Yadda jama'a ke murnar ganin sabon Fafaroma a dandalin St. Peter's

Lokacin karatu: Minti 2

Dubban mutane ne suka cika a Dandalin St. Peter da ke Birnin Vatican domin nuna farin ciki da kuma shaida wannan babban tarihi.

Tun daga lokacin da farin hayaƙi ya fito daga bututun Sistine Chapel, har zuwa sanarwar daga baranda na Basilica St. Peter, ga wasu hotunan da ke nuna yadda mutane ke nuna farin cikinsu da kuma yadda suke ji daga wajen taron.

Mutane ɗage da tutocin Amurka cikin taron jama'a a dandalin St. Peter

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Robert Prevost, wanda za a fi sani da Leo XIV, shi ne ɗan asalin Amurka na farko da zai zama Fafaroma. Ana iya ganin mutane suna ɗaga tutocin Amurka cikin taron jama'a.
Wata mai hidimar majami'a ta nuna bayyana farincikinta ta hanyar ɗaga hannunta a sama bayan farin hayaƙi ya tashi daga bututun Sistine Chapel – alamar da ke nuna cewa manyan limamai sun zaɓi sabon Fafaroma.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An bayyana da sabon Fafaroman ne bayan taron zaɓen da aka yi a sirrance da ya ɗauki zama uku a cikin sa'o'i 24.
Wani mutum cikin taron yana zubar da hawaye tare da rufe bakinsa da hannu, yana nuna farin ciki sakamakon zaɓen sabon Fafaroma.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yawan mutane da ke nufar Dandalin St. Peter ya ƙaru sosai bayan farin hayaƙi ya fita daga bututun Sistine Chapel, alamar cewa an yanke shawara.
Hoton jama'a a Dandalin St.Peter.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sama da mutum 40,000 ne suka halarta Dandalin St. Peter in ji 'yan sanda.
Mata da ke yi wa majami'a hidima suna dariya tare da hawaye duk a cikin murnar bayyanar sabon Fafaroma.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mata da ke yi wa majami'a hidima suna dariya tare da hawaye duk a cikin murnar bayyanar sabon Fafaroma.
Mata masu yi wa majami'a hididma suna sauraron jawabin sabon Fafaroma na Farko ga taron jama'a a dandalin St. Peters

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Yayin da sabon Fafaroma yake gabatar da jawabinsa na farko ga taron jama'a — an ga mata masu yi wa majami'a hididma suna sauraro tare da yin addu'a.
Taron jama’a na sauraron jawabin sabon zaɓaɓɓen Fafaroma Leo XIV, Robert Prevost

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Ana ɗaukar Fafaroma Leo XIV a matsayin ɗaya daga cikin manyan limaman Latin Amurka, saboda shekaru da dama da ya shafe yana aiki a ƙasar Peru, kafin daga bisani Archbishof a can.