Ko Hitler na da alaƙa da Yahudawa?

    • Marubuci, Tiffany Wertheimer
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wani bincike da aka yi game da ƙwayar halittar Adolf Hitler ya fito da wasu muhimman bayanai kan tsohon mayaƙin da kuma yanayin lalurorin da ya yi fama da su a lokacin da yake raye.

Masana kimiyya da suka gudanar da binciken sun gano tare da watsi da raɗe-raɗin da aka daɗe ana yaɗawa cewa Hitler yana da alaƙa da Yahudawa, sannan binciken ya gano batun wata cuta da ke al'aura girma kamar yadda masana suka gano daga jini da aka gani a wani kyallen kujerar ɗakin ƙarƙashin ƙasa da yake kansa a ciki.

An daɗe ana yaɗa cewa al'aurarsa ƙarama ce, sannan ƴaƴan marainansa ɗaya ne, sannan binciken ya gano cewa yana da cututtuka irin su cutar damuwa da rashin son shiga mutane.

Wannan ya sa ake tambayar shin mene ne amfanin binciken tun a farko? shin akwai wani amfani da ya yi?

"Na shiga damu kan abubuwan da sakamakon binciken ya nuna," in ji Farfesa Turi King.

Masaniyar ta ƙwayoyin halitta ta shaida wa BBC cewa shekarun baya ne aka buƙaci ta shiga cikin masu gudanar da binciken, inda ta ce tun farko ta san akwai ƙalubale babba "kan gudanar da bincike kan mutum kamar Hitler."

Sai dai ta ce ta san cewa idan ma ba su yi ba, dole nan gaba wasu za su gudanar da binciken, amma ko banza, idan ta shiga ciki, za ta tsaya kai da fata domin tabbatar da cewa an yi amfani da ilimi kuma an bi ƙa'ida.

Ba yau Farfesa King ta fara shiga cikin masu gudanar da bincike masu ɗaukar hankali, domin ita ce kan gaba wajen bincike gawar Sarki Richard III bayan an gano gawarsa a ƙarƙashin garejin mota a birnin Leicester a 2012.

Kyallen, wanda yake da shekara 80 a duniya daga cikin tufafin Hitler ana samo a ƙarƙashin ƙasa da ya kashe kansa aka samo lokacin da sojojin haɗin gwiwa suka far masa a ƙarshen Yaƙin Duniya II.

A lokacin da yake bincika ɗakin na ƙarƙashin ƙasa, Kanal Roswell P Rosengren na sojin Amurka, sai ya ɗauko kyallen, wanda yanzu ke ajiye a gidan adana tarihi na Gettysburg Museum of History da ke Amurka.

Masana sun ce idan lallai jinin na Hitler ne, to lallai sakamakon na ɗauke da darussa masu yawan gaske.

Wannan binciken karon farko da aka nazarci ƙwayoyin halittar Hitler, kuma binciken wanda zuwa yanzu aka yi shekara huɗu ana yi, zai taimaka wajen fahimtar wane ne Hitler.

Amma dai abin da ya zama tabbas shi ne, Hitler ba shi da jiɓi da Yahudawa, in ji masanan.

Wani binciken kuma mai muhimmanci shi ne, yana ɗauke da cutar Kallmann da ke hana namiji cika a matsayin ɗa namiji da hana al'aura girma, kamar yadda aka daɗe ayan yaɗawa a tarihi.

Masana tarihi sun daɗe suna nazarin me ya sa Hitler ya mayar da hankalinsa kacokam kan siyasa, "ba tare da mayar da hankali kan jin daɗin rayuwa ba," wanda masana suka ce wataƙila wannan binciken ya bayar da amsa.

Waɗannan sakamakon na cikin abubuwan da masana suka ce suna da matuƙar amfani, kamar yadda Farfesa King ta ce, "an samu haɗin gwiwa tsakanin tarihi da ƙwayoyin halitta."

Wani binciken da ya ɗauki hankali shi ne batun shin Hitler yana da wata cutar damuwa?

Masanan sun ce lallai idan aka duba yanayin sakamakon binciken, sungano cewa Hitler yana da cutar damuwa da ware kai, duk da cewa wasu masanan sun ce akwai ƙarin gishiri a binciken.

