Dalilan da suka sa Nijar ke ɗari-ɗari da jamhuriyar Benin

..

Asalin hoton, Getty Images

Firaministan jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine yayi allahwadai da abin da ya kira cin zarafin da hukumomin ƙasar Benin suka yi musu na saɓa yarjeniyoyin da suka ƙulla da Niger da China dangane da fitar da ɗanyen man jamhuriyar daga tashar jiragen ruwan Coutonou.

Firaiministan wanda ya jaddada cewa akwai yarjejeniya tsakanin jamhuriyar Niger da Benin, ta haka kuma aka ƙulla tsakanin jamhuriyar Benin da China har ma da ƙasashen biyu inji Firaministan, duka waɗannan yarjeniyoyin hukumomin Benin sun karya su.

“Wannan bututun na mai da aka yi daga ƙasarmu ta Niger can Kulale har zuwa ƙasar ta Benin, kamin ayi shi akwai yarjejeniya da aka yi, bayan an yi shi akwai yarjejeniya da ke tsakaninmu da su. Kai ko yaƙi za a yi ba a iya a tsaida wannan man”.

Akwai takarda tsakanin gwamnatin tamu da tasu da ta haramta masu ɗaukar matakan da za su sa wannan man ya gudana. Akwai takarda tsakaninsu da su da mutanen China, amma duk da haka mutanen nan shi shugaban nasu ya fito ƙarara ya ce ba zai bari ba a ɗora wannan man bisa ruwa, sai mun buɗe iyaka”. In ji Firaiministan.

Dangane da batun rufe iyakoki Firaministan Ali Mahaman Lamine Zeine ya sanar da cewa saboda wasu dalilai na tsaro ne Nijar ta yanke shawarar rufe wannan kan iyaka, da ma wasu dalilan da ya lissafa.

“Iyaka bakwai gare mu a ƙasar Nijar kuma cikin ECOWAS ƙasashe huɗu ne muke da su. Da ma ba a zancen Mali da Burkina Faso ko Najeriya da aka ce sun rufe iyakarsu. To bisa wannan iyakokin namu ƙasashe guda baƙwai, ƙasar Benin ce kawai ta ɗauki matakan da wato ko mage ba ta wucewa.

To bisa haka da suka ce sun ga dama sun ɗage wannan takunkumi, an buɗe iyaka. mu kuma da magabatanmu musamman ma sojojinmu suka hango cewa lokacin buɗe iyaka bai yi ba. Mene ne dalili? Turawan da muka kora daga nan, sai suka kewaya suka koma can, suna nan mun san da zamansu." In ji Lamine.

Firaministan ya kuma ƙara da cewa akwai sansanoni a jamhuriyar Benin ciki har da wasu da ake "horar da ƴan ta’adda, waɗanda ake horarwa da zummar su kawo tashin hankali a Nijar".

Harwayau, Lamine Zeine ya ƙara da cewa akwai sansanoni har guda biyar da aka gano a jamhuriyar ta Benin.

Da kuma yake magana a kan matakin ƙasar ta Benin na hana shiga da abinci dangin Masara da shinkafa da sauran su zuwa cikin jamhuriyar, Ali Muhammad Lamine Zeine cewa yayi "akwai niyya ga gwamnatin Nijar ta cika rumbunan ajiya taf da cimaka domin amfanin talakawa."