Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe za a gyara katsewar lantarki a arewacin Najeriya?
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Kwana tara kenan a jere aƙalla jihohi tara na arewacin Najeriya ke cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki, lamarin da ya jefa harkokin rayuwa da na tattalin arziƙi cikin yanayi maras daɗi.
Asibitoci da masana'antu da gidajen al'umma duka na cikin wani hali, inda sakamakon rashin wutar a asibitoci ke jawo jama'a na rasa rayukansu,a cewar rahotonni, sannan gidaje na fuskantar matsalar rashin ruwan sha.
Katsewar lantarki a yankin na arewa na zuwa ne ƴan kwanaki bayan ɗaukacin ƙasar ta yi fama da katsewar wutar har sau uku a cikin kwana biyu sakamakon lalacewar babban layin wutar na ƙasa wato national grid.
Wannan hali ne dai ya sa ƴan arewacin ƙasar ke neman amsoshin tambayoyi uku: yaushe za a gyara wutar? Mene ne ya jawo matsalar? Me ce ce mafita domin ganin ba a sake koma wa matsalar ba?
BBC ta yi nazari, ga kuma amsoshin waɗannan tambayoyi:
Yaushe za a gyara wutar?
"Sai an samar da tsaro a dajin da ke ɗauke da layin sannan a gyara, idan ba haka ba kuma to babu ranar gyara" In ji Ali Bukar jami'in hulɗar cinikayya na kamfanin TCN
Kamfanin na TCN dai ya ce jami'ansa na ƙokarin shawo kan matsala, inda ake ta ganin jami'an kamfani na ta faman gyare-gyare.
To sai dai gyaran ba na layin lantarkin 330kV da ke Ugwaji-Apir da ke tsakanin Shiroro zuwa Kaduna ba ne kamar yadda majiyar BBC a kamfanin na TCN ta shaida.
"Gaskiya ba layin ake gyarawa ba saboda akwai matsalar tsaro a wurin. Muna kyautata zaton ƴan ta'adda ne suka kayar da turakun layin wutar ta hanyar saka masa bam, to ka ga ai zai yi wuya a iya zuwa wurin domin a gyara."
Yanzu gyaran da ake yi shi ne na layin da ya tafi daga Benue zuwa Jos wanda idan aka gyara zai samar da kwarya-ƙwaryar wuta ga wasu jihohin na arewa. Amma abin da ya kamata jama'a su sani shi ne ko an gyara wannan layin to fa ba wai za a samu wuta kamar a baya ba idan dai har ba a gyara wancan layin na Shiroro ba wanda shi ne ke bai wa arewa wuta mai yawa.
Shi layin Benue-Jos yana samar da kaso ɗaya bisa huɗu na wutar da arewa ke buƙata ne. Kenan ko da an gyara bai zama lallai gidaje su samu wutar da suke buƙata ba.
Saboda kamfanoni da ke dillancin wutar yanzu haka suna matse saboda ba su da wutar da za su samu kuɗi. Saboda haka da zarar sun samu wutar za su fi mayar da hankali ga masana'antu wato inda za su samu kuɗi." In ji majiyarmu a TCN.
Mene ne ya jawo katsewar wutar?
Kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a Najeriya wato Transmission Company of Nigeria, TCN, ya danganta rashin wutar da tangarɗa da ɗaya daga cikin layuka biyu na lantarkin 330kV da ke garin Ugwaji-Apir da ke tsakanin Shiroro zuwa Kaduna.
Layukan biyu dai su ne suka ɗauki wuta daga babban layin wutar lantarki na ƙasa wato national grid inda suke shayar da jihohin Kano, Katsina, Jigawa da Kaduna da Bauchi da Gombe da wasu ƙarin jihohin arewa maso gabas da ma arewa ta tsakiya.
Ali Bukar jami'in hulɗatayyar cinikayya na kamfanin TCN ya shaida wa BBC cewa "ana zargin cewa ƴan ta'adda ne suka sa bam a ɗaya daga cikin turakun layin wutar. Kuma da ma kafin faruwar hakan ɗaya layin na Benue-Jos ya lalace."
Mafita
Masana da jami'an gwamnati da suka tattauna a shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa na ranar Juma'ar da ta gabata sun yi amanna cewa hanya ɗaya ce tilo ta tabbatar da cewa yankin na arewaci bai sake fuskantar irin wannan katsewar wutar ba a nan gaba.
Masanan da suka haɗa da Ali Bukar jami'i a TCN da Injiniya Sani Bala, ɗan majalisar wakilai daga Kano sun amince cewa dole ne gwamnatocin jihohi su samar da tashoshin wutar lantarki ko domin su gamsar da buƙatun masana'antun jihohin.
Wane hali jama'a ke ciki?
Tun dai bayan faruwar katsewar wutar lantarkin, ƴan arewacin ƙasar suka fara hawa kafafen sada zumunta suna bayyana halin da suke ciki musamman irin yadda ake samun asarar dukiyoyi da ma rayuka.
Wata mai suna Aishatu a shafin X ta wallafa cewa "wata ƙawata ta haifi tagwayen bakwaini jiya amma a yau suka koma baki ɗayansu saboda rashin wutar lantarki."
Shi ma wani da ake kira Muhammad Saulawa a shafin X, ya ce ɗansa mai shekara 11 ya rasu sakamakon tsayawar takunkumin iskar da ke hancinsa saboda ɗaukewar wutar lantarki a ranar Talatar da ta gabata.
Nan kuma wata ce mai suna Fauziyya D. Sulaiman take nuna irin girmar rashin wutar inda take kira da a gyara wutar lantarki a arewacin Najeriya, inda ta maƙala hoto daga ƙirƙirarriyar basira ta AI.
Shi ma wani da ake kira Sadiq Madabo a shafinsa na Facebook, ya wallafa cewa al'ummar unguwar Tudun Murtala na sayen jarkar ruwa mai lita 25 a kan naira 250 zuwa 300 sakamakon rashin wutar lantarki.