Wace ce Liz Truss? - sabuwar Firaministar Birtaniya

Tun a lokacin da take shekara bakwai, Liz Truss ta taɓa fitowa a matsayin firaiminista a wani wasan kwaikwayo da suka yi a makaranta lokacin tana 'yar shekara bakwai inda ta fito a matsayin Margaret Thatcher a lokacin zaben firaiminista.

Sai dai ba kamar firaiminista ɗin ba wadda ta ci zabe bayan samun rinjaye a 1983, ba ta samu nasara ba a wasan kwaikwayon da suka yi.

Bayan shekaru, Ms Truss ta tuno cewa a lokacin da suka yi zaben ba ta samu ƙuri'a ko ɗaya ba inda ita ma ba ta zabi kanta ba.

Sai dai bayan shekara 39 da faruwar lamarin ta samu damar da za ta bi sahun tsohuwar firaiministar Birtaniya domin zama shugabar masu ra'ayin riƙau kuma firaiminista.

Sakatariyar harkokin wajen ta Birtaniya na biye da Rishi Sunak a duka zaɓuka biyar da aka yi.

Sai dai jama'a na hasashen cewa ita za ta samu nasara bayan shafe shekaru tana ƙulla alaƙa da mutane kuma ta kasance mai biyayya ga Boris Johnson a lokacin da yake cikin matsi.

An haifi Mary Elizabeth Truss a Oxford a 1975. Ta bayyana cewa mahaifinta Farfesa ne a ɓangaren lissafi, yayin da mahaifiyarta ma'aikaciyar jinya ce kuma mai ra'ayin kawo sauyi.

A lokacin da tana ƙarama, mahaifiyarta ta sha ɗaukarta inda take kai ta kamfe ɗin rabuwa ko kuma daina amfani da makamin nukiliya, wanda kamfe ne da gwamnatin Thatcher ke adawa da shi a lokacin na barin Birtaniya ta ajiye makaman nukiliya na Amurka a Landan.

Wasu abubuwa game da Elizabeth Truss

Shekara: 47

Wurin haihuwa: Oxford

Garuruwan da take zama: London da Norfolk

Ilimi: Makarantar Roundhay da ke Leeds da Jami'ar Oxford

Iyali: Tana auren wani akanta mai suna Hugh O'Leary inda suka haifi ƴan mata biyu

Gundumar da take wakilta: South West Norfolk

A lokacin da Ms Truss ke ƴar shekara huɗu da haihuwa, iyayenta sun koma Paisley da zama, yammacin Glasgow.

A yayin da yake hira da BBC, ɗan uwanta ya shaida cewa ƴan gidansu na son buga wasanni dangogin dara, amma kuma Ms Truss a lokacin da tana ƙarama, ba ta son a cinyeta a wasan na dara.

Daga baya sai iyayenta suka koma Leeds da zama a lokacin da ta soma karatu a makarantar Roundhay, wadda makarantar sakandire ce ta jiha.

Daga baya Ms Truss ta tafi Jami'ar Oxford inda ta naƙalci falsafa da siyasa da tattalin arziki kuma ta kasance ɗaliba mai matuƙar son siyasa inda a baya take ɓangaren masu kawo sauyi.

A lokacin da ta yi jawabi a yayin wani taro na jam'iyar, ta yi magana inda take goyon bayan daina amfani da tsarin sarauta.

"Mu masu ra'ayin kawo sauyi mun yarda kowa zai iya samun dama, ba wai an haifi mutum bane don ya rinƙa mulki."

Siyasa

A lokacin da take Oxford, Ms Truss ta tsaya takara domin wakiltar Hemswoth a zaɓen 2001 a West Yorkshire, sai dai ba ta samu nasara ba.

Haka kuma Ms Truss ta sake rashin nasara a Calder Valley a West Yorkshire a 2005.

Amma ta samu nasara a wani zaɓe a matayin kansila a Greenwich da ke kudu maso gabashin Landan a 2006.

Shugaban Conservative David Cameron ya saka sunan Ms Truss a jerin sunaye na musamman wadanda yake son su tsaya takara a zaɓen 2010 inda kuma a zaɓe ta domin tsayawa a kujerar Kudancin West Norfolk.

Sai dai daga baya an ta ce-ce-ku-ce bayan an gano cewa ta taɓa alaƙa da ɗan majalisar yankin nata Mark Field a shekarun baya.

Sai dai an kasa korarta inda Ms Truss ta samu nasara a zaɓen da sama da ƙuri'a 13,000.