Sojojin Benin sun fuskanci mummunan hari a kusa da kan iyakar ƙasar

Lokacin da sojojin Benin ke barin sansanin soji na Ouidah a arewacin ƙasar, domin halartar atisayen soji na haɗin gwiwa a watan Disamban 2004 a Ouidah lokacin atisayen soji na 'RECAMP IV'.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A baya-bayan na Benin ta sha fuskantar ƙaruwar hare-haren masu ikirarin jihadi a arewacin ƙasar
    • Marubuci, Paul Njie & Wycliffe Muia
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomin Benin sun ce dakarun sojin ƙasar sun fuskanci mummunan hari a kusa da kan iyakar ƙasar da ƙasashen Nijar da Burkina Faso.

Babban hafsan sojin ƙasar, Kanal Faizou Gomina ya ce an kai hari kan ɗaya daga cikin sansanonin sojin ƙasar mafiya ƙarfi a yankin Alibori da ke arewacin ƙasar ranar Laraba da maraice.

"Mun fuskanci mummunan hari a sansaninmu," in ji Kanal Gomina.

A baya-bayan nan ƙasar na fuskantar ƙaruwar hare-hare a yankin arewacin ƙasar.

Wani abu da ake zargin masu iƙirarin jihadi da ke zaune a maƙwabtan ƙasashe da ƙaddamarwa.

Fiye da sojojin Benin 120 aka kashe tsakanin 2021 zuwa Disamban bara, kamar yadda wata majiyar diplomasiyyar ƙasar ta shaida wa AFP.

A watan da ya gabata ma, wasu 'yanbindiga suka kashe sojojin ƙasar uku, tare da raunata huɗu, da ke kula da bututun mai a arewa maso gabashin ƙasar.

Kanal Gomina, bai bayyana adadin sojojin da aka kashe a harin na ranar Laraba ba, to amma babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar, 'Democrats', ta ce kusan sojoji 30 ne aka kashe a yankin na Alibori, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

To amma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata majiyar soji na cewa sojoji 28 aka kashe a harin.

"Muna ci gaba da tantance ɓarnar, kuma mun kashe maharan 40 a lokacin harin,'' in ji majiyar sojin.

Kanal Gomina harin ya kasance, ''ɗaya daga cikin manyan hare-haren da aka kitsa''.

Haka kuma babban hafsan sojin ƙasar ya yi kira da manyan kwamandojin sojin ƙasar su inganta tsare-tsarensu domin magance kowace irin barazanar tsaro.

"Manyan dakarunmu da shugabannin rassa na sansanoninmu, ku miƙe tsaye, akwai jan aiki a gabanmu," in ji shi.

A shekarar 2022, Benin ta jibge dakaru kusan 3,000 a kusa da kan iyakokinta domin magance matsalar tsaro a raewacin ƙasar.