'Nutsewa na haddasa mutuwar mutum 250,000 a kowace shekara'

wani yaro na wasa cikin ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun ba da shawarar tabbar da cewa yara na ƙarƙashin kulawar babba mai ƙwazo, lokacin da suke kusa da ruwa.
    • Marubuci, Onur Erem
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Nutsewa wata annoba ce a ɓoye mai yin kisan mummuƙe kuma ita ce ta uku kan gaba wajen haddasa mace-mace da za a iya kiyayewa a duniya.

"Mutane na tsammanin cewa a yayin da mutum ke nutsewa cikin ruwa, za a ji ƙarar ruwa kamar yadda ake nunawa a fina-finai, wanda ba haka ba ne, kwata-kwata ba a jin ƙarar nutsewa," in ji Kate Eardley ta Royal National Lifeboat Institution (RNLI) ta Burtaniya.

A duk shekara, kusan mutum 250,000 ne ke mutuwa sakamakon nutsewa a duniya, inda kusan 82,000 daga cikinsu ƴan kasa da shekaru 14 ne, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Wannan na nufin sama da mace-mace 650 na faruwa a kowace rana, wanda hakan ya sa hukumar ta WHO ta kira nutsewa da “annobar ɓoye mai kisan mummuƙe.”

Bayan mummunar sakamako da nutsewa ke haifarwa ga iyalai, tana kuma lalata tattalin arziki.

Mutuwar da aka yi da wuri da kuma munanan raunukan da wasu da suka tsira daga nutsewa na shafar ma’aikata kuma hukumar ta WHO ta kirga kudin rashin rashin ɗaukar mataki zai kai dalar Amurka tiriliyan hudu nan da shekarar 2050.

Saboda tsananin matsalar lamarin, Majalisar Dinkin Duniya a cikin shekarar 2021 ta ayyana cewa 25 ga Yuli a matsayin ranar kiyayewa daga nutsewar ruwa ta duniya na shekara-shekara, a wani yunƙuri na magance "batun lafiyar jama'a da aka yi watsi da su".

Amma yaya girman matsalar take, kuma mene ne za a iya yi don magance ta?

flourish map
Bayanan hoto, Ƙiyasin yara da ke mutuwa ta hanyar nutsewa a faɗin duniya

‘Kowane mutum zai iya nutsewa’

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Nutsewa ita ce abu na uku da ke haddasa mutuwar mutane ba da gangan ba a duniya, wanda ya kai kashi 7 cikin 100 na duk mace-macen da ke da nasaba da rauni, a cewar WHO.

Tana shafar yara da matasa daidai gwargwado, kuma tana cikin manyan dalilan mutuwar mutane da ke ƙasa da shekara 25 a kowane yanki na duniya.

Waɗanda nutswewa ta fi shafa su ne yara masu shekaru ɗaya zuwa huɗu, saboda idan suka faɗa cikin ruwa, ba za su iya fitowa ba.

"Kowa zai iya nutsewa," in ji Dr David Meddings, jami'in kula da fasaha na WHO na kiyayewa daga nutsewa.

“Tana faruwa ne cikin mintuna."

Ko da mutum ya tsira, nutsewa za ta iya haifar da raunuka masu canza rayuwa ciki har da illa ga ƙwaƙwalwa.

Fiye da kashi 90 cikin 100 na mace-macen nutsewa a duniya suna faruwa ne a cikin ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin samu, yayin da sama da kashi 60 cikin 100 kuma na faruwa a yankin yammacin yankin Pacific da kuma Kudu maso Gabashin Asiya, a cewar WHO.

Ƙasashe masu samun kuɗin shiga sosai suna da ingantaccen tsarin ilimi da kayan aiki don koya wa yara yadda ake yin iyo.

Duk da manyan bambance-bambance a tsakanin ƙasashe, gaba ɗayan adadin waɗanda suke mutuwa sakamakon nutsewa a duniya yana raguwa tsawon shekaru.

Dr Meddings ya ce ci gaban tattalin arziki da ingantacciyar fasaha da ingantattun ababen more rayuwa da ingantacciyar hanya da kuma ingantaccen tsari duk suna taimakawa wajen daƙile matsalar nutsewa.

'Rashin sani'

Gwamnatoci za su iya rage yawan nutsewa cikin sauƙi da zarar sun himmatu wajen tabbatar da hakan, a cewar Dr. David Meddings. Babban kalubalen, in ji shi, shi ne "rashin sani."

