Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Majalisa ta hana Tinubu sayen jirgin ruwa, ƴan kwadago za su koma yajin aiki
Wannan maƙala na ɗauke da muhimmai daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata na 30 ga watan Oktoba zuwa 4 ga Nuwamba.
Majalisar wakilai ta yi watsi da buƙatar Tinubu ta sayen jirgin ruwan alfarma
Majalisar wakilan Najeriya ta cire kuɗi naira biliyan biyar da aka ware a cikin ƙaramin kasafin kuɗin ƙasar domin sayen jirgin ruwan shaƙatawa na shugaban ƙasa.
Shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi, Abubakar Bichi, shi ne ya sanar da hakan ranar Alhamis bayan sun amince da ƙaramin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17.
Bichi ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin ya mayar da kuɗn zuwa ɓangaren bashin karatu na gwamnatin tarayya, inda a yanzu kuɗin da aka ware wa bashin ya kai naira biliyan 10.
Dama dai batun sayen jirgin ruwan shaƙatawan na shugaban ƙasa ya haifar da muhawara a tsakanin al'umma, inda mutane da dama suka soki lamarin.
Boko Haram ta kashe kusan mutum 40 a Yobe
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe ta ce wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun halaka kusan mutum 40 a jihar da ke arewa maso gabashin ƙasar tsakanin ranakun Litinin da Talata.
Sun ce mayaƙan sun riƙa harbin mutane da bindiga da kuma jefa masu bam a ranakun Talata da Laraba.
Ana ganin cewa wannan shi ne wani hari mafi muni da aka kai a jihar cikin wata 18.
Ƴan sintiri da ke aikin samar da tsaro a yankin sun ce mayaƙan na Boko Haram sun kai musu harin ne bayan da mazauna ƙauyukan suka ƙi biyan kuɗaɗen harajin da ƴan bindigar suka ƙaƙaba musu.
Mai magana da yawun 'yan sandan Yobe ya faɗa wa BBC Hausa cewa maharan sun fara kai hari ne ranar Talata tare da kashe gomman mutane a yankin ƙaramar hukumar Geidem.
'Yan bindigar sun sake far wa masu zaman makoki a ranar Laraba, inda nan ma suka kashe mutane da yawa.
Ya ce har yanzu ba su kai ga tattara alƙaluman waɗanda aka kashe ba, amma mazauna yankin na cewa adadinsu ya kai kusan 40.
Sau da dama gungun ƴan bindiga a wasu ƙauyukan Najeriya kan nemi mazauna yankunan su biya haraji a wani yunƙuri na tabbatar da ikonsu.
Kungiyar ƙwadago za ta shiga yajin aiki sanadiyyar 'kama shugabanta'
Gamayyar ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya na NLC da TUC sun bayyana aniyarsu ta shiga yajin aikin gama-gari sanadiyyar "kamawa da kuma dukan" da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Ƙungiyar ta sanar da batun yajin aikin, wanda zai fara a ranar Laraba a wata tattaunawa da manema labarai ranar Juma'a, a Abuja.
Shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun kuma bai wa gwamnatin tarayya sharuɗɗa shida da suke so a cika.
Cikin sharuɗɗan akwai sauke kwamishinan ƴan sanda na jihar Imo, da babban jami'in ƴan sanda na yankin da lamarin ya faru bisa zargin su da hannu a "cin zarafi da kuma wulaƙanta Mista Ajaero da sauran ƴaƴan ƙungiyar."
Kwale-kwale ya kife a jihar Adamawa
Rahotannin da muke samu daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani jirgin ruwa ya kife ɗauke da fasinjoji da dama.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Fufore da ke jihar.
Zuwa yanzu an ciro gawawwaki shida, yayin da aka ceto mutane 14 da ransu.
Zan kori duk ministan da ya gaza taɓuka abin kirki - Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi barazanar korar duk ministan da bai taɓuka abin kirki a ma'aikatarsa ba.
Tinubu na wannan maganar ne a lokacin taron bitar kwana uku da aka shirya wa ministoci mataimaka na musamman ga shugaban ƙasar, da manyan sakatarorin gwamnati, da sauran manyan jami'an gwamnati .
Shugaban ƙasar ya ce ya zaɓo manyan jami'an gwamnatin nasa ne domin su taimaka a ci nasarar tafiyar da gwamnati tare.
Ya ƙara da cewa “a ƙarshen wannan bita, za mu sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar fayyace ƙwazon aiki".
“Don haka ne ma muka ɓullo da sashen tantance ƙwazo, kuma a ƙarshen wannan bita za ku saka hannu kan yarjejeniyar fahimta tsakaninku (ministoci) da manyan sakatarorin gwamnati da kuma ni kaina", in ji Tinubu.
“Matuƙar ka yi ƙwazo, babu abin fargaba a ciki, idan kuwa ba ka yi komai ba, za mu duba, matuƙar babu abin da ka yi, za mu sauke ka, babu wanda zai iya rayuwa shi kaɗai".
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince Tinubu ya ciwo bashin dala biliyan 7.8
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100 a matsayin kuɗin da Shugaba Bola Tinubu zai ciyo bashi.
Shugaban ya rubuta wa Majalisar wasiƙa yana neman amincewarta game da ciyo bashin a tsarin rance na 2022 zuwa 2024 don kammala wasu ayyuka.
Kazalika, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya sanar da buƙatar Tinubu ta neman amincewa da mutanen da yake son naɗawa a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa.
Majalisar ta amince da naɗin kwamishinoni bakwai a zaman nata na yau Laraba.
Mun tsare shugaban NLC Joe Ajero ne don kare rayuwarsa - Ƴan sanda
Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Imo ta musanta rahotannin da ke zargin jami'anta da kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero a garin Owerri.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar a jihar Imo, ASP Okoye Henry, ta ce ta tafi da shi ne "domin tsare rayuwarsa".
Sai dai ƙungiyar ƙwadagon ta ce jami'an tsaro sun kama shugaban nata ne bayan ya isa jihar ta Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.
"Daga cikin abubuwan da Mista Ajaero ya je yi Imo akwai shirya babbar zanga-zanga da tsayar da aiki cak a filin jirgin sama, kuma a wajen yunƙurin yin hakan ne wasu ma'aikata suka nuna rashin amincewa kuma wani dandazon jama'a ya kai masa hari," in ji ASP Henry.
"Bayan mun samu labari, sai rundunar 'yan sandan Imo ta tura dakarunta kuma jagoran tawagar ya ɗauki shugaban na NLC zuwa hedikwatarta don tabbatar da kare rayuwarsa daga maharan."
Sanarwar ta ƙara da cewa "daga nan sai kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umarnin kai shi asibitin 'yan sanda don duba lafiyarsa...kuma aka ba shi cikakken tsaro don ci gaba da harkokinsa".
Sai dai kuma, rundunar ta jaddada cewa ya kamata a yi la'akari da hukuncin kotun ɗa'ar ma'aikata da ta hana NLC gudanar da zanga-zangar a ranar 27 ga watan Oktoba.