Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za ku kare kanku daga matsalar bugun zuciya
- Marubuci, Ameer Ahmed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
Zuciya mai lafiya na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa jikin mutum yana aiki yadda ya kamata. Zuciya na harba jini domin kai iskar oxygen da muhimman sinadarai zuwa sassan jiki.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cututtukan zuciya da jijiyoyi (wanda ake kira Cardiovascular Diseases) su ne mafi yawan dalilan mutuwa a duniya, inda suke kashe kusan mutane miliyan 18 a kowace shekara.
Daga cikin mutuwar da waɗannan cututtuka ke haddasawa, hudu cikin biyar na faruwa ne sakamakon bugun zuciya ko bugun jini a kwakwalwa.
Kiyaye lafiyar zuciya — wanda ga manya ke nufin zuciya tana bugawa sau 60 zuwa 100 a cikin minti ɗaya a lokacin hutu — abu ne da mutum ya kamata ya kula da shi a kullum, in ji masana na zuciya.
"Za mu iya rage lahani ga zuciyarmu tun daga ƙuruciya ta hanyar cin abinci mai kyau da motsa jiki, da guje wa amfani da kayayyakin taba," in ji Dr Evan Levine, ƙwararren likitan zuciya daga Amurka.
Amma, shin lamarin yana da sauƙi haka? Wato cewa, zuciya mai lafiya za ta rage haɗarin kamuwa da bugun zuciya?
Mene ne bugun zuciya?
Bugun zuciya na iya faruwa ne idan jinin da ke zuwa zuciya ya toshe ba zato ba tsammani.
Idan jinin da ke kawo iskar oxygen zuwa zuciya ya tsaya ko ya ragu sosai, tsokar zuciya na iya samun rauni ko kuma ta fara mutuwa. Idan ba a samu kulawar gaggawa ba, wannan na iya haddasa mummunan lahani ga zuciya da ba za a iya gyarawa ba.
Idan babban yanki na zuciya ya sami irin wannan lahani, zuciya na iya daina bugawa gaba ɗaya – wanda hakan ka iya janyo mutuwa.
Rabin mutuwar da ake samu sakamakon bugun zuciya na faruwa ne cikin sa'o'i uku zuwa hudɗu bayan alamun farko sun bayyana. Saboda haka, yana da matuƙar muhimmanci a ɗauki bugun zuciya a matsayin matsala ta gaggawa da ke buƙatar kulawa nan da nan.
Babban abin da ke haddasa bugun zuciya shi ne cutar jijiyar zuciya (coronary heart disease) – wato lokacin da wani kitse ke taruwa a cikin jijiyoyi, wanda ke hana jinin gudana yadda ya kamata ta hanyar matse hanya.
A kowace shekara, kusan mutum 805,000 ke fama da bugun zuciya a Amurka. Daga cikin waɗannan, 605,000 ne ke fama da shi karo na farko, yayin da 200,000 ke fuskantar shi bayan sun taɓa yi a baya.
Wannan na nufin kusan mutum ɗaya ke samun bugun zuciya duk bayan daƙiƙa 40, a cewar Hukumar Lafiya ta Amurka (CDC).
Ta yaya zan gane idan ina fama da bugun zuciya?
Bugun zuciya na iya zuwa da alamomi daban-daban, amma mafi yawanci shi ne jin zafi a ƙirji – wanda ba wai kawai zafi mai kaifi ba ne, har ma da takurewa da matsewa me ƙarfi da tsanani a faɗin kirji.
Wasu mata na iya jin wannan zafi a ƙirji tare da zafi a wuya da kuma a hannaye biyu.
Dr Ailin Barseghian, likitar zuciya daga California, ta ce a farko, ana iya ɗaukar bugun zuciya a matsayin ciwon ciki. Amma saɓanin ciwon ciki, bugun zuciya na haifar da zafi a wasu sassan jiki kamar hannu na hagu da haɓa da baya da kuma ciki.
Wasu daga cikin sauran alamomin bugun zuciya sun haɗa da jin nauyi a kai ko jin juyayi da zufa mai yawa da wahalar numfashi da kuma shakar iska da ƙarfi.
Kodayake wasu bugun zuciya na zuwa ba zato ba tsammani, akwai lokutan da ake samun gargaɗi sa'o'i ko kwanaki kafin hakan ya faru. Jin zafi a ƙirji wanda bai daina ba ko da an huta na iya zama gargaɗi.
"Idan ba a dawo da gudun jini ba cikin sa'o'i uku, tsokar zuciya na iya fara mutuwa. Ina ba da shawarar a narkar da maganin aspirin a bakin wanda ya samu bugun zuciya har sai masu bada agajin gaggawa sun iso," in ji Dr Ailin Barseghian.
Masana lafiyar zuciya na jaddada muhimmancin samun kulawa nan take idan ka yi tunanin kana fama da bugun zuciya.
"Ya kamata ka san kanka da abubuwan haɗarin – shekaru da nauyi da halayen shan taba da barasa, da kuma tarihin cutar a iyali. Idan kana da waɗannan abubuwa kuma kana jin takurewa da matsewa a ƙirji, to ka kira agajin gaggawa nan take," in ji Dr Evan Levine, likitan zuciya daga Amurka.
