Mene ne amfani da illar gishiri a jikin ɗan'adam?

Hoton hannu anan barbada gishiri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akasari muna cin gishiri fiye da yadda ya kamata
Lokacin karatu: Minti 4

Gishiri na daɗa wa abincimu ɗanɗano. Yana kuma da muhimmanci ga rayuwar bil adama.

Sinadarin Sodium da ke cikin gishiri yana daidaita ruwan jikin mutum.

Shirin The Food Chain na BBC ya yi duba kan rawar da gishiri ke takawa a jikin ɗa'adam da kuma yaushe za a iya cewa ci ko shan gishiri ya yi yawa?

Muhimmancin gishiri

“Gishiri na da muhimmanci ga rayuwa," in ji Paul Breslin, wani farfesan kan kimiyyar abinci mai gina jiki a jami'ar Rutgers da ke Amurka.

Hoton kwanuka dauke da nau'in abinci daban daban, irinsu crisps, da biskit, da alawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Doka ta tilastawa masu sarrafa kayan abinci a Birtaniya su rage yawan gishiri a abincinsu

“Gishiri ya na da muhimmanci ga ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa da gadon baya da kuma tsoka. Haka kuma yana da muhimmanci sosai ga fata da kuma ƙashi".

Farfesa Breslin ya yi gargaɗi cewa idan babu sinadarin sodium za mu iya mutuwa.

Rashin sinadarin sodium na janyo matsalolin da ka iya janyo rashin tabbas da tashin zuciya da amai da suma da doguwar suma.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar shan gram 5 na gishiri kowace rana wanda yake ɗauke da gram biyu na sodium. Hakan ya yi daidai da ƙaramin cokali ɗaya.

Amma adadin da mutane suka fi sha duk rana ya kai gram 11. Hakan zai ƙara haɗarin cututtukan zuciya da kansar hanji da ƙibar da ta wuce ƙima da kuma ciwon ƙoda.

WHO ta yi ƙiyasi cewa mutum miliyan 1.89 ne ke mutuwa duk shekara saboda yawan shan gishiri fiye da ƙima.

.

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, A Kazakhstan, ana amfani da gishiri mai yawa wajen adana nama a lokacin hunturu

Ƙasashen da suka fi cin gishiri

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƙasashe da dama, yawan cin gishiri na faruwa ne saboda adadin da ke ƙunshe a abincin kamfani.

Amma dalilan na iya yin alaƙa da tarihi. Mutane a Kazakhstan na cin kusan gram 17 na gishiri duk rana, fiye da ninki uku na adadin da ake ba da shawarar ci.

Maryam na zuane a Astana, babban birnin Kazakhstan.

Ta ce suna shan gishiri ne saboda tarihinsu. "Tsawon shekaru, muna gararamba a filin Allah, ɗauke da nama mai yawa da dole a adana su ta hanyar amfani da gishiri."

"Iyalai suna siyan abubuwan amfani a lokacin sanyi. Suna iya adana naman sa ko rago ko kuma na doka."

Shekara takwas baya, ɗiyar Maryam ta fuskanci matsala. Likitanta ya shawarce ta da ta rage shan sukari da kitse da kuma gishiri. Nan da nan iyalinta suka daina sa gishiri a abincinsu.

"Washegari da muka soma, ɗanɗanon abincin babu armashi. Za ka ɗanɗana abincin amma sai ka kasa gane ko wane irin abinci ne."

Amma yanayin bai tsawaita ba. Iyalin Maryam sun saba tafiyar da rayuwarsu ba tare da cin gishiri ba.

.

Asalin hoton, Maryam (contributor)

Bayanan hoto, Mariyam ta ce mutane a Kazakhstan na cin gishiri sosai saboda yanayin abincinsu

Yaya jiki ke yi idan aka ci gishiri?

Idan muka sha gishiri, muna jin ɗanɗano a harshenmu da kuma ɓangaren maƙoshi mai taushi.

"Gishiri yana ƙara wa jikinmu kuzari," in ji Farfesa Breslin.

"Sinadarin sodium da ke taruwa ya zama gishiri yana narkewa ya zama miyau".

Waɗannan sinadarn suna kuma zuwa sinadaranmu na ɗanɗano sannan kuma kai tsaye su motsa ƙwayoyin halitta.

"Yana yin ɗan tartsatsi."

Yaushe gishiri yake yin yawa?

Tasirin yawan gishiri a jikin mutum ya danganta ne da yanayin halittun ɗan'adam.

Fiye da mutum biliyan ɗaya a duniya na fama da hawan jini. Rage cin gishiri zai iya taimakawa wajen samar da kariya.

"Idan ka ci gishiri mai yawa, abin da jikinka ke fara yi shi ne ya sirka shi. Jikinsa na da ruea, a don haka bugun jininka zai ƙaru domin zuƙo ƙarin ruwa," kamar yadda Claire Collins, farfesa a ɓangaren abinci mai gina jiki a jami'ar Newcastle ta Australia ta ce .

"Idan akwai wani rauni a jijiyoyin jini, kamar waɗanda ake da su a ƙwaƙwalwa, suna iya fashewa su kuma haifar da shanyewar ɓarin jiki".

A Birtaniya, cin gishiri ya ragu zuwa kusan gram takwas duk rana wanda har yanzu dai ya zarce adadin gram shida da ake shawartar a sha. Wannan raguwa ta faru ne sakamakon dokokin da aka samar na tilasta wa masu yin abincin gwangwani su rage yawan gishirin da suke amfani da shi.

Yawan gishirin da ake son a ci ya bambanta tsakanin ƙasashe. Gwajin fitsari ne ke iya gano ko gishiri ya yi wa jiki yawa ko kaɗan.

Domin daidaitawa gishirin da kake ci, kana iya amfani da jadawalin abinci ko manhajar da za ta lissafa yawan sinadarin sodium na kowane abinci. Babu guda cikin waɗannan hanyoyin da yake iya tantancewa ɗari bisa ɗari in ji Collins, amma kowanne na iya taimakawa.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Har yanzu Mariyam na cin abinci da daman da ake zubawa gishiri sosai

Hanyoyin rage yawan cin gishiri

Ko da yawan gishirin da kake sha ya yi yawa, ragewa ba zai zo ta sauƙi ba. A Astana, haryanzu Maryam tana ƙoƙarin ƙin cin abincin Kazakhstan mai suna beshbarmak, wanda nama ne da aka tafasa haɗe da taliya. Iyayenta da suka manyanta ba su sha'awar rage cin gishiri duk da cewa sun san haɗarin da ke tattare da hakan.

Farfesa Collins ya yi kira da mu nemi burodi da taliya ko duk wani nau'in abinci da ba shi da gishiri mai yawa.

"Idan za ka dafa abincinka, ka ƙara sinadaran ƙarawa girki ɗanɗano a maimakon gishiri."