Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani game da ƴaƴan shugaban Hamas da Isra'ila ta kashe a Gaza
- Marubuci, Adnan El-Bursh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
An kashe ƴaƴa uku na jagoran siyasar Hamas, Ismail Haniyeh, a wani hari da Isra'ila ta kai ta sama a Zirin Gaza ranar 10 ga watan Afrilu kafin sabuwar tattaunawa a Alƙahira game da tsagaita wuta a zirin.
Yaran uku - Hazem da Amir da Muhammad, waɗanda aka kashe tare da ƙananan yaransu huɗu - suna cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa ziyara gidan ƴan uwansu a sansanin ƴan gudun hijira na al-Shati da ke yammacin Gaza bayan kammala azumin Ramadan.
Jikokin Isma'il Haniyeh - mata uku da yaro ɗaya - Hamas ta bayyana sunayensu da Mona da Amal da Khalid da Razan.
Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe dakarun Hamas uku a tsakiyar Zirin Gaza, inda suka ƙara da cewa su ne ƴaƴan Haniyeh kuma mambobi a rundunar Hamas.
Mista Haniyeh ya ce ya samu labarin yayin da yake ziyartar Falasɗinawa da suka ji rauni waɗanda aka kai su Doha, babban birnin Qatar domin samun kulawa inda jagoran Hamas ke zama.
Daga baya ya ce mace-macen ba za su shafi buƙatun ƙungiyar tawayen ba a tattaunawar sulhu da ake yi.
Ya ƙara da cewa an kashe mutum 60 daga danginsa tun da Isra'ila ta soma yaƙi da Hamas.
Daga majiyoyin Hamas, ana ganin Haniyeh na da ƴaƴa maza 13. Wasu a cikinsu suna zaune ne a Doha babban birnin Qatar.
Ko ƴaƴan Haniyeh na da hannu a ayyukan soji?
Duka shaidun da aka samu sun nuna cewa babu ƴaƴan Haniyeh da ke da hannu kai tsaye da ayyukan sojoji.
Yayin da wasu a cikinsu suka samu horo a sansanonin rundunar Izz al-Din al-Qassam (ɓangaren sojoji na Hamas), ba su da hannu a ayyukan sojoji ko riƙe manyan muƙamai a cikin ƙungiyoyin.
Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Alhamis, Mista Haniyeh ya musanta cewa ƴaƴansa mayaƙan Hamas ne.
A cewar Yasser Abu Hain, wani masanin siyasa da ƙwararre kan harkokin Hamas da ke Gaza, yaran ba za su saki jiki su shiga jama'a ba idan a ce suna da hannu a ayyukan soji.
A maimakon haka, za su samu wasu tsari ne na ɓoye kan su da fita kamar yadda jagororin ƙungiyar suke, ta hanyar amfani da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa ko ɓoye inda suke.
Yana da muhimmanci a sani cewa suna tare da ƙananan ƴaƴansu a lokacin ziyarar zuwa gidan ƴan uwa a motar farar hula domin bikin sallah ƙarama, bayan ƙarshen Ramadan.
Kisan ƴaƴan Ismail Haniyeh da jikokinsa shaida ce cewa ruɗewar Isra'ila da gazawa wajen cimma ƙudurorin sojojin, in ji Mista Abu Hain.
Wataƙila Isra'ila na ƙoƙarin kai hari kan wuraren da ba su da muhimmanci saboda ba su samu cimma burinsu ba kamar kai hari kan manyan jagororin Hamas ko sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.
Harin wataƙila na iya zama wani yunƙuri na mayar da martabar rundunar Isra'ila bayan da rundunar al-Qassam ta ce ta kashe sojojin Isra'ila da dama a samamen baya-bayan nan a garin Zana da ke gabashin Khan Younis a kudancin Gaza.
Kisan gilla na buƙatar ƙoƙari na gaske da haƙiƙanin bayanan sirri da kuma tattara bayanan wanda ba shi da muhimmanci a harin da aka kai ranar Laraba kan wata motar farar hula, in ji Mista Abu Hain.
Isra'ila na ganin duka jagororin Hamas, har da Mista Haniyeh, a matsayin "ƴan ta'adda’ kuma ana tunanin suna da hannu a kisan mataimaki Saleh al-Arouri a Beirut a watan Janairu.
Iyalin na fuskantar matsin lamba
Rndunar sojin Isra'ila a baya ta yi amfani da farfaganda da nufin gurgunta ƙwarin gwiwar Isma'il Haniyeh da sauran jagororin Hamas da ke zaune a wajen yankunan Falasɗinawa.
Jiragen Isra'ila a baya sun jefa takardu masu yawa a zirin Gaza ɗauke da farfagandar adawa da Hamas, inda aka faɗa wa Falasɗinawa cewa "jagororinsu na rayuwar ƙasaita a otal-otal masu tsada yayin da suke ƙyale ku ku mutu a Gaza".
An kuma yi amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa bayanan da ke nuna adawa ga Hamas.
A makon da ya gabata, ƴan sandan Isra'ila sun kama ƴar uwar Ismail Haniyeh a garin Tel Sheva da ke yankin Negev a kudancin Isra'ila.
Yayin samame a gidanta, ƴan sanda sun ce sun gano shaida da ta alaƙanta ta ga "laifukan da ke illa ga ƙasar Isra'ila."
A cewar bayanan ƴan sanda, Sabah Abdul Salam Haniyeh, mai shekara 57, yana tsare a Tel Sheva kuma hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet na gudanar da bincike a kansa.
Abdulsalam Al-Bakr, babban ɗan Ismail Haniyeh, yana riƙe da manyan muƙamai a siysar Falasɗinu: mamba ne a majalisar ƙolin Falasɗinu kan matasa da wasanni sannan kuma mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Falasɗinu, Jibril Rajoub.
Ta matsayinsa, ya yi ƙoƙarin ya cike matsayin da ke tsakanin manyan ɓangarorin da ke gaba da juna a siyasar Falasɗinu: Fatah da Hamas.
Yana ganin harkar wasa za ta ba da gudummawa ga abin da yake yawan kira haɗin kan ƙasa musamman a tsakanin Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Sai dai, zuwansa wurin wasa tsakanin Qatar da Iran a gasar cin kofin Asiya cikin Fabarairun bana, ya fusata mutane da sa mamaki a tsakanin mazauna Gaza da masu fafutuka a shafukan sada zumunta.
Mutane da dama suna ganin hakan bai kamata ba a yaƙin da ake.
Kafar yaɗa labaran Isra'ila musamman wadda ke da alaƙa da dakarun IDF sun nemi su yi amfani da hoton ta hanyar yaɗa shi a shafukan sada zumunta a wani ɓangare na ƙoƙarinsu na lalata sunan tafiyar da kuma ofishinta na siyasa.
Mista Hanaiyeh ya karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar a 2017 inda yake tafiye-tafiye tsakanin Turkiyya da Qatar da kaucewa takunkumin tafiye-tafiye da Isra'ila ta ƙaƙaba a Zirin Gaza.
Ya jagoranci tattaunawar sulhu a baya-bayan nan kuma a baya-bayan nan ya je Iran da Rasha.