Yadda za a kiyaye kamuwa da bugun zuciya
Akwai hanyoyi da dama da za a iya bi domin rage haɗarin kamuwa da bugun zuciya, ciki har da rage hawan jini da matakin kitse a cikin jinin jiki ta hanyar abinci mai kyau da motsa jiki.
Maiƙo wato cholesterol wani sinadari ne da ke cikin jini wanda ke da amfani wajen gina ƙwayoyin jiki masu lafiya. Amma idan ya yi yawa, yana iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya da jijiyoyi.
Masana zuciya suna jaddada muhimmancin rayuwa mai tsafta da ƙoshin lafiya, a matsayin wani abu da za mu iya aikatawa kullum don kare zuciyarmu.
Ana ba da shawarar cin abinci mai ƙunshe da nau'in fibre da mai kaɗan tare da rage amfani da gishiri zuwa kusan gram 6 a rana, domin yawan gishiri yana haifar da hawan jini.
Hakanan, ana shawartar kaucewa cin abinci da aka sarrafa fiye da kima da kuma abincin da ke ɗauke da kitse dayawa, domin hakan na ƙara yawan cholesterol a jiki.
Waɗannan na'ukan abincin sun haɗa da meat pie da kek da alawa (biscuits) da sausages da man shanu da abinci da ke ɗauke da man gyaɗa ko manja.
A cewar masana, abinci da aka dafa da mai da yake da kyau, yana taimakawa wajen ƙara cholesterol mai kyau a jiki da kuma buɗe jijiyoyi. Irin waɗannan abinci sun haɗa da man kifi da man avocado da man gyada da man kayan lambu (vegetable oils).
Haɗa cin abinci mai kyau da motsa jiki na yau da kullum na ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen kiyaye lafiyar zuciya.
Samun nauyin jiki da ya dace yana rage haɗarin samun hawan jini. Dr Evan Levine, masani kan cututtukan zuciya, yana ba da shawarar a motsa jiki na tsawon mintuna 30 a rana, sau biyar a mako.
Amma babban shawararsa don rayuwa mai lafiya ita ce kada mutum ya taba shan taba ko sigari ko e-cigarette (vape).
Wani bincike da aka yi kan mutum 24,927 ya nuna cewa masu amfani da sigari ko wace iriya duka suna da haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya iri ɗaya.
Ga mutanen da suka taɓa samun bugun zuciya sau ɗaya, ƙungiyar fadakarwa kan lafiyar zuciya ta America ta bayyana cewa kusan mutum 1 cikin 5 ana sa ran za su koma asibiti cikin shekaru biyar saboda bugun zuciya karo na biyu.
Ko yaya, amfani da magungunan rage maiƙo kamar 'statins' da 'ezetimibe' bayan samun bugun zuciya na taimaka rage yiwuwar faruwar karo na biyu, a cewar binciken da masana daga Imperial College London da Jami'ar Lund ta Sweden suka gudanar.
Waɗannan magunguna suna rage yawan cholesterol a jiki inn ji Dr Ailin Barseghian.
Ƙaruwar matasa masu fama da bugun zuciya
Duk da cewa haɗarin bugun zuciya yana ƙaruwa ne da shekaru, bayanan da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa a Amurka ta fitar sun nuna cewa ana samun ƙaruwa a cikin matasa.
A shekarar 2019, kimanin kashi 0.3 cikin 100 na mutanen da shekarunsu ke tsakanin 18 zuwa 44 ne suka kamu da bugun zuciya. Amma zuwa shekarar 2023, wannan adadin ya ƙaru zuwa kashi 0.5.
Dr Evan Levine ya danganta wannan ƙaruwar da canje-canjen salon rayuwa, ciki har da yawan cin abinci da aka sarrafa da ƙarancin motsa jiki a tsakanin wannan rukuni na shekaru.
"Muna buƙatar motsa jiki fiye da yadda muke yi — ba sai an je dakin motsa jiki ba, amma iya motsa jiki a gida ma.
Abin damuwa shi ne, tun bayan cutar COVID-19, mutane da ke aiki daga gida suna shiga cikin salon rayuwa ba tare da motsa jiki wanda hakan na da haɗari," in ji shi.
Yayin da aka san shan taba ko sigari, hakan yana daga cikin abubuwan da ke haifar da taruwar kitse a cikin jijiyoyin jiki, masana zuciya irin su Dr Evan Levine na nuna damuwa kan tasirin shan sigari ta e-cigarrete musamman ga matasa, wanda har yanzu ba a san cikakken illarsa ba.
Dr Ailin Barseghian kuma ta ƙara da cewa;
"Abubuwan gado irin su 'familial hyperlipidaemia' (wani yanayi da ke haifar da yawan cholesterol tun daga haihuwa) su ma na daga cikin dalilan da ke haddasa bugun zuciya tun da wuri."
"Haka kuma, abubuwa kamar damuwa da rashin isasshen barci na ƙara samun karɓuwa a matsayin manyan abubuwan da ke da tasiri wajen kamuwa da bugun zuciya."