Muradun wa Amurka ke karewa ne a tattaunawar Rasha da Ukraine?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Luis Barrucho
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
A gargaɗin baya-bayan nan, Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya ce dole ne dakarun Ukraine su fice daga yankin Dobas da ke gabashin Ukraine ko kuma Rasha ta ƙwace yankin da ƙarfin tuwo, inda ya yi watsi da buƙatar kawo ƙarshen yaƙin da Rashar ke yi da Ukraine.
Kafin nan dai da ma Shugaban Nato, Mark Rutte, ya ce "akwai mutum ɗaya kawai a duniya da zai iya warware duk wani cikas" a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine.
Ya faɗi haka ne a taron ministocin harkokin waje da aka yi a Brussels ranar Laraba, kafin
Ya ƙara da cewa, "Wannan mutumin shi ne Shugaban Amurka, Donald Trump," yana kuma yabon ƙoƙarin tawagar Amurka wajen neman sulhu tare da masu ba Vladimir Putin shawara.
Ko da yake tattaunawar wannan makon a Moscow tsakanin Putin da wakilin Amurka, Steve Witkoff, ba ta haifar da wani babban ci gaba ba, fadar Kremlin ta ce ba daidai ba ne a ce Putin ya ƙi karɓar shawarwarin zaman lafiya da Amurka ta gabatar game da Ukraine.
Jami'an Rasha sun bayyana tattaunawar da cewa "mai amfani ce," kuma "akwai wasu shawarwari daga Amurka da za a iya tattaunawa," amma sun ce "ba a cimma wata matsaya ba" kan batun miƙa yankuna.
A halin yanzu, wasu masana suna cewa shirin da Shugaba Trump ke nema domin kawo ƙarshen yaƙin ya daidaita da muradun Rasha fiye da na Ukraine, kuma hakan na iya nuna inda tattaunawar za ta dosa.
Tattaunawar ta baya-bayan nan ta mayar da hankali ne kan sabon nau'in wani shiri na zaman lafiya 28 da jami'an Amurka da Rasha suka rubuta tun a watan Oktoba.
A tsarin farko, an gabatar da shawarwarin miƙa wasu sassan yankin masana'antar Donbas waɗanda Ukraine ke riƙe da su zuwa hannun Rasha, tare da rage girman rundunar sojin Ukraine.
Ba a san cikakken abin da aka canza a tsarin kafin tattaunawar wannan makon ba. Amma a ranar Lahadi, tawagar Amurka da Ukraine sun kammala kwanaki biyu suna aiki kan shirin a Florida.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce wasu abubuwa "har yanzu suna buƙatar a yi musu gyara," amma ya jaddada cewa "yanzu fiye da kowane lokaci akwai damar kawo ƙarshen yaƙin."
Shugaban majalisar tsaron ƙasa ta Ukraine, Rustem Umerov, zai gana da Witkoff a Miami ranar Alhamis.
Don haka, yaya Shugaba Trump ke daidaita buƙatun Moscow da Kyiv tare da burinsa na ganin ya cimma yarjejeniyar zaman lafiya, kusan shekara huɗu bayan Rasha ta mamaye Ukraine da ƙarfi?

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Trump ya ɗauki matakai da dama da ke amfani ga muradun Moscow" in ji Keir Giles a shirin Rasha da Eurasia a cibiyar nazarin Chatham House da ke Birtaniya, duk da cewa babu cikakken bayani kan dalilan hakan a fili.
Ya ce waɗannan matakan sun haɗa da dakatar da tallafin Amurka ga Ukraine a lokacin bazarar wannan shekarar, da kuma shrin rage yawan sojojin Amurka a Turai a duk lokacin da yake mulki.
Amma a watan Yuli, Trump ya yi alƙawarin ba Ukraine sabbin makamai tare da barazanar sanya takunkumi ga masu sayen kayan Rasha idan Moscow ba ta amince da zaman lafiya ba.
Giles ya ce abin da aka gabatar yanzu ba shirin zaman lafiya ba ne, sai dai Rasha ta sanya bukatunta a matsayin ginshiƙin tattaunawar ko a tsakiyar tattaunawa.
Wasu bayanan da aka fitar ko da ba a tabbatar da su ba sun nuna daidaituwa tsakanin Amurka da Rasha, a cewar Vitaliy Shevchenko na BBC Monitoring.
Bloomberg ta wallafa abin da ta ce rubutaccen tattaunawar waya da ta gudana a 14 ga watan Octoba, inda jakadan Amurka Steve Witkoff ya bai wa mataimakin Putin shawara kan yadda zai gabatar da shirin sulhu ga Trump.
Da yake magana kan alaƙar Amurka da Rasha a Fox News, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya soki ra'ayin da ya kira "ba shi da tushe" cewa bai kamata Amurka ta tattauna da Rasha ba inda ya ce: "Ba za ka iya kawo ƙarshen yakin Rasha da Ukraine ba ba tare da yi wa Rasha magana ba."
Rubio ya ce ba zai yiwu ba a yi ta tsammanin cewa Amurka za ta ci gaba da ba da kuɗi ba iyaka ga Ukraine muddin yaƙin yana ci gaba.
A cewar Emily Ferris, masaniyar tsaro ta cibiyar RUSI, ta ce Amurka ba ta goyon bayan ɓangare ɗaya, kawai tana aiki ne don kare muradunta. Abin da Amurka ke so in ji ta shine kawo ƙarshen yaƙin da ya daɗe yana addabar mutane da kashe rayuka.
A cewarta, Washington ta yanke shawarar cewa bai wa Rasha wasu rangwame ne hanya mafi sauƙi ta jawo ta shiga tattaunawar sulhu.
Ta ƙara da cewa Ukraine tana cikin rauni a ɓangaren soja da siyasa da tattalin arziƙi, don haka tana iya fuskantar matsin lamba cikin sauƙi yayin da Rasha kuwa ba ta jin matsin lamba saboda takunkumi ba su tasiri, soja ma ba ta tasiri, don haka babu madafar da za a matsa mata.
A karshe, Vitaliy Shevchenko ya ce ba wani abu sosai da Trump ya yi da zai sa Putin ya sauya ra'ayi, abin da ke sa shugaban Rasha ya ji tsananin ƙarfin guiwa.

