Yadda aka sace munduwar hannun Fir'auna a gidan tarihi na Masar

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Atiya Nabil
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic - Cairo
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani abin tarihi da ya ɓace a gidan adana tarihi na Tahrir Square da ke Masar ya ja hankali matuƙa, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida na Masar ta bayyana kwanaki kaɗan bayan sanar da sace kayan tarihin.
Ma'aikatar ta ce an sace munduwar ce ta hanyar haɗa baki da wasu gungun mutane suka yi.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, wata ma'aikaciya ce ta sace munduwar hannun a ranar 9 ga watan Satumba, sai ta nemi wata mai sayar da azurfa mai zuna Sayeda Zeinab a Cairo, wadda ta sayar da ita ga wani mai sayar da zinare a lardin Sagha a kan fam 180,000 na Masar kimanin dala 3,720. Shi kuma sai ya sayar da ita a kan fam 194,000 na Masar kimanin dalar Amurka 4,000, sannan aka narka tare da wasu azurfofin, aka yi sababbi.

Asalin hoton, Social media
"Ta ɓace har abada"
Ma'aikatar cikin gida ta Masar ta ce babu yadda za a iya gano munduwar mai kimanin shekara 3,000 a duniya. Yanzu dai babu labarinta mai daɗaɗɗen tarihi, ta ɓace har abada saboda an riga an narka ta, kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sai dai matsalar ta buɗe sabon babi, inda ake tambayoyi game da hanyoyin tsaron gidan adana tarihi a ƙasar.
Dr. Magdy Shaker, babban masanin kayayyakin adana tarihi a ma'aikatar harkokin buɗe ido ya ce Masar na da aƙalla gidajen adana kayayyakin tarihi guda 75, amma ayyyukansu ya bambanta, inda suke alaƙa da ma'aikatu ciki har da mai alaƙa da ma'aikatar al'adu da mai alaƙa da ma'aikatar noma da jirgin ƙasa.
Shaker ya ce akwai buƙatar a tattara bayanan dukkan gidajen adana tarihin a ƙarƙashin ma'aikata guda ɗaya.
Masanin ya kuma ce akwai buƙatar a riƙa amfani da wasu lambobi na sirri a kan kowane kayan tarihi, wanda zai ƙunshi tarihi da sauran bayanan kowane daga ciki tun daga gano shi har zuwa adana shi.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a riƙa tattarawa tare da adana dukkan gidajen adana tarihin da aka kai kayayyakin.
Babban mai kula da kayayyakin adana tarihi a ma'aikatar yawon buɗe ya ce akwai buƙatar a buɗe ɗakin adana bayanai na musamman da zai ƙunshi bayanan gidajen adana tarihi da bayanan su.

Asalin hoton, Social Media
Albashin ma'aikata
Da yake zantawa da BBC, shugaban sashen kula da kayan tarihi na ma'aikatar yawon buɗe ido ya ce akwai buƙatar a ƙara wa ma'aikatan gidajen adana tarihin albashi.
Ya ce shi kansa bayan tsawo lokaci yana aiki, albashinsa bai wuce fam 9,000 na Masar ba, kimanin dalar Amurka 185, wanda a cewarsa hakan yana hana ma'aikata sakat, wanda ya ce zai iya tursa su fara sata.
Sai dai ya ce ba ya nufin yana ba satar kayayyakin kariya ba ne.
Sai dai wannan maganar ta samu suka mai zafi daga wata masaniyar adana kayayyakin adana tarihi na Masar mai suna Dr Monica Hanna wadda ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, "zan so in fayyace wani abu mai muhimmanci a nan game da sace kayan adana tarihi a Masar. Ma'aikatan adana tarihi suna cikin ƙwararrun ma'aikata da na sani a Masar. Amma batun cewa ƙarancin albashi ne ya sa suke sace kayan tarihi cin fuska ne a gare mu baki ɗaya."

Asalin hoton, Getty Images
Ban-kwana da munduwar Sarki Amenemub
A ranar 16 ga watan Satumba, ma'aikatar yawon buɗe ta fitar da sanarwar tabbatar da ɓacewar munduwar daga gidan adana kayan tarihi da ke Tahrii, inda ta ce ƴansanda na bincike kan lamarin.
Ma'akatar ta ce dukkan hukumomi an ba su umarnin su ɗauki matakan da suka dace.
Ma'aikatar yawon buɗe ta fitar da sanarwa a kafofinta na sada zumunta, inda a ciki darakta-janar na gidan adana tarihin Tahrir yake cewa, "munduwar da ake magana ta zinare ta musamman ce wadda take ɗauke da ɗigon ƙwallaye na lapis lazuli, kuma tana cikin kayayyakin da Sarki Amenemeuti ya bari tun a zamanin 664 BC."











