Southampton ta kunyata Man City a Kofin Carabao

Kwallon da Moussa Djenepo ya ci City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda Moussa Djenepo ya ci Manchester City ke nan

Kociyan Southampton Nathan Jones ya yi nasara mafi girma a dan takaitaccen aikinsa, inda ya kai kungiyar wasan kusa da karshe na cin Kofin EFL wato Carabao bayan doke, Manchester City da ake ganin za su yi nasara, 2-0.

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya ajiye manyan ‘yan wasansa, irin su Erling Haaland da Kevin de Bruyne, saboda kila karawar hamayya da za su yi a karshen makon nan da Manchester United a Old Trafford, amma duk da haka wasan da Southampton ta yi ya burge.

Tun a kashin farko na wasan ne aka yi ta ta kare inda Sekou Mara y afara daga ragar Manchester City bayan minti 23 da take leda, sai kuma kwallo ta biyu wadda bayan minti biyar da ta farko, Moussa Djenepo ya faki golan City Stefan Ortega ya fito, inda ya dankaro masa kwallo daga can nesa, ta kwana a raga.

Ganin wankin hula zai kai shi dare, kociyan City, Guardiola nan da nan bayan hutun rabin lokaci ya sako De Bruyne da Haaland, to amma ya makaro, domin Southampton sun tashi haikan suka tsare bayansu da niyyar lalle sai sun kai wasan kusa da karshe, inda za su hadu da Newcastle.

Manchester City sun je wasan ne a matsayin wadanda ake ganin za su yi nasara a karawar su kai wasan kusa da karshe, a kan Saints din wadanda ke fama a gasar Premier, to amma sai labari ya sha bamban, inda Zakarun na Premier suka girbi abin da suka shuka na rashin tabuka abin-a-zo-a-gani.

Duk da cewa Guardiola ya yi sauyi a jerin ‘yan wasansa to amma duk da haka akwai kwararru irin su Kyle Walker da Aymeric Laporte da Jack Grealish da Ilkay Gundogan da Joao Cancelo da Phil Foden da kuma Julian Alvarez da ya dauki Kofin Duniya da Argentina.

Duk da cewa Kofin na Carabao ba lalle ba ne ya damu Guardiola ko City sosai to amma dai rashin nasarar abu ne da zai bat awa kociyan da kungiyar rai matuka.