Matashi sabon jini da ya ƙwaci kujerar majalisar wakilai daga tsohon hannu

Wani matashin dan siyasa mai shekara talatin da uku ya samu nasara kan wani tsohon dan majalisa da ya shafe shekara goma sha shida yana wakiltar mazaɓar Goronyo da Gada ta jihar Sakoto a majalisar wakilai ta Najeriya.

Bashir Usman Gorau ɗan jam'iyyar PDP ya samu nasara ne kan abokan takararsa ciki har da Musa Sarkin Adar na jam'iyyar APC wanda ya daɗe a majalisar wakilai ta Najeriya.

Wannan nasarar ta bai wa mutane da dama mamaki musamman a lokacin da ake yi wa matasa kallon ba su iya ba a harkar siyasa.

Musa Sarkin Adar dai ɗan majalisar wakilai ne da aka fara zaɓa daga mazaɓar Goronyo da Gada a 2007, kuma ya sake yin nasara a zaɓen 2011 da kuma na 2015.

A zaɓen 2019, Musa Sarkin Adar ya sake cin zaɓe a karo na huɗu da gagarumin rinjaye a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Shi dai matashin ɗan majalisar na Goronyo/Gada ya shaida wa BBC cewa ko da yake shi sabon jini ne amma ba yau ya fara siyasa ba, don kuwa ya yi gwagwarmaya a matsayinsa na ɗalibin jami'a, kuma ya yi harkar siyasar makaranta.

Bashir Gorau dai na ɗaya daga cikin matasa da dama da suka hana wasu jiga-jigan 'yan majalisa komawa zauren majalisar wakilan bayan sun daɗe suna wakilci.

Baya ga siyasar makaranta, Bashir ya ce gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya naɗa shi kwamishinan matasa da wasanni, kuma ya yi namijin ƙoƙari a wannan muƙami.

"Abin da ya ba ni ƙwarin gwiwa shi ne irin shugabanci da na ga ake yi a ƙasashen duniya wanda yake janyo matasa da kuma tsofaffi su yi tafiya tare ta yadda matasan za su iya koyon tafiyar da mulki sannu a hankali," in ji matashin ɗan majalisar.

Ya ƙara da cewa abin da ya taimaka masa wajen cin nasara, shi ne kyakkyawar mu'amala da mutane.

Zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya ce idan ya fara aiki bayan rantsar da su a zangon majalisa ta goma, zai fi mayar da hankali ne kan ayyukan da suka shafi gina rayuwar matasa.

"Zan yi ƙoƙari da fafutukar ganin an raba ma'aikatar wasanni da ta matasa don kuwa wasanni aka fi mayar da hankali a kansu, maimakon ayyukan gina rayuwar matasa" in ji shi.

Sabon wakilin na mazaɓar Goronyo da Gada daga jihar Sakoto a Majalisar Dokoki ta Tarayya ya ƙara da cewa, ya ji ɗadi har ya kai shi ga sharɓar kuka ganin yadda mutane suka nuna masa soyayya da halarci duk da yake shi ba mai kuɗi ba ne.