Ƙasashe biyar da ke taimaka wa mutane gano asalinsu

Italiya na fatan 'yan yawon buɗe idanu masu ɗauke da asalin Italiya za su koma ƙasar domin gano asalin danginsu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Italiya na fatan 'yan yawon buɗe idanu masu ɗauke da asalin Italiya za su koma ƙasar domin gano asalin danginsu.
Lokacin karatu: Minti 6

Ana kallon bulaguron neman asali a matsayin wata hanya mai ɗorewa da za ta maye gurbin yawan shaƙatawa.

Tarayyar Turai musamman, wadda ake ganin ta fi ko'ina yawon buɗe ido a duniya, ta yi kira ga ƙasashe mambobinta su ƙarfafa yawon buɗe idon neman asali.

Kamfanonin shirya tafiye-tafiye da suka ƙware a shirya bulaguron neman asali, sun ƙara shahara suma.

A 2021, amfanin shirya tafiye-tafiye na Kensington Tours ta haɗa gwiwa da Ancestry.com wajen shirya bulaguron neman asali zuwa wasu wurare a Italiya da Jamus da Ghana tare da haɗin gwiwa da ƙwararrun likitocin mata domin taimakawa wajen samar da cikakken bayanin wuraren tarihi da za su iya taimaka wa mutane gano asalinsu.

"Waɗannan tafiye-tafiye sun fara samun shahara a 2022, bayan ƙarewar annobar covid, da janye dokar taƙaita tafiye-tafiye a faɗin duniya,'' in ji Dakta Debra Loew na cibiyar shirya tafiye-tafiye na Kensington Tours.

"Hakan kuma ya faru ne bayan da aka samu ƙaruwar tafiye-tafiyen iyalai domin neman asali ko tsatsonsu bayan shafe watanni a wasu wuraren kuma shekaru ba tare da yin tafiye-tafiye ba.''

A yayin da mafi yawan ƙasashen Turai suka sheafe gomman shekaru suna ƙarfafa bulaguron neman asali, wasu na ƙoƙarin samar da wasu keɓantattun hanyoyi na haɗa masu ziyara da asalinsu.

Ga wasu wurare da ke taimaka wa matafiya wajen gano asalinsu.

Italiya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kusan mutum miliyan 80 ne a faɗin duniya suka iya gano asalinsu zuwa Italiya, kuma ma'aikatar yawon buɗe idanu ta ƙasar na ƙarfafa wa 'yan asalin ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje su koma gida, tare da ayyana 2024 a matsayin "Shekarar gano asalin 'yan Italiya a Duniya"

Sun ƙaddamar da wani shafin intanet, domin sauƙaka wa masu ziyara samun bayanai game da yankunan ƙasar 20, tare da dabarun yadda za su gano asalin tarihin danginsu.

Masu shirya tafiye-tafiye sun samu gagarumar nasara sakamakon wannan yunƙuri.

''Kamfanin shirya tafiye-tafiye na Heritage Travel ya kasance kan gaba a wannan tsari, inda ya samar da fiye da kashi 95 na ƙudirinmu,'' in ji Marino Cardelli, wanda ya samar da kamfanin shirya tafiye-tafiye na BellaVita a 2018.

Ya kuma ce gano asalin na na da wahalar gaske. Da yawan Italiyawa sun yi ƙaura a farkon shekarun 1900, kuma wataƙila an ruguza gidajensu a lokacin yaƙunan duniya.

Italiya na da cikakken tsarin adana bayanai tun shekarun 1400, da ke samar da cikakkun bayanai - wanda kuma a wasu lokuta kan taimaka wajen gano inda 'yan'uwansu ke zaune.

Ghana

Majami'ar Elmina da sauran cibiyoyin cinikin bayi na da matuƙar muhimmanci ga masu neman asalinsu a Afirka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Majami'ar Elmina da sauran cibiyoyin cinikin bayi na da matuƙar muhimmanci ga masu neman asalinsu a Afirka.

Ƙasar da ke yankin Yammacin Afirka - wadda ta taɓa zama cibiyar cinikayyar bayi - ta jima tana karɓa 'ayn Afirka mazauna ƙetare da ke neman asalinsu, ciki har da shekarar 2019 da aka yi wa laƙabi da Shekarar Komawa da kuma shirin neman asalin mutane na ''The Joseph Project'' a 2007.

Ƙaruwa gwajin ƙwayoyin halitta na DNA na ƙara taimakawa wajen gano asalin 'yan Afirka da ke son gano asalinsu ko ƙabilarsu da kuma inda kakanninsu suka taso.

Sakamakon tarihinta na muhimmiyar tasha a lokacin cinikin bayi, Ghana ta zama muhimmiyar sansanin bulaguro don neman asali a Afirka

Tsakanin ƙarni na 16 zuwa na 18, an yi safarar dubbban a wurare kamar su majami'ar Elmina, wuri na ƙarshe da ake tsare bayin a nahiyar kafin a loda su a jirgin ruwa zuwa Arewaci da Kudancin Amurka.

A yau kamfanonin shirya tafiye-tafiyen neman asali irin su Kensington na shirya tafiye-tafiye zuwa irin waɗannan wuraren tarihi, tare da shirya ganawa da ƙwararru domin masu ziyara su samu bayanai kan wasu ƙabilu ko yaruka da asalinsu, tare da samun cikakkun bayani kan ƙaurarsu da al'adu da ɗabi'unsu.