Farfesa Denise Syndercombe Court a Jami'ar Kings College London, ya ce masu binciken sun "ƙara gishiri a tunaninsu," in ji Farfesa Court, wadda ita ma ta taɓa nazarin ƙwayar halittar Hitler a 2018 a zantawarsa da BBC.

Ta ce ba zai yiwu a a iya tasakance abubuwan da ake faɗa ba saboda abin da ta bayyana da "rashin cikakken bayani."

Haka kuma wasu sun soki sunan da aka ba shirin tarihin na Hitler, musamman zango na biyun wanda aka kira da Blueprint of a Dictator, wato tsarin mai kama karya.

Farfesa King da a ita ce ba za ta zaɓi wannan sunan ba, kuma Farfesa Thomas Weber masanin tarihin da ya fito a shirin ya ce ta yi mamakin sunan da aka ba shirin.

Ya ce mutane masu matsaloli irin na damuwa da rashin son mutane za su ji wani iri idan suka kalla shirin.

Sai dai tashar Channel 4 ta kara shirin nata da sunansa, inda hukumomin tashar suka ce "DNA ai ƙwayar halitta ce.

Kuma aikin tashar ita ce tsare shirye-shirye da za su kai ga mutane masu yawan gaske, musamman wajen gwama binciken masana da tarihi.

Haka kuma akwai tambayoyi da dama game da amfani da dokokin da aka bi wajen binciken da ma shirya shirin.

Shin ya dace a gudanar da bincike kan ƙwayoyin halittar Hitler duk da ba a samu amincewarsa ba ko na wani na kusa da shi?

Sannan kuma yaya batun kasancewarsa kan gaba wajen kisan kiyashi mafi girma a tarihin? shin duk da haka ya cancanci haƙƙin mallaka da sirri?

Masanin tariri Subhadra Das ya ce, "haka masanan kimiyya suke yi. An nazarci ƙwayoyin halittar ɗaruruwan mutane, yadda ake kallon sakamakon ne matsalar."

Kuma game ko ya dace a nazarci ƙwayar halittarsa, "yanzu Hitler ya yi kusan shekara 80 da rasuwa. Ba shi da ƴaƴa, kuma ba shi da wasu sanannun ƴanuwa. Ya jefa mutane da dama cikin wahala. Wannan ya sa dole a shiga tsaka mai wuya kan ƙoƙarin yi masa adalci.

Sannan kuma ɗakuna gwaje-gwaje da dama a turai sun ƙi amincewa su shiga cikin binciken, sai dai wani wajen binciken na Amurka ne ya shige gaba.

Amma waɗanda suka tsare shirin sun shaida wa BBC cewa an bi dukkan ƙa'idoji wajen gudanar da shirin.

Don haka shin tun farko ma ya dace a gudanar da bincike? BBC ta zanta da masanan kimiyya da masana tarihi, inda ta samu amsoshi mabambanta.

Waɗanda suke da hannu a shirin sun bayyana gamsuwarsu da shirin, inda suka ce shirin ya taimaka wajen ƙara fahimtar Hitler.

"Ya kamata mu yi duk mai yiwuwa wajen fahimtar abubuwan da suka faru a baya," in ji Farfesa Weber.

"Ya kamata mu faɗa wa kanmu gaskiya, dama Hitler sanannen mutum ne. Ba yanzu ba ne muka fito da maganar. Dama can mutane suna raɗe-raɗin yana da wasu cututttuka."

Amma ba dukkan masana tarihi ba ne suka amince da wannan.

"Ina tunanin ba wannan hanyar ta kamata a bi ba wajen nuna abubuwan da suka Hitler ya aikata abubuwan da ya aikata," in ji mataimakin farfesa Iva Vukusic a Jami'ar Utrecht.

A nata ɓangaren, masaniyar tarihi a cibiyar tarihi ta NIOD a Amsterdam, Anne van Mourik ta ce suk da cewa akwai abubuwan ban sha'awa a binciken, akwai wasu abubuwan lura da dama a ciki.

A yanzu dai da aka kammala bincike, kuma ake ci gaba da nazarin sakamakon, nan gaba kaɗan za a fitar da cikakken sakamakon.

Farfesa Weber ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan wajen amfani da sakamakon bincike, amma ya ce yana da yaƙinin sakamakon zai taimaka.

Dr Kay ya ce yana kyau kowa ya yi amfani da binciken kimiyya, amma a riƙa taka-tsantsan wajen amfani da sakamakon, ciki har da kafofin sadarwa.