‘Gazawar gwamnatin Buhari ce ta sa aka kasa karbo fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna’

Asalin hoton, OTHERS
Wani mai shiga tsakani don ganin an kubutar da fasinjojin jirgin kasan da aka sace daga Abuja zuwa Kaduna ya ce gazawar gwamnatin kasar ce ta sa aka kasa ceto mutanen.
Tukur Mamu ya shaida wa BBC Hausa hakan jim kadan bayan ya shige gaba an kubutar da karin mutum bakwai da ake garkuwa da su.
Ya ce shi kadai ya tattauna da ‘yan bindiga har aka samu nasarar karbo mutane bakwai daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka sace a jirgin kasan na Abuja zuwa Kaduna.
Dama dai, a cewarsa, shi ne ya jagoranci tattaunawa ta baya, inda aka yi nasarar karbo mutum 11.
“Idan wani a matsayinsa na dan kasa zai iya yin haka shi kadai, to idan gwamnati ta saukar da kanta a cikin kwana daya zuwa uku za a iya samun abin da ya fi haka, watakila ma a kubutar da su baki daya,” in ji Tukur Mamu.
Sai dai ya ce da alama lamarin ya fi karfin gwamnati.
Ya kara da cewa tun bayan kwashe mutanen an kasa samun daidaito tsakanin gwamnati da maharan.
Ya ce maharan sun gabatar da bukatu wadanda gwamnati ba ta amince da su ba.
Sai dai ya ce a ganinsa tattaunawa ce kadai hanyar da za a bi wurin ceto mutanen da suke rike a hannun ‘yan bindigar.
A ranar Litinin 28 ga watan Maris ne ƴan bindiga suka kai harin bom a jirgin ƙasa da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja suka sace mutane da dama tare kashe mutum takwas.
A baya dai ‘yan bindigar sun sako wasu daga cikin mutanen da suka sace, sai dai har yanzu akwai saura da dama a hannunsu.
Wadanda aka sako din a wannan karo sun hada da wani dan asalin kasar Pakistan, sai kuma sauran ‘yan Najeriya, ciki har da Sadik Ango Abdullahi, dan shugaban kungiyar dattawan arewacin Najeriya.










