Da gaske an samu jakunkuna cike da kuɗi a Gabon?

Gabon Coup

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Bayan hamɓarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon, an riƙa yaɗa bidiyo a intanet da iƙirarin nuna tsoffin jami'an gwamnatin da aka kama da akwatuna cike da kuɗi.

Sai dai BBC ta tabbatar da cewa aƙalla ɗaya daga cikin bidiyon, na ƙarya ne.

Bidiyon dai yana nuna yadda kama tsohon shugaban majalisar dokokin Gabon, Guy Nzouba-Ndama a 2022.

A bidiyon, ana iya ganin Mista Nzouba-Ndama a tsakiyar cincirindon mutane a bayan wata babbar mota, lokacin da suke ɓalle jakunkunan guda biyu, kuma aka gan su cike da takardun kuɗin saifa.

Lamarin dai ya faru ne a kan iyakar ƙasar da Kongo.

Nzouba-Ndama, wanda shi ne shugaban jam'iyyar adawa ta LD, daga bisani an yi masa ɗaurin talala, a cewar rahotannin da suka fito a lokacin.

Bayanin da aka wallafa a shafukan sada zumunta cikin kuskure ya yi iƙirarin cewa an ɗauki bidiyon ne ranar Laraba 30 ga watan Agustan 2023.

Akwai ƙarin bidiyo da masu amfani da shafukan sada zumunta ke iƙirarin cewa daga Gabon su ma suka fito, sai dai BBC ba ta iya tabbatar da hakan ba.

Biyu a cikinsu sun nuna mutane da dama a wani ɗaki sun barbaza akwatunan da aka zuge bakinsu cike da kuɗaɗe.

A wani lokaci cikin ɗaya bidiyon, daga gefen dama, kyamara ta nuna wani sashe na jikin wani mutum sanye da kakin sojoji mai kama da na launin wanda dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa na Gabon, rundunar da ta yi wa Ali Bongo juyin mulki.

Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi iƙirarin cewa an ɗauki bidiyon ne a gidan ɗan Ali Bongo, yayin da wasu ke iƙirarin cewa gidan wani dangin Shugaba Bongo ne.

Ɗan Ali Bongo, Nouredin Bongo Valentin da shugaban ma'aikatansa, Chislain Ngoulou na cikin waɗanda sojoji masu juyin mulki ke tsare da su a ƙasar.