Ana zargin sojojin haya na Rasha da aikata kisan gilla a Mali

Mutane biyu ƴan Mali a sansanin ƴan gudun hijira na M'berra a Mauritania yayin da rana ta yi ƙasa.
    • Marubuci, Thomas Naadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, M'berra
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gargaɗi: Wannan labarin ya ƙunshi bayanin azabtarwa da cin zarafi, waɗanda za su iya tayar da hankalin masu karatu.

Wani mai shago ya shaida wa BBC yadda sojojin hayar Rasha da ke yaƙi da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi a Mali suka aiwatar da kisan gillar da aka yi wa wasu mutane biyu a gabansa, sannan suka yi barazanar sare masa yatsu da ma kashe shi.

Wannan dai na ɗaya daga cikin shaidu iri-iri da BBC ta tattara da ke nuna irin dabarun da mayaƙan na Rasha suka yi amfani da su wajen kai wani mummunan farmaki na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasar da ke yammacin Afirka - dabarun da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka yi Allah wadai da su.

A shekara ta 2021 ne gwamnatin mulkin soji ta ƙwace mulki a ƙasar Mali, lamarin da ya tilastawa sojojin Faransa ficewa daga ƙasar bayan da suka zarge su da gazawa wajen daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya. Majalisar mulkin sojan ta karkata hankalin zuwa ƙasar Rasha, inda ta nemi taimakon sojojin hayar Wagner, waɗanda a wancan lokacin ke da alaƙa da fadar Kremlin.

Tuni dai Wagner ya fice daga ƙasar, kuma rundunar Africa Corps ta maye gurbinta inda ta karɓe ikon gudanar da ayyukanta, wanda ke ƙarƙashin ma'aikatar tsaron Rasha.

Wasu daga cikin sojojin haya na Wagner sun bayyana irin ta'asar da suka aikata a wata tasha ta musamman a dandalin sada zumunta na Telegram, har zuwa lokacin da aka kai ga rufe tashar a tsakiyar wannan shekarar, in ji wani rahoto da Majalisar Tarayyar Turai ta fitar a watan jiya.

Rahoton ya ƙara da cewa "sun riƙa musayar hotuna da bidiyo akai-akai da ke nuna kisan kai da fyaɗe da azabtarwa da cin mutuncin mutane da wulaƙanta gawarwakin waɗanda ake zargi da tayar da zaune tsaye da fararen hula", in ji rahoton.

A watan Yuni, jaridar Africa Report ta ce ta "kutsa kai" cikin wata tashar Telegram mai alaƙa da Wagner, inda ta gano bidiyo guda 322 da hotuna 647 na cin zarafi, da suka haɗa da waɗanda ke nuna kawuna da aka sassare da idanuwa da aka ƙwakule, da kuma rubuce-rubuce "masu nuna wariyar launin fata".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai shagon da muka zanta da shi ya riga ya tsere daga ƙasar Mali kuma yanzu haka yana zaune a sansanin ƴan gudun hijira da ke kan iyaka a ƙasar Mauritania. Mun sanya masa suna Ahmed, kuma mun canza sunayen duk waɗanda aka ambata a cikin wannan labarin saboda dalilai na tsaro.

Ya shaida wa BBC cewa matsalarsa ta fara ne a lokacin da mayaƙan Wagner suka isa wani babban kantin sayar da kayayyaki da ya ke aiki a tsakiyar garin Nampala a watan Agustan 2024.

Duk da kasancewarsu kwastomomi na yau da kullun, mayaƙan na Wagner sun so su tsare ubangidansa, kuma sun zarge shi da hada baki da mayaƙan masu iƙirarin jihadi da ke da karfi a yankin, in ji Ahmed.

Ya ƙara da cewa "Sun jefa ni cikin mota suka danne ni a ciki suka ɗaure min hannu."

"Wani sojan Wagner ya ɗauki wuƙa ya ɗora a yatsana, ya tambaye ni: 'Ina mai shagon?' Na ce masa yana (babban birnin) Bamako, amma ya amsa: 'ba amsar ba ke nan."

Ahmed ya ce mayaƙan Wagner, waɗanda suka yi amfani da tafinta, sun kai shi wani katafaren sansanin sojojin Mali, suka sanya shi a cikin wani garejin jiragen sama.

