Wane ne Moussa Tchangari, mutumin da ake gangami a kansa a Nijar?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar 3 ga watan Disamban 2024 ne gwamnatin mulkin sojin jamhuriyar Nijar ta kama ɗan gwagwarmaya, ɗanjarida kuma sakatare janar na ƙungiyar Alternative Espaces Citoyens.

Wasu ƴansandan farin kaya ne dai suka yi awon gaba da ɗan gwagwarmayar daga gidansa da ke birnin Yamai.

Kamun ya faru ne shekara ɗaya bayan juyin mulkin da gwamnatin soji ta Abdurrahmane Tchiani ta yi wa gwamnatin farar hula ta Mohamad Bazoum.

Mousa Tchangari na ɗaya daga cikin mutane fiye da 50 da aka kama a ƙasar tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 2023.

Wane laifi Tchangari ya yi?

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayan kamun da aka yi masa Moussa Tchangari ya shafe aƙalla wata ɗaya a hannun jami'an tsaro masu yaƙi da ta'addanci sai aka kai shi zuwa gidan kaso na garin Filingue mai nisan kimanin kilomita 180 daga Yamai, babban birnin jamhuriyar.

An dai tuhumi ɗan gwagwarmayar da laifin "haɗa kai da ƴan ta'adda", da yi wa "bayanan sirri na ƙasa zagon ƙasa" da "bai wa abokan adawar ƙasar bayananta na sirri."

Tuhume-tuhumen sun biyo bayan irin sukar da Tchangari yake yi wa gwamnatin musamman abin da ya shafi shirin komawar ƙasar kan turbar dimokraɗiyya da cigaba da kuma matsalar tsaro a yankin Sahel.

Moussa Tchangari ɗan gwagwarmaya

..

Asalin hoton, Getty Images

Mousa Tchangari ya kwashe shekaru fiye da 30 yana gwagwarmayar neman ƴancin ɗan'adam da yaƙi da rashawa da cin hanci da kuma ganin an samar da shugabanci mai nagarta.

A 2015 ma lokacin mulkin Mohammadu Issoufou an kama Tchangari bisa sukar gwamnatin kan yadda take tafiyar da al'amuranta dangane da sha'anin yaƙi da Boko Haram da irin illar da ta'addanci ke yi ga fararen hula ƴan ƙasar.

Moussa Tchangari yana koyar da wani fanni kan nazari da sanin ƴancin ɗan'adam a Kwalejin Horar da Ƴansanda ta Niamey da ke jamhuriyar ta Nijar.

Ɗan gwagwarmayar ya kasance sananne a yankin Sahel a fannin ƴancin ɗan'adam da mulkin dimokraɗiyya inda yake gabatar da ƙasidu a wuraren taruka daban-daban a nahiyar Afirka.

Kiraye-kirayen a sake shi

Ƙungiyoyi da dama da ɗaiɗaikuwa mutane na ta kiraye-kirayen a saki ɗanjaridar wanda yanzu haka ya kwashe shekara guda a tsare.

Ƙungiyoyin da suka hada da Amnesty International da Ƙungiyar Alternative wanda yake jagoranta da dai sauran su sun bayyana ci gaba da riƙe ɗan gwagwarmayar da take haƙƙin ɗan'adam.

Bugu da ƙari, iyalansa ma sun fito sun shiga cikin masu gangamin neman a sake shi a ranar Larabar nan da suka haɗa da ƴaƴansa mata guda biyu, Falmata da Yakaka Mariama.