Ferris ta gargadi cewa duk da cewa shirin Amurka ya ƙunshi abubuwa da dama da Rasha za ta so, bai bayar da duk abin da take nema ba, misali a tsayar da amfani da makamai ko sojoji a Ukrain da kuma ba ta son a sa mata kulawar ƙasa da ƙasa.
A cewarta cewa Rasha na iya yin sassauci a kan buƙatunta idan har an ba ta yarjejeniya mai matuƙar armashi, tana mai cewa za su iya gamsuwa da yankunan da suke riƙe da su yanzu, kuma ana iya tilasta musu ja da baya daga wasu wuraren da ba su mallaka ba.
Sai dai ta ce babban cikas ɗin shi ne: yawan tallafin sojan Yammacin Turai ga Ukraine, wanda Rasha ba za ta taɓa amincewa da shi ba.
A gefe guda, ƙasashen Turai sun fito da wani shiri daban, inda suka maye gurbin miƙa yankuna kai tsaye da tattaunawa kan musayar yankuna, tare da ƙarfafa batun tsaron Ukraine, wanda yake babbar damuwar Kyiv.
Putin dai yayi watsi da buƙatun Turai inda ya ce "ba masu karɓuwa bane", sannan ya ƙara da cewa:
"Ba za mu yi yaƙi da Turai ba, amma idan Turai na son ta yi yaƙi da mu, to a shirye muke."

Asalin hoton, EPA
Giles ya ce ana samun rikicewar tattaunawa game da yaƙin Ukraine saboda yaɗuwar bayanan bogi daga Rasha, musamman irin labaran da ke cewa Rasha tana samun manyan nasarori a fagen daga.
Wannan, a cewarsa, yana sa mutane su yi tunanin cewa Ukraine ta kusa ƙarewa kuma dole ne a yi yarjejeniyar zaman lafiya cikin gaggawa.
Ya ce "A zahiri Rasha ba ta samu manyan nasarori ba a watanni da suka wuce. Sai dai ta iya sa kafafen sada zumunta na Yamma su yi tunanin tana cin nasara."
A yanzu haka, Ukraine da Rasha suna bayar da rahoto daban-daban kan halin da ake ciki a birnin Pokrovsk da ke Donetsk. Rasha ta bayyana cewa ta karɓe birnin, tare da yaɗa bidiyo na sojojinta suna daga tutar Rasha.
Amma duk da cewa sojojin Ukraine sun ce halin da ake ciki a ƙasar ya yi tsanani, har yanzu suna riƙe da ikon wasu sassan birnin.
Giles ya yi imanin cewa har yanzu ba a kai ga kayar da Ukraine ba yana cewa:
"Yaƙin ba ya dab da ƙarewa, kuma Ukraine na da ƙarfi sosai har yanzu, tana jawo wa Rasha babban hasara."
Sai dai ya nuna shakku cewa tattaunawar Amurka da Rasha za ta haifar da wani abu da zai amfani Ukraine:
A hirarsa da Fox News, Marco Rubio ya jaddada cewa Ukraine da Rasha ne za su yanke hukunci, ba Amurka ko Turai ba.
Ya ce:
"A ƙarshe dai, ba mu ne masu yanke hukunci ba. Ba mu cikin yaƙin. Ba mu ne muke fafatawa ba."










