Ƴan Hisbah sun kai samame gidan bikin ƴan luwaɗi a Kano

Asalin hoton, SANI MAIKATANGA
Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun kama wasu mutum 19 da ake zargin su da halartar wani bikin auren jinsi.
Hukumar ta kai samame ne wajen da ake auren a Kano bayan da aka tsegunta mata batun, kamar yadda mai magana da yawunta Lawal Ibrahim Fagge ya ce.
Ma'auratan dai wadanda ba a kai ga ɗaura auren nasu ba, sun tsere kuma a yanzu ƴan sanda na neman su, ya ƙara da cewa.
Kano jiha ce da mafi yawan al'ummarta Musulmai ne, kuma tana bin tsarin shari'ar Musulunci.
An haramta luwaɗi da maɗigo haramun ne a dukkan fannonin shari'un ƙasar.
Hukumar Hisbah ita ke kula da yanayin ɗabi'un mutane da kuma ɗaukar mataki a kan duk wanda ya taka dokar shari'ar Musulunci a Kano.
Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa ƴan sanda ba su yi nufin hukunta maza 15 da mata huɗun da aka kama su a wajen halartar bikin ba wanda aka yi ranar Lahadi.
A maimakon hakan, ya ce ana yi wa mutanen da aka kama din da suka haɗa da ƴan daudu da ƴan luwadi bitar sauya ɗabi'u, kuma an buƙaci iyayensu su je hukumar.
"Za mu bi dukkan hanyoyin da za a kawo sauyi kafin mu gurfanar da su a kotu. Da farko dai muna yi musu nasiha, sannan muna saka iyayensu cikin maganar tare da fatan za su sauya halayensu," a cewar mai magana da yawun Hisbah din.
Kotunan shari'ar Musulunci na Kano dai ba su taɓa yanke wa ƴan luwaɗi wani hukuncin ba.
Fagge ya ce a bara ma an taɓa samun wasu mutum 18 sun halarci auren jinsi amma daga baya aka sake su bayan da suka yin rantsuwa tare da sa hannu cewa ba za su sake ba.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun daɗe suna fafutukar ganin an bai wa masu auren jinsi damar watayawa, amma hakan na cin karo da adawa daga mafi yawan ƴan ƙasar waɗanda Musulmai ne da Kiristoci.











