Sukar da Tinubu ke sha kan yunƙurin tura sojoji Nijar

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na shan suka a gida game da barazanar da ya yi ta amfani da ƙarfin soja don kawo ƙarshen juyin mulkin da sojoji suka yi a maƙwabciyarsu Nijar.
'Yan majalisar ƙasar sun tafka muhawara a kan batun ranar Asabar, inda suka ƙi goyon bayan matakin duk da cewa jam'iyyar APC ce mai mulki ke jagorancin majalisar.
Lamarin ya fi ƙamari musamman ga 'yan majalisar da suka fito daga jihohin da ke da iyaka da Nijar mai tsawon kilomita 1,500, haka nan kuma 'yan ƙasa da dama sun yi tir da yunƙurin.
Ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma ce ta saka wa'adin ranar Lahadi da ta wuce ga sojojin da su sauka daga mulki ko kuma su fuskanci ƙarfin soja.
Ana kallon matakin a matsayin na Tinubu kaɗai saboda shi ne shugaban Ecowas, kuma Najeriya ce babbar mamba a cikinta.
Duk da cewa sojojin sun yi buris da wa'adin, Ecowas ba ta mayar da martani ba ta hanyar tura dakaru. Hakan ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya da dama, waɗanda suka fi son a bi hanyoyin difilomasiyya.
Da ma can wasu na ganin wa'adin kamar ba mai yiwuwa ba ne ganin cewa sai Najeriya da sauran ƙasashen Ecowas sun nemi amincewar majalisunsu kafin tura dakarun Nijar.
Kazalika, wasu sun yi mamakin yadda Najeriya ta katse wa Nijar wutar lantarki bisa umarnin Shugaba Tinubu, inda aka jefa babban birnin Yamai da wasu jihohi cikin duhu.
Masu sukar gwamnati na cewa hakan ya saɓa da yarjejeniyar da aka ƙulla wadda ta bai wa Najeriya damar gina madatsar ruwa a Kogin Neja, duk da cewa magoya bayan Tinubu kan ce an ɗauki matakin ne saboda a matsa wa sojoji su sauka daga mulki.
Najeriya da Nijar na da alaƙa mai ƙarfi ta fuskar tattalin arziki da al'adu, kuma duk wani yaƙi da za a kai wa Nijar zai shafi arewacin Najeriya, yankin da da ma tuni yake fama da matsalolin tsaro.
Wasu ƙungiyoyi na addini da fitattun 'yan Najeriya da dama sun gargaɗi Tinubu game da "gaggawa wajen shiga rikici da maƙwabta saboda siyasar duniya".

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sojojin mulki a Burkina Faso da Mali sun ci alwashin taimaak wa Nijar idan Ecowas ta yi yunƙurin amfanin da ƙarfi, abin da zai iya ta'azzara rikicin zuwa na yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya.
Yanzu hankali zai koma kan Tinubu wanda ya fi ɗaga murya wajen yin tir da juyin mulki a Afirka ta Yamma, kuma ya faɗa a watan da ya gabata cewa ba zai yiwu Ecowas ta zauna "kamar karen da ba shi da haƙora ba".
"Wajibi ne mu kare dimokuraɗiyya. Babu shugabanci ko 'yanci ko doka da oda idan babu dimokuraɗiyya. Ba za mu yarda da juyin mulki akai-akai ba a Afirka ta Yamma," in ji Tinubu jim kaɗan bayan ya zama shugaban Ecowas.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa shugaban ƙasa bai isa ya tura sojoji zuwa wata ƙasa ba ba tare da amincewar majalisa ba - ma'ana majalisar dokoki da ta dattijai.
Babu tabbas ko shugaban zai samu goyon bayan 'yan majalisar nan gaba.
"Ecowas ta yi ɓarin zance, shugaban Najeriya ma ya yi ɓarin zance," a cewar Farfesa Khalifa Dikwa, malami a Jami'ar Maiduguri kuma mamba a ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya.
Cikin wani sanarwa da suka fitar bayan tattaunawar sirri, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya nemi Ecowas ta ci gaba da "lalubo hanyoyin sasanta rikicin cikin gaggawa".
Babu mamaki aƙidar Tinubu ta yaƙi da juyin mulki na da alaƙa d abin da ya faru da shi. Bai wuce shekara ɗaya ba a matsayin ɗan majalisa a 1990 lokacin da aka soke zaɓukan, aka rusa majalisar sannan Janar Sani Abacha ya ƙwace mulki.
Ya shiga ƙungiyoyin fafutikar dawo da mulkin farar hula, abin da ya haɗa shi rigima da sojoji har suka sa ya tafi gudun hijira. Ya koma Najeriya a 1998 bayan mutuwar Sani Abacha, ɗaya daga cikin shugabannin Najeriya mafiya rashin imani.
Sai dai wasu 'yan Najeriya da dama na ganin Ecowas ta yi gaggawar ba da wa'adi ga sojojin Nijar ɗin, kuma Shugaba Tinubu bai yi tunanin da yawa ba game da tasirin da yaƙin zai yi idan aka yi amfani da ƙarfi.
"Nijar ɓangare ne na arewacin Najeriya har zuwa lokacin da aka yi Taron Berlin [na 1884 zuwa 1885 lokacin da ƙasashen Yamma suka tsaga iyakokin ƙasashen Afirka]. Kana tunanin Arewa za ta yaƙi kanta da kanta ne?" in ji Farfesa Dikwa.

Asalin hoton, Getty Images
Saɓanin wanda ya gada Muhammadu Buhari, Shugaba Tinubu ba shi da masaniya kan harkokin soja, haka ma mai ba shi shawara kan tsaro, Nuhu Robadu, wanda ɗan siyasa ne.
Hafsoshin tsaro na Ecowas sun ce ƙarfin soja "shi ne mataki na ƙarshe" da za su ɗauka bayan zaman da suka yi a makon da ya gabata.
Shugabannin Ecowas za su sake yin zama a Abuja ranar Alhamis don yanke shawara kan mataki na gaba.
Duk da cewa wasu ƙasashen Afirka ta Yamma sun yi alƙawarin shiga yaƙin, abu ne mawuyaci su iya yin hakan ba tare da Najeriya ba, idan majalisa ba ta amince da buƙatar Tinubu ba.
Tinubu na sanye da hula biyu ne - ta Ecowas da kuma ta shugabancin Najeriya. Ɗaya ta sharɗanta ɗaukar matakai don kare dimokuraɗiyya da kuma Afirka ta Yamma, amma za ta iya jawo abubuwa marasa daɗi ga ɗayar.











