Barcelona ta naɗa Flick a matakin sabon kociyanta

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta naɗa tsohon kociyan Bayern Munich, Hansi Flick a matakin sabon wanda zai horar da ita kan yarjejeniyar kaka biyu.
Flick, wanda tawagar Jamus ta sallama cikin Satumbar 2023, ya karbi aikin daga Xavi, wanda aka kora a makon jiya.
Tagawar Jamus ta bai wa Flick aiki, sakamakon rawar da ya taka a Bayern Munich da ɗaukar kofi uku a 2020, wato Bundesliga da German Cup da kuma Champions League.
Ɗan ƙwallon Barcelona, Robert Lewandowski, mai shekara 35 ya taka leda karkashin Flick tsawon kaka biyu a Allianz Arena.
Bayan da Barcelona ta sallami Xavi ya sanar da cewar ''Duk kociyan da ya karɓi aikin horar da ƙungiyar Camp Nou zai sha wuya, domin tana da wuyar sha'ani.''
Xavi ya ja ragamar Barcelona ta lashe La Liga a kakar farko da Spanish Super Cup a bara, sai dai a bana ta yi ta biyu a teburin La Liga da Real Madrid ta lashe da tazarar maki 10 tsakani.
Barcelona ta kori Xavi ne, bayan kalaman da ya yi kan matsin tattalin arziki da ƙungiyar ke fuskanta.
A wani jawabi da Barcelona ta fitar ranar Laraba ta ce ''Ta zaɓi kociyan da ya san halin da ƙungiyarsa ke ciki, wanda zai iya ɗaukar matsi da fuskantar ƙalubale da hakan ya sa ya samu nasara da yawa a fannin horar da tamaula.''











