Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke jawo haɗura a kan manyan titunan Abuja
Daga Ahmad Tijjani Bawage
Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe da ake yawan samun haɗuran ababen hawa a titunan ƙasar.
Haduran mota sun zama tamkar ruwan dare a Najeriya, inda zai yi matukar wahala a yi kwana biyu zuwa uku ba tare da an yi wani hatsarin mota a kan manyan hanyoyin kasar ba.
Haduran kan faru ba zato babu tsammani, kuma sukan kasance munana da kan haifar da asarar rayuka. Wani lokaci sukan zo da sauki.
Sai dai duk da haka mutane da dama na ganin hadari ba ya faruwa haka nan idan ba tare da wasu dalilai da ke haddasa su ba.
Kuma ko wane hadari da ya danganci sufuri ba zai yiwu a ce ya faru haka nan ba, sai da wani dalili.
A babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, duk da cewa akwai manyan hanyoyi masu kyau, wuri ne da ake yawan samun haɗura kamar sauran biranen kasar, inda a kullu yaumin ake samun haɗari.
Wata hanya da ake fuskantar wannan matsalar ta haɗura a Abuja, itace babbar hanyar zuwa anguwar Kubwa da ke Abujan.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
Abin da Direbobi da Fasinjoji ke cewa
Mutane da dama da ke bin hanyar wadanda BBC ta tattauna da su sun danganta yawan haɗura da ake samu a kan hanyar kan yawan gudu da masu ababen hawa ke yi.
Wani direba mai suna, Kamal Ibrahim Yunusa, ya bayyana cewa ya ga haɗura da dama wadanda suka tayar masa da hankali.
‘Gaskiya ana samun haɗura sosai, abinda kuma ke jawo haɗuran shi ne na farko akwai gudu fiye da kima da mutane ke yi da kuma bin one-way, wanda kuma ba daidai bane’ in ji shi.
Ya kara da cewa ‘su da suke tuki ya kamata su bi dokokin tuki ba tare da gudu fiye da kima ba, inda ya ce ‘wani gudu zaka yi, kai da ba mai nisa zaka yi ba.’
Ya kuma ce akwai haɗari da ya taba gani wanda mota taje ta doki kan gada saboda gudu fiye da kima.
Shi ma wani Fasinja da ke bin hanyar a kullu yaumin, mai suna Hussaini Muhammad ya ce gaskiya abin babu dadin gani saboda yawan haɗuran da ake samu.
"Za ka ga wani zai tafi kai-tsaye, wani kuma ya kusa ya shiga inda zai ratsa, maimakon ya dawo inda zai shiga, sai yabi hannun tsakiya, lokacin da yake son dawo wannan hannu sai kaga motocin sun hadu da juna," a cewarsa.
Haka nan ma, shi ma wani Malami da ke bin hanyar, Ya’u Dahiru ya ce so da dama abin da ke jawo haduran shi ne amfani da wayar hannu yayin tuki .
"Za ka ga mutum yana 'over-speed' yana kuma amfani da waya, tafiya yake yi amma ya hada tafiya da kula da waya, kafin ka ankara wani direba ya sa kai,’ In ji Malam Ya’u Dahiru.
Me Hukumomi ke yi
Hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya wato FRSC, tana kokarin gain cewa an samu raguwa na haɗuran ababen hawa musamman a kan manyan hanyoyin Abuja da wasu sassan Najeriya.
‘Muna zuwa tasoshin mota domin wayar da kan direbobi musamman ma direbobin motocin Bas da ke dogon tafiya kan illar gudu fiye da kima saboda su san yadda za su yi tafiya a kan hanya da kuma su fasinjoji kansu.’ In ji Adamu Sulaiman, jami’i a bangaren hulda da jama’a na hukumar kiyayye haɗura da ke Abuja.
Ya kara da cewa akwai wasu na’urori da ake sawa motoci da ke rage musu gudu fiye da kima, wanda hakan kuma na taimakawa sosai wajen rage yawan haɗura da ake samu a titunan Abuja, babban birnin Najeriya.