Scotland

Ƙasar Scotland ta fuskanci ƙaruwar masu ziyarar neman asalinsu a shekarun baya-bayan nan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙasar Scotland ta fuskanci ƙaruwar masu ziyarar neman asalinsu a shekarun baya-bayan nan

Fiye da mutum miliyan 40 da ke zaune a sassa daban-daban na duniya, kan yi iƙirarin cewa su 'yan asalin Scotland ne, a cewar shafin Visit Scotland, kuma sakamakon haka miliyoyin matafiya kan koma ƙasar a kowace shekara domin haɗuwa da asalin danginsu.

Kashi 70% na masu ziyara da suka fito daga nesa (waɗanda suka fito daga Canada da Amurka da Australia da yankin Asiya) sun bayyana cewa tarihi da al'adu shi ne dalilin ziyararsu - kuma da yawa waɗanda suka zo suna ba da rahoton jin daɗin dawowa gida".

Ƙasar Scotland ta fuskanci ƙaruwar msu ziyarar neman asalinsu.

Ga matafiyan da suka san sunayen wasu daga cikin kakannin kakanninsu, gwamnatin ƙasar ta samar da wani rumbun bayanai na yadda za a yi lalubo suna da shekaru.

Wasu - waɗanda ke da wani sunan Scotland na daban, za su iya neman sunan ƙabilarsu, ko sana'ar da ƙabilarsu ta shahara, an kammala tsara cikakken sunayen daga A zuwa Z na kowane ƙabila.

Akwai fiye da wurare 30 da suka shafe shekara 5,000 da ke taimaka wa wajen gano asali da ƙabilar mutane a Scotland.

Indiya

Indiya na ganin ziyarar masu neman asali a matsayin muhimmiyar ƙaruwa a fannin yawon buɗe idanu a ƙasar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Indiya na ganin ziyarar masu neman asali a matsayin muhimmiyar ƙaruwa a fannin yawon buɗe idanu a ƙasar

Kasancewar ta ƙasar da mutanenta suka fi yawa a ƙasashen waje, inda aka ƙiyasta haifar 'yan asalin ƙasar miliyan 18 a ƙasashen ƙetare, Indiya na da kyakkyawan dalilin janyo hankalin waɗancan mutane da sauran waɗanda ke da asalin Indiya don ziyarartar ƙasarsu ta asali.

A baya-bayan nan gwamnati ta ƙaddamar da shirin jigilar jrigin ƙasa kyauta na Pravasi Bharatiya, wani jirgin ƙasa da ke taimaka wa 'yan asalin Indiya mazauna ƙetare gano asalinsu.

Duk da cewa jirgin zai iya ɗaukar fasinjoji 156, tafiyar mako uku da zai zagaya cikin ƙasar, zai ziyarci muhimman wuraren yawon buɗe idanu da cibiyoyin addinai a faɗin ƙasar, , kuma gwamnati ce za ta biya duka kuɗaɗen jigilar.

Akwai yiwuwar ci gaba da zuba kuɗaɗe a wannan harka, yayain da Indiya ke mayar da hankali wajen ƙarfafa gwiwar ziyara neman asali.

Ƙasar ta samu ci gaban tattalin arziki bayan covid, inda aka samu ƙaruwar kashi 46 na masu yawon buɗe idanu, kamar yadda ƙungiyar Trevolution ta bayyana.

Bayan haka, an samu tururuwar bulaguron Amurka 'yan asalin Indiya zuwa ƙasar domin ziyartar abokai da 'yan'uwansu , suna masu cewa bulaguron neman asali zai ci gaba da haɓaka fannin yawon buɗe idanu a ƙasar.

Macon da Georgia a baya wasu ƙauyuka 60 ne suka haɗu suka kafa ƙasar Muscogee (Creek)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Macon da Georgia a baya wasu ƙauyuka 60 ne suka haɗu suka kafa ƙasar Muscogee (Creek)

Amurka

Kodayake Amurka da Kanada duk sun fuskanci yawan ƙaura zuwa Turai a lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniyya, wannan ƙaura ta sa 'yan ƙasashen da dama sun watsu a sassan duniya.

Sau da yawa an riƙa tilasta wa mazauna ƙasar yin nisa daga yankunansu, ’yan asalin ƙasar ba su da wani zaɓi illa su zauna a wani wuri.

A yau, wasu ofisoshin yawon shaƙatawa sun yi ƙoƙarin maraba da iyalan da suka dawo, tare da yin aiki tare da shugabannin 'yan asalin yankin don adanawa da kuma raba muhimmin tarihi tare da zuriyar da aka raba da matsugunai da sauran baƙi zuwa yankin.

Misali ɗaya shi ne yankin da a yanzu ake kira Macon da Georgia, wanda aaya wasu ƙauyukan 60 ne suka haɗu tare da kafa ƙasar Muscogee (Creek).

'Yan asalin ƙasar Muscogee sun riƙa komawa ƙasarsu, ba wai a matsayin masu ziyara ba, har ma a matsayin masu taimaka wa wajen gina abubuwan ci gaba a garin Macon.

Ma'aikatar kula da gandun daji ta ƙasar na ɗaukar ƴan ƙasar Muscogee (Creek) aiki akai-akai, kuma ana ba da fifiko ga membobin ƙasar don samun matsayi.

A cikin Satumba 2024, an buɗe alamun tituna na farko waɗanda ke ɗauke da sunayen Ingilishi da Creek, tare da ƙarin 100 da za a girke a gundumar cikin gari a cikin watanni masu zuwa.