"Ni da wasu mutanen Wagner uku muna cikin garejin, sai suka cika tanki da ruwa, suka ce in cire tufafina. Sai suka tsoma kai na a cikin ruwan har sai da na kusa shaƙewa sai na faɗi, sannan suka ɗora ƙafafun su a kirjina na fara numfashi sama-sama.

"Sai suka sake tsoma kai na a cikin ruwan, suka tambaye ni a karo na biyu game da mai shagon, na ce musu yana Bamako," in ji Ahmed, ya ƙara da cewa an sake azabtar da mutane a karo na uku, kuma ya ci gaba da ba da amsar da ya bayar tun farko.

Bayan wannan bala'in, Ahmed ya ce an jefa shi cikin wata ƴar ƙaramar banɗaki, inda akwai wasu mutanen yankin da ya sani – ciki har da Hussein, wanda aka yi ɗan karen duka har ya kasa gane shi da farko.

"Bayan mintuna 40 suka kawo Umar [wani wanda ya sani], shi ma yana cikin wani mummunan hali, sun azabtar da shi, mun kwana a ban ɗakin, washe gari suka kawo burodi da karamin kofin shayi," in ji Ahmed.

Ahmed ya ce masu yi masa tambayoyin sun jefa shi cikin wani ɗakin girki, inda ya kwana tare da wasu mutane biyu da bai sani ba - wani ɗan ƙabilar Abzinawa, wanda ya shaida masa cewa an tsare shi ne yayin da ya ke kiwo ba tare da an gaya masa dalilin da ya sa aka kama sh ba, da kuma wani Balarabe da ya ce an ɗauko shi ne yayin da ya ke neman rakumansa.

Wani ɗan ƙabilar Abzinawa a kan raƙumi da wasu kayayyaki a kai, da wasu raƙuma a gabansa da bayansa, a ƙasar Mali.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Makiyaya suna zirga-zirga a hamadar arewacin Mali da rakumansu

Bayan sun kwana Ahmed yace an mayar da shi garejin jiragen saman.

"Sun kawo mutanen biyu (Ba abzinen da balaraben) suka fille kawunansu a gabana," in ji Ahmed.

A firgice Ahmed yayi ƙoƙarin danne hawaye yayin da yake shaida wa BBC abin da ya biyo baya.

"Sun kawo ɗaya daga cikin gawarwakin kusa da ni a jiƙe da jini, suka ce: "Idan ba ka gaya mana inda mai shagon ya ke ba, za ka fuskanci irin wannan hukuncin."

Ahmed ya ce an ceto ransa ne bayan wani kwamandan Wagner ya kira wani jami'in sojan Mali, wanda ya tabbatar masa da cewa mai shagon ba ya haɗa baki da masu iƙirarin jihadi.

Ahmed ya ce daga nan ne kwamandan ya je sansanin domin ya sake shi, tare da wani mai shago na daban da kuma Umar.

"Na shafe kwanaki 15 a can. Daga nan na yanke shawarar yin hijira zuwa Mauritania tare da matata da ƴaƴana," in ji Ahmed.

BBC ta tuntubi ma'aikatun tsaron Rasha da Mali domin jin ta bakinsu, amma har yanzu ba su mayar da martani ba.

Bayan ta yi iƙirarin kammala ayyukanta a Mali duk da cewa mastalar tsaro ta ci gaba da ta'azzara. Wagner ta fice ddaga Mali a watan Yunin wannan shekarar, kuma masu sharhi na cewa akasarin mayaƙanta sun koma ƙarƙashin ƙungiyar Africa corps.

Cibiyar bincike ta Timbuktu da ke Senegal ta yi ƙiyasin cewa kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na mayaƙan Afirca corps sun kasance, tsoffin mayaƙan Wagner ne.

Mayakan Wagner

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An tura Wagner zuwa ƙasar Mali bayan da sojojin gwamnatin ƙasar suka ƙulla ƙawance da ƙasar Rasha

Ahmed ya ce yana son a gurfanar da mayaƙan na Wagner a gaban kuliya, kuma a hukunta su kan ta'asar da suka aikata.

"Lamarin da na fuskanta na damuna. Yana matuƙar tayar mun da hankali," in ji shi yayin da yake zaune sanye da bakaƙen tufafi a sansanin, ba tare da sanin ko zai sake komawa rayuwarsa ta yau da kullun a matsayin mai tsare shago ba.