Chelsea ta dauki Estevao Willian daga Palmeiras

Chelsea ta amince za ta dauki matashin ɗan wasa mai shekara 17, Estevao Willian daga Palmeiras kan kudi £29m.

Cikin kunshin kwantiragin za a kara wa matashin ɗan kwalllon Brazil kudi idan ya kara kwazo, ya kuma taka rawar da ake bukata.

Wannan wani karin ci gaba ne daga Chelsea, wadda ke kokarin sayen matasan ƴan kwallo, domin bunkasa ƙungiyar nan gaba.

Tuni ƙungiyar ta Stamford Bridge ta dauki matasan ƴan wasa da yawa daga Kudancin Amurka da suka hada da Andrey Santos da Deivid Washington da Angelo.

Cikinsu har da matashi mai shekara 17 ɗan kasar Ecuador, Kendry Paez, wanda zai koma Ingila da taka leda a 2025 daga Independiente del Valle.

Haka kuma Chelsea ta mallaki, Sam Jewell daga Brighton, wanda yana cikin matasan da ta farauto daga ƴan kwallon Kudancin Amurka.