Nau'ukan abinci 8 da ke jawo tusa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, BBC Food
- Lokacin karatu: Minti 5
Tusa abu ne da aka saba yi - mutum yakan yi tusa sau 5 zuwa 15 a rana. A zahiri ma yin tusa sosai a wasu ranakun na iya zama alamu na lafiya.
Dalilin haka shi ne abincin da ke sa tusa akasari masu ƙara lafiyar zuciyar ne, da masu sa kuzari da ke ɗauke da wasu sinadarai waɗanda jikinka ba ya iya narkawa amma ƙwayoyin bacteria da ke cikinka za su iya.
A don haka, wane nau'ukan abinci ne ke sa ka tusa, waɗanne ke sa tusar wari, kuma a yaushe ya kamata ka ziyarci likita?
Abinci mai kitse
Abinci mai kitse na sa abinci ya narke a hankali, wanda zai sa su daɗe a cikinka, su yi tsami su kuma yi wari.
Nama mai kitse na da sarƙaƙiya saboda yana ɗauke da sinadarin methionine wanda kuma ke ɗauke da sinadarin sulphur.
Ƙwayoyin bacteria da ke cikinka na narkar da sulphur ya zama hydrogen sulphide - wanda warinsa ke kama da na kwai da ya ruɓe - kuma yana ƙara warin tusan da wasu nau'ukan abinci ke janyo wa.
Wake

Asalin hoton, Getty Images
Wake da danginsa kamar su lentils suna ɗauke da sinadarin raffinose, wani nau'in sukari da bama iya narkarwa yadda ya kamata.
Waɗannan nau'ukan na sukari na tafiya zuwa hanji, wanda cikinka ke amfani da su domin ba ka kuzari, wanda zai kai ga samar da hydrogen, da methane da kuma sinadarin sulphur mai wari.
Ƙwai
Kwai ba ya sa wasu daga cikinmu tusa kamar yadda ake yawan faɗi.
Sai dai su na ɗauke da sinadarin methionine da ke cike da sulphur. A don haka idan ba ka son ka yi tusa mai wari, kar ka ci ƙwai tare da abinci mai sa tusa kamar wake ko nama mai kitse.
Idan ƙwai na sa maka kumburin ciki da kuma tusa, wataƙila jikinka ba ya so ne.
Albasa

Asalin hoton, Getty Images
Albasa da tafarnuwa da dangoginsu kamar su artichoke da leeks na ɗauke da sinadarin Fructans- sinadarin da zai iya sa tusa da kumburin ciki.
Madara da abin da ake samu daga cikinsa
Madara daga shanu ko akuya na ɗauke da lactose, wani nau'in sukari da ke sa iska taruwa a ciki.
Bugu da ƙari, kimanin kashi 65 cikin 100 na yawan matasan duniya, jikinsu ba ya son sinadarin lactose, kuma shan madara ko abubuwan da aka samar daga cikin madara zai sa cikinsu ya kumbura ya kuma sa su tusa.

Asalin hoton, Getty Images
Alkama da datsa
Ana samun sinadaran fructans mai sa tusa a cikin hatsi kamar alkama da danginsa kamar su Oats, don haka burodi ko taliya ko datsa na iya sa tusa.
Bugu da ƙari wasu daga cikinsu na ɗauke da sinadarin gluten.
Idan jikinka ba ya son gluten, cikin ka zai iya kumubura ka yi ta tusa idan ka ci abinci mai ɗauke da sinadarin.
Broccoli da cauliflower da Kabeji
Ganyayyyaki da suka ƙunshi kabeji da broccoli da cauliflower da kale, da kuma wasu koren ganyayyaki na ɗauke da harza mai yawa, kuma ya kan ɗan yi wa jikin mu yawa ya kasa narkar da shi.
Sai dai ƙwayoyin bacteria ɗin da ke cikinmu na son amfani da shi wurin bayar da kuzari, hakan kuma na kai wa ga sakin tusa.
Akasarin waɗannan ganyayyayki na kuma ɗauke da sinadarin sulphur, kuma dai kun san irin warin da ya ke janyo wa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴaƴan itatuwa
Ƴayan itatuwa kamar su mangwaro da tufa da piya na da sinadarin fructose mai yawa. Kuma wasu kayan marmarin kamar tufa da piya na ɗauke da harza.
Mutane da dama ba sa iya narkar da sinadadrin Fructose sosai, kuma cin ƴaƴan itatauwan nan na iya sa su tusa saboda ba sa iya narkar da sukarin yadda ya kamata.
Za ka iya daina tusa?
Ƴaƴan itatuwa da ganyayyayaki da wake na iya sa mutum tusa, sai dai cin wasu daga cikinsu a kowace rana ya fi muhimmanci fiye da kokarin kaucewa yin tusa.
Idan a baya ba ka cin abinci mai harza, ƙara shi sosai cikin abincinka zai iya sa ka shiga yanayi na rashin jin dadi.
Kamata ya yi ka sanya su cikin abincinka kaɗan-kaɗan.

Asalin hoton, Getty Images
Shan ruwa sosai yana hana yiwuwar samun kumburin ciki wanda ke janyo yin tusa sosai. Idan bahaya ya daɗe a cikinka, zai cigaba da ruɓewa, wanda zai samar da tusa mai wari sosai.
Ka yi ƙokarin shan ruwa a duk lokacin da ka ci abinci ka kuma yi ƙokarin ci gaba da shan ruwa har dare.
Hukumar lafiya ta Birtaniya ta bayar da shawarar shan shayin na'a-na'a domin rage yin tusa da kumburin ciki.
Lemukan kwalba ma na ɗauke da iska, kuma idan ka sha su dayawa za su sa ka yin gyatsa da tusa fiye da yadda za kayi idan ba ka sha ba.
Haka ma idan ka ci chingam ko ka sha miya da cokali. Idan iska ya shiga cikinka, dole ne ya samu wurin da zai je.
Shin ya kamata ka damu?
A lokuta da dama, yin tusa ba abin damuwa ba ne. Yawancin dalilan yin tusa ba sa buƙatar bincike ko magani.
Sai dai a wasu lokutan, yin tusa sosai na iya zama alamu na wani ciwon, don haka idan ka damu da yawan tusan, ka ziyarci likita.
Tusa mai wari na kuma iya zama saboda wasu magunguna da kake sha.











