Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Subul-da-bakan Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
'Yan Najeriya sun shafe dare har zuwa wayewar garin wannan Larabar suna ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai ko subul-da-baka da ɗan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa.
A jiya Talata ne Bola Tinubu ya kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyyar suka halarta.
Sai dai a jawabinsa lokacin da ya hau dandamali ya yi wasu kalamai da wasu ke gani subul-da-baka ne.
Irin wadannan kalamai su ne wasu 'yan Najeriya suka rinka watsawa a shafukan sada zumunta, wasu na amfani da kalaman zolaye, wasu kuma na cewa wannan katoɓara alamomin gazawa ce.
Subul-da-bakan Tinubu
Kusan abu biyu ne suka ja hankalin ma'abota shafukan sada zumunta da kuma mutanen da suka bibbiya yadda gangamin ya kasance a garin Jos.
Akwai kuskure da ɗan takarar Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen kiran sunan jam’iyyarsu ta APC, inda aka jiyo ɗan takarar na ambato harufa biyu na babbar jam'iyyar adawa wato PDP, inda ya ce "PD..." amma daga bisani ya gyara ya ce "APC".
Wannan kuskure ko subul-da-baka da Tinubu ya yi ya ja hankali sosai, inda mutane suka yanko daidai wajen suna ta sake wallafawa da takfa muhawara a kai.
Wasu ma sun haɗe sunan suna cewa ko dai Najeriya ta yi sabuwar jam'iyya ce ta "PDAPC".
@SavvyRinu ya ce: Wace jam'iyya ce kuma PDAPC kuma?
@elonchorh ya ce: Mutumin da ba zai iya tuna sunan jam'iyyarsa ba, zai iya tuna kudurinsa kuwa, balantana idan aka zo kan batun alkauran zabe?
Wace jam'iyya ce kuma PDAPC?
Wani abu na biyu kuma da ya ja hankali shi ne lokacin da dan takarar zai ambaci sunan shugaban kasa domin yaba masa.
Bola Tinubu ya ce: "Buhari Buhari Buhari Buhari Buhari shegege Buhari".
Mutane sun rinka zolaye da tafka muhawara musamman a Tuwita da Facebook suna cewa garin neman gyara za a rasa ido.
End of Wasu labaran masu alaƙa da za a iya karantawa
"Tinubu ya tabbatar PDP ce mafita"
Da alama wannan subul-da-bakan na Tinubu ya yi wa jam’iyyar PDP dadi, saboda tuni ta wallafa a shafukanta tare da bayyana cewa Tinubu ya amince cewa su ne za su iya ceto Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar, babbar jam’iyyar ta adawa, ta ce Tinubu a zuciyarsa yana da yardar cewa PDP ce za ta iya ceto Najeriya ta hanyar magance duk wasu matsaloli da hada kan kasar.
Jami’in yada labaran jam’iyyar ta kasa, Honorabul Debo Olagunagba, a cikin sanarwar yana mai cewa Tinubu ya yi musu addua a Jos, kuma wannan manuniyace shi yasa har aka kai ga ya furta abin da ke cikin zuciyarsa.
PDP ta ce tana fatan ‘yan Najeriya za su fahimci hakan wajen zabi nagari domin ceto kasar daga kangin tarin matsalolin da ke neman durkusar da ita.
Sauran abubuwan da Tinubu ya faɗi
Duk da cewa Tinubu ya yi wasu kura-kurai a wajen yaƙin nema zaɓensa, akwai kuma batutuwa masu muhimmanci da ya taɓo, tare da alkawarta shawo kansu da zaran ya kasance mai nasara a zaɓen 2023.
Mista Bola Tinubu ya lissafo mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da karancin abubuwan more rayuwa da durkushewar masana'antu da rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Sannan ya yi alwashin magance su ta hanyar hada kwararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa.
Ya ce: "Mu a jam’iyyar APC da yardar Allah mun yi wa 'yan Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yunkuri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zukatan al'umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu. Za mu hada ayarin jarumai don ciyar da kasa gaba".
Kazalika, ɗan takarar shugaban kasar ya caccaki abokan hamayyarsa musamman ma na jam'iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora.
Haka zalika da dama cikin 'ya'yan jam'iyyar da suka yi jawai sun nuna suna da kwarin gwiwa APC za ta kai labari a zabe mai zuwa.
Amma Shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya shawarci 'yan jam'iyyar da kada su shagala, su bari mulki ya ruɗe su, su yi wa jam'iyya aiki idan suna so su ga alheri:
Ya ce: "Kasancewa a kan karagar mulki ba ya sa a dawwama a kan mulki. Ba zai hana faduwa ba idan ba mu dage mun yi abin da ya kamata mu yi da zai ma samu karbuwa a zukatan masu kada kuri'a ba.
Wannan ne ya sa nake jaddada cewa mu kasance masu himma. Mu hada kai ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare," in ji Abdullahi Adamu.