Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin kamfanin NNPCL ya talauce ne?
Tun bayan da kamfanin man Najeriya, NNPCL ya fitar da wata sanarwa ranar Lahadi inda ya bayyana cewa yana fama da ƙarancin kuɗi sakamakon bashin dala biliyan shida ($6bn) da ake bin sa, ƴan Najeriya suke shiga tsoron ko kamfanin ya talauce ne.
Sanarwar wadda mai magana da yawun kamfanin ya fitar ta alaƙanta rashin kuɗin da dogayen layukan mai da ake gani a ƙasar.
A baya dai kamfanin ya sha musanta rahotannin da ke nuna NNPCL na fama da bashi abin da ke janyo matsalar layukan da ƙaranci mai a Najeriya.
Tambayoyin da ƴan Najeriya ke yi yanzu su ne shin ko NNPCL ya talauce ne? Kuma me hakan yake nufi sannan ta yaya zai shafi wadatar mai da farashinsa a ƙasar?
Me ya janyo kuɗi ya ƙare wa NNPCL?
Malam Shu'aibu Miƙati wani masani kan makamashi ya lissafa wasu dalilai da ka iya jefa kamfanin na NNPCL cikin ƙangin rashin kuɗi kamar haka:
- NNPCL ya ciyo bashin dala biliyan 3.5 daga wani bankin Afirka da ke ƙasar Misra a bara. Saboda haka idan NNPCL ya ce ana bin sa bashi ba ƙarya ba ne. Kuma dole ne ya biya.
- Yanzu kusan shekaru fiye da 15, matatun man fetur na ƙasar ba su aiki amma kamfanin na biyan ma'aikatan matatun albashi. Sannan ana biyan tallafin man fetur. Ka ga nan ma dole kamfanin ya samu tasgaro.
- A baya Najeriya na fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu ɗari biyu inda yanzu kuma ake fitar da ganga miliyan da dubu ɗari biyu.
Me hakan ke nufi?
Masanin ya ce abubuwa biyu ne ya fahimta daga cikin wannan iƙirarin na kamfanin NNPCL kamar haka:
Na farko ƴan Najeriya ka iya fuskantar matsala wajen samun kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya da jihohi da ma ƙananan hukumomi bisa la'akari da yadda ƙasar ta dogara kacokan ga man fetur a matsayin kuɗaɗen shiga saboda NNPCL zai mayar da hankali wajen biyan basukan da ake bin sa.
Abu na biyu kuma shi ne za a iya samun ƙaranci da matsalar samun man fetur a ƙasar tunda NNPCL ne ke shigar da mai ƙasar. Amma gwamnati za ta iya shigar da man ta wata hanyar idan tana son guje wa wannan matsala.
Ta yaya hakan zai shafi farashin mai a Najeriya?
Malam Shu'aibu Miƙati ya ƙara da cewa kai tsaye ba za a iya cewa karayar arziƙin da NNPCL ya ce ya samu zai shafi farashin man fetur ba.
Sai dai kuma ya ce "bashin da ake bin NNPCL ba zai zama dalilin ƙaruwar farashin man fetur ko kananzir ko gas suka ƙaru ba. Abubuwa guda biyu ne za su iya sanya farashin man ya karu: wato faɗuwar darajar naira da kuma tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya," in ji Miƙati.
Sai dai kuma masanin bai musanta hasashen da ƴan Najeriya ke yi ba na yi wa iƙirarin na NNPCL kallon yunƙurin ƙarin farashin mai "lallai idan aka ce da makaho ba rami to ka ga mai ya kawo labarin rami babu ramin. Akwai ƙanshin gaskiyar samun ƙarin farashin litar mai musamman idan man ya yi ƙaranci tunda NNPCL ɗin ba zai iya samar da yawan man da kasar take buƙata ba.
Sannan kamfanin ba shi da kuɗin da zai biya tallafi da wai aka ce ana biya duk da dai mu har yanzu mun kasa fahimtar shin ana biyan tallafi ko kuwa ba a biya. Domin dai mun san shugaba Tinubu ya ce ya cire tallafi...," in ji Shu'aibu Miƙati.
Wane tasiri matatar man Ɗangote za ta yi?
"E to man fetur daga matatar Ɗangote ka iya sa a samu wadatuwarsa mai a Najeriya amma kuma hakan ba ya nufin farashinsa zai zama mai sauƙi. Abubuwa ne guda biyu mabanbanta juna," In ji masanin.
Malam Miƙati ya bayyana dalilinsa da cewa "abubuwan da ake la'akari da su a tace ɗanyen man fetur su ne na farko nawa ake sayar da gangar ɗanyen mai sannan nawa ake tace shi sannan nawa ake biya kuɗin dakon man da inshora? Ka ga za ka ga mene ne Ɗangote ba zai biya ba a nan? Abu biyu ne kawai wato kuɗin dako da insora da haraji su ne za a samu ɗan ragin da ba zai taka kara ya karya ba."