Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abun da ya sa Ecowas ta ɗage wa Nijar da Mali da Burkina Faso takunkumai
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ɗage tarin takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Giunea.
Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a wani taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya.
Ƙungiyar ta ce a yanzu za ta iya gayyatar ƙasashen huɗu zuwa tarukanta da suka shafi tsaro da zaman lafiya.
Takunkuman sun haɗa da na zirga-zirga tsakanin ƙasashen, da na kasuwanci da tattalin arziki.
Huka kuma ƙungiyar ta jaddada kiranta na sakin hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazaoum da sojojin ƙasar ke ci gaba da yi wa ɗaurin talala.
Ecowas ta kaƙaba wa ƙasashe takunkuman ne bayan da sojoji suka kifar da gwamnatocin fara hula a ƙasashen.
Daga cikin takunkuman da ƙungiyar ta ƙaƙaba wa ƙasashen sun haɗa da rufe iyakokin ƙasashen da na ƙungiyar da kuma yanke wutar lantarki a Nijar da sauran takunkuman karya tattalin arziki.
A makonnin baya-bayan ne ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso suka ayyana ficewa daga ƙungiyar bayan da suka zargi ƙungiyar Ecowas da ƙaƙaba musu takunkuman karya tattalin arziki.
Wasu dalilan da Ecowas ta bayyana domin dage wa kasashen takunkuman sun hada da:
Azumi
Dalili na farko da Ecowas bayar kan dage takunkuman shi ne cewa a yanzu haka mabiya addinin kirista na cikin lokacin azumi, wanda ake kira ‘lent’ a turance, sannan kuma Musulmai na gab da fara nasi azumin a cikin watan Ramadana.
A cikin sanarwar da ta fitar, Ecowas ta ce: “Hukumar ta yi la’akari da lokacin azumin kirista na ‘lent’ da kuma karatowar watan azumin Ramadana”.
Azumi dai lokaci me da mutane kan bukaci karin nau’ukan abinci masu tallafa wa jiki da kara lafiya.
Sai dai a irin wannan lokaci akan samu tashin farashin kayan abinci saboda bukata da kan karu.
jin kai
Baya ga azumi Ecowas ta bayyana jin kai a cikin dalilanta na dage wa kasashen uku takunkuman.
Dama dai takunkuman da kungiyar ta kakaba wa kasashen sun haifar da tashin farashin kayan abinci da na masarufi a kasashen.
Haka nan katsewar lantarkin da ake samar wa Jamhuriyar Nijar daga Najeriya ya jefa wasu yankuna da dama na Nijar din cikin duhu.
Wannan lamari ya shafi harkokin kasuwanci da tattalin arziki tare da kara jefa masu karamin karfi cikin halin kunci.
Tsaro
Sanarwar kungiyar ya bayyana cewa takunkuman za su kawo cikas ga ayyukan tabbatar da tsaro da ke gudana a yankin na Yammacin Afirka.
“Janyewar (kasashen) zai shafi hadin kai na tsaro a bangaren musayar bayanan sirri da shigar su cikin yarjeniyoyin yaki da ta’addanci a yankin, kamar shirin tsaro na Accra da kuma Dakarun tabbatar da tsaro na kasa da kasa”. In ji sanarwar.
Tun bayan juyin mulkin dai an samu karuwar rashin tsaro a wasu yankuna na kasashen.
Hare-haren masu dauke da makamai sun karu a yankunan iyakar Mali da Nijar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji da fararen hula.
Ecowas ta riƙa fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane kan ta ɗage wa ƙasashen takunkuman.
Ko a makon da ya gabata ma tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Yakubu Gowon wanda shi ne mutum ɗaya tilo da ya rage cikin shugabanin da suka kafa ƙungiyar, ya yi kira ga shugabanninta da su ɗage wa ƙasashen takunkuman.
Nijar ta samu kanta cikin takunkuman Ecowas bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin farar hula da Mohamed Bazoum cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.
Dama dai masu sharhi sun daɗe suna ta kiraye-kiraye ga shugabannin ƙungiyar su yi kaffa-kaffa, su mai da hankali wajen lalamar 'ya'yan kungiyar idan ba haka ba garin gyaran gira a rasa ido.
Duk da cewa tun da farko shugabannin kungiyar Ecowas ɗin sun cije a kan matsayinsu na dakatar da kasashen da suka bijire wa demokuradiyyar tare da sanya musu takunkumi, Farfesa Jibrin Ibrahim ya shaida wa BBC cewa ba gazawa ba ce idan suka sassauta domin a samu maslaha.
Mazauna sassan Jamhuriyar Nijar da dama dai sun koka dangane da tsadar rayuwa da suka shiga sakamakon rufe iyakokin ƙasar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
'Yan kasuwa sun ƙara farashi kan kayayyakin masarufi, suna masu alaƙanta hakan da takunkuman da aka saka wa ƙasar sakamakon juyin mulkin sojoji.
Tuni wasu mazauna birnin Yamai suka ce hauhawar farashin ta fara kaiwa matakin da ba su taɓa gani ba.
Sun kuma alaƙanta lamarin da yanke alaƙa tsakanin ƙasashen Ecowas da ƙasarsu.
Cikin matakan da ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar ɗauka har da na ƙarfin soja yayin wani taron da ta gudanar a Abuja cikin shekarar da ta gabata.