Kate Eardley daga Royal National Lifeboat Institution (RNLI) ta jaddada cewa shugabannin da yawa ba su san girman batun ba. "Sau da yawa, za mu shiga taro tare da jakadu ko wakilai waɗanda za su ce, 'Ba mu san ainihin dalilin da ya sa kuka zo nan ba; nutsewar ruwa ba wani batun da za a damu da shi ba ne,' "in ji ta.

"Amma bayan wani ɗan lokaci za su yi tambaya kan batun da kuma yadda za su iya shiga domin bayar da goyon bayansu.

Dr. Meddings ya yi imanin cewa gabatar da ranar wayar da kan jama'a kan wannan lamarin ya riga ya yi tasiri sosai. A Tanzaniya, alal misali, gwamnati ta aiwatar da sabbin dabarun rage nutsewa a ruwa nan da nan bayan sanar da ranar kiyayewa daga nutsewa a ruwa ta duniya ta farko.

Wannan yunƙuri ya kuma sa hukumar lafiya ta duniya WHO ta shirya rahoton matsayin duniya kan kiyayewa daga nutsewa a ruwa, wanda ake sa ran za a buga a ƙarshen shekara.

Yadda za a iya rage mace-mace daga nutsewa

Hoton ɗan yaro kusa da ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Faɗawon yara cikin ruwa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo nutsewar ruwa

Hanya daya da WHO ta ce za a iya rage yawan mace-macen nutsewa ita ce ta koyar da yara a makarantu dabarun yin iyo, kiyaye ruwa da dabarun ceto.

Yin hakan zai iya hana mutuwar mutum 238,000 da kuma 549,000 da ba za su samu rauni sosai ba nan da shekarar 2050, in ji hukumar.

Shirin cibiyar Ceton Ruwa ta Kasa kan tsira daga nutsewa a Afirka ta Kudu ta bai wa yara fiye da 900,000 darussan kiyaye nutsewa a bara.

Sau biyu, yaran da suka shiga cikin shirin sun ceto wasu yara daga nutsewa, in ji Andrew Ingram na NSRI.

Ya kamata a rika lura da yara sosai yayin da suke iyo ko suke kusa da ruwa kamar yadda idan aka bar su kadai, za su iya mutuwa cikin ‘yan mintoci kadan, in ji shi.

Amma iyaye masu aiki da ke zaune a yankunan karkara ba sa iya lura da ’ya’yansu duk rana.

Kuma a ƙasashe masu ƙaramin karfi da matsakaicin kudin shiga, nutsewar yaran na da alaka da rashin kulawar manya, in ji WHO.

Hukumar ta ce wata hanya ta rage mace-macen nutsewa ita ce ta samar da wuraren kulawa da yaran da ba su kai zuwa makaranta ba.

Hukumar ta kuma ce nan da shekarar 2050, wannan na iya hana kusan mutuwar mutum 536,000 daga nutsewa da kuma 444,000 wadanda ba za su samu rauni sosai ba.

Jhorna Begum da ɗanta Yasin

Asalin hoton, RNLI/Syed Naem

Bayanan hoto, Jhorna Begum da ɗanta Yasin

Tasirin matakin da mutum zai ɗauka

Hukumar ta WHO ta yi kiyasin cewa wasu ƙasashe suna asarar kusan kashi 3 cikin 100 na kuɗaden shiga na shekara-shekara kan mutuwar nutsewa.

Jimillar asarar tattalin arzikin na iya kai wa dalar Amurka tiriliyan hudu a duniya, in ji WHO.

Yadda za ka iya kare kanka a kusa da ruwa

...

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar agaji ta Royal Lifesaving Society ta Birtaniya ta shawarci mutane kada su kasance su kadai a kusa da ruwa, kuma su yi iyo kawai tare da abokai ko dangi, kuma a wurin da ke da mutum wanda zai iya ceto duk wanda ke cikin hatsarin nutsewa.

Yana kuma da mahimmanci a tabbatar da cewa yara na ƙarƙashin kulawar manya a kodayaushe a kusa da ruwa.

Kungiyar agajin ta kuma bayar da shawarar cewa idan mutane suka fada cikin ruwa ko kuma suka gaji yayin iyo, to su natsu su yi iyo a bayansu kafin su nemi taimako.

Har ila yau, ƙungiyar ta bayar da shawarar cewa mutane kada su yi nisa sosai daga gaɓar ruwan, su yi iyo a kusa da bakin gaɓa.