bakwai a duniya, mahaifinta ya amince zai aurar da ita da zarar ta tasa, domin warware wata taƙaddama tsakanin iyali.
Ana yin irin wannan auren ne domin sasanta iyalai biyu waɗanda ba su ga-maciji da juna.
A lokacin da Nazdana ta cika shekara 15 a duniya, Hekmatullah ya zo gidansu domin tafiya da matarsa gida.
Sai Nazdana ta shigar da ƙara nan take, inda ta yi nasara.
Nazadana ta ce: "Na yi ta jaddada wa kotu cewa ba na son auren shi."
"Bayan kwashe shekara biyu ana tafka shari'a, daga ƙarshe na yi nasara. Kotu ta taya ni murna ta ce min yanzu 'kina da ƴancin auren wanda ranki ke so.'"
A kan haka har sai da aka shirya ƙwarya-ƙwaryar walima a ƙauyen nata, inda aka raba wa mutane abinci a masallaci.
Sai dai bayan shekara ɗaya, Taliban ta ƙace mulkin ƙasar, inda ta ƙaƙaba tsattsauran tsarin shari'a a faɗin ƙasar.
Tsohon mijin nata, wanda daga baya ya zama ɗan ƙungiyar Taliban ya buƙaci kotu ta soke hukuncin da kotu ta zartar a ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe.
A wannan karon ba a abai wa Nazdana damar jin bahasinta ba, bisa tsarin shari'a na Taliban.
"Kotu ta ce min kada na sake zuwa harabar kotun kasancewar hakan ya saɓa wa shari'a. Sai suka ce ɗan'uwana ne zai wakilce ni," in ji Nazdana.
"Sun ce mana idan muka saɓa umarnin, za su miƙa Nazdana ga Hekmatulla da ƙarfi da yaji," in ji Shams, ɗan'uwan Nazdana mai shekara 28.
Duk da roƙon da Shams ya yi wa kotu, tare da cewa ƴar'uwar tsa za ta shiga cikin mummunan haɗari, alƙalin ya soke hukuncin da kotu ta yanke a baya, tare da yanke hukuncin cewa Nazadana ta koma gidan tsohon mijinta, Hekmatullah, nan take.
Nazdana ta ɗaukaka ƙara domin samun lokacin da zai ishe ta ta tsere daga ƙasar. Daga nan ne ita da ɗan'uwanta suka fice zuwa ƙasa mai maƙwaftaka.
Alƙalin kotun da ke lardin Uruzgan ya ce ba zai yi mana bayani ba, amma mun je kotun ƙoli ta Taliban da birnin Kabul domin neman bayani.
Jami'in hulɗa da jama'a na kotun, Abdulwahid Haqani ya ce: "Alƙalanmu sun yi nazari kan hukuncin inda aka gano cewa Hekmatullah ne ke da gaskiya".
Mun yi yunƙurin jin ta bakin Hekmatullah, amma ba mu samu damar yin magana da shi ba.
Shari'ar Nazdana, ɗaya ne kacal daga cikin shari'o'i 355,000 da kotunan Taliban suka ce sun sake yin nazari a kai tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace mulki a watan Agustan 2021.
Mata a harkar shari'a
Lokacin da Taliban ta koma kan mulki, sun yi alƙawarin kawar da rashawa da kuma tabbatar da adalci.
Sun sauke dukkanin alƙalan ƙasar, sannan suka ayyana cewa mata ba za su kasance cikin alƙalai.
"Mata ba za su iya yin shari'a a tsarin shari'armu ba, aikin shari'a na buƙatar mutane masu kaifin tunanin," in ji Abdulrahim Rashid, daraktan harkokin ƙasashen waje da yaɗa labaru a Kotun ƙolin ƙasar.
Tsohuwar mai shari'a a kotun ƙolin Afghanistan, Fawzia Amini na daga cikin alƙalan da Taliban ta sauke daga muƙaminta.
Ya ce ya kamata shari'a ta bai wa mutane kamar Bibi Nazdana kariya.
Shari'a
A Kotun ƙolin Taliban, an nuna mana wani ɗaki maƙare da tarin takardu na shari'o'i da ake gudanarwa.
An faɗa mana cewa mafi yawan shari'o'in sun faru ne a lokacin gwamnatin da ta gabata amma yanzu ana sake duba su.
Zama shiru
Tun bayan tserewarta zuwa wata ƙasa mai maƙwaftaka, Nazdana na zama ne a ƙasan wata bishiya a gefen titi.
Tana zaune ɗauke da wasu ƙunshin takardu, waɗanda su ne su ne hujjojin ta na cewa aurenta ya mutu.
"Na nemi taimako daga wurare daban-daban, ciki har da wurin ajalisar Dinkin Duniya, amma babu wanda ya saurare ni. Ina taimakon yake? Ban cancanci zama mace mai ƴanci